HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ai kam Fatima bata san sanda ta danƙi wuyan nurse ɗin ba, cikin masifa tace”Nace ki duba ta zan biya ko nawa kuke buƙata!!”.

Da sauri Mujahid ya ƙaraso inda suke yana raba Fatima da jikin nurse ɗin, ita kuwa sai wani tirjewa take” Ka sake ni, ka sake ni nace maka!, ai wallahi ku baza ku taɓa gamawa da duniya lafiya ba!

Shi kuwa doctor da yake cikin office yaji hayaniya tayi yawa da sauri ya fito yana tambayar me ke faruwa, na Mujahid yake mai bayani, kallon nurse ɗin yayi yace”Baki da hankali ne!? y za a kawo patient she is unconscious kice wai sai ta buɗe file za a duba ta? Go and find a wheelchair ki shiga da ita a duba ta stupid human being kawai wainda basu san darajar mutane ba!

Ai kuwa jiki na rawa ta shige ciki ta kawo wheelchair, nan aka shigar da Suhaila nan da nan likitan ya fara duba ta cikin ƙwarewa, inda ta ƙurje akayi mata ɗinki gurin kuma da baya buƙatar ɗinki aka mata dressing ɗin shi.

Ita kuwa Fatima sai safa da marwa take a gurin tana tunanin me ya samu Suhailan why is she bleeding?

Tana nan a tsaye Mujahid ya kawo mata snacks ɗin da yasiyo don ko breakfast basu yi ba.

Miƙo mata yayi amma ta tsaya tana kallon shi kamar wata wawiya, sai da ya kama hannun ta ya zaunar da ita kafin ta zauna, abincin ya buɗe ya fara bata a baki, kaɗan taci tace ta ƙoshi.

Ɗan shiru yayi kafin yace “Kin faɗawa su Abbu abunda ya faru kuwa bayan na fita?

Saurin ɗagowa tayi ta kalle shi tace” Na bar waya ta a gida, kuma ba yanzu zan kira su ba”.

Kallon mamaki kawai ya mata yana tunanin me yasa suke ɓoye abunda yake faruwa”Kin ga ba neman shawarar ki nake ba zan fita waje na kira shi yanzu, ya za ayi don rashin hankali tana cikin wannan halin kice baza a sanar da su ba, what if wani abu ya same ta fa ummm? Me zaki ce musu? “.

” Abu Nihla am scared ban san me zai faru bane shiyasa”.

“To then ki bari na kira su kawai”.

Lumshe idon ta tayi, tana jin zuciyar ta tana mata zafi, a hankali ta gyaɗa mai kai.

Tashi yayi daga Reception ɗin ya fita waje don kiran Abban nasu,ai Kuwa a bugu na uku ya ɗauki wayar, cikin girmamawa da mutuntawa Mujahid ya gaishe da Alhaji Muhammad” Abba dama wata muhimmiyar magana na kira na faɗa maka amma fa sai anyi haƙuri, tun kwanakin baya akwai abunda yake faruwa da Suhaila amma sunƙi su sanar da kowa ni kaina ɗin nan Fatima bata gaya mun abunda yake faruwa ba, to sai yau ne Suhailan ta kira tana kuka shine muka je gidan”. Ɗan shiru yayi yana tunanin ta inda zai faɗawa Abba wannan zancen,shi kuwa Abba da ya ƙagu yaji abunda ke faruwa yace”Uhmm Mujahid ina jinka ya kuma kayi shiru yi magana mana”.

“To a gaskiya Abba sai dai ayi haƙuri don a yanzu haka ma muna asibiti SUHAILA bata san inda kanta yake ba”.

Alhaji Muhammad kuwa nan da nan yaji wani jiri yana ɗiban shi cikin tashin hankali yace”Me ya sami mama na!?”

Shi kuwa Mujahid tsit yaya jin yadda hankalin Abba ya tashi sosai tun be sanar da shi ma asalin abunda yaji ita Suhailan tana faɗa ba.

” Abba ka kwantar da hankalin ka in sha Allah zata samu lafiya dama cewa nayi bari na sanar daku kar wani abu ya faru da ita kuma ba a sanar muku ba”.

“Innallilahi wainnailaihi raji’un”. ya faɗa yana komawa ya zauna akan kujera domin kuwa har ya rataya jakar shi zai fita zuwa wajen aiki.

Ita kuwa Ammi da take zaune akan kujera tana kallon tashar arewa 24 tana kallon shirin gari ya waye tayi saurin juyowa ta kalle shi jin ya kira sunan mama na.

A hankali ya furta”To ina fatiman take ita? bani waya muyi magana da ita naji me yake samun ƴar uwar tata”.

“Abba a halin yanzu Fatima baza ta iya magana ba saboda tana cikin tashi hankali matuƙa”.

Abbu kam yanzu kasa daurewa yayi tunda har yace Fatima baza ta iya magana ba to lallai Suhailan tana cikin wani yanayi.

Ammi kuwa saurin dawo wa tayi kusa da shi tace”Me ke faruwa Abban SUHAILA?

Be san sanda maganar ta fito daga bakin shi ba sai ji yayi kawai ya faɗa”Suhaila tana asibiti bata san inda kanta yake ba”.

Da sauri naga Ammi ta miƙe tana me dafa ƙirjin ta”Na shiga uku ni Asiya, me ya same ta?

“Wallahi ban sani ba, ban sani ba”.ya ƙarashe maganar kamar zai yi kuka..

Ganin Ammi yayi kawai ra shige ɗaki ba a fi 10 minute ba ta fito riƙe da jaka a hannun ta alamar ita har tayi shirin ɗaukar hanyar Kaduna.

Tsayawa kallon ta yayi kawai mamaki kwance akan fuskar shi”Asiya ina kuma zaki je?

“Au tambaya ta kake ma ina zan je,, lallai ma mutumin nan idan kai baza ka je ba to ka bani kuɗin mota naje na ga ƴata”.

Da sauri Farida ta fito daga ɗaki jin abunda suke faɗa, nan take tambayar abunda ke faruwa, duk abunda Mujahid ya sanar da shi ya faɗa mata, nan fa kowa ya shiga tashin hankali, mubarak kuwa yana makaranta be san wainar da ake toyawa ba.

Kallon Farida yayi yace”Farida bari muje ki kula da MUBARAK don Allah, wata ƙila na dawo da daddare idan kuma ban samu dama ba to sai gobe da safe zan taho.

Farida kuwa gaba ɗaya idon ta ya ciko da ƙwalla, ji take kamar ta bisu ko me ya sami yayar tata oho.

Haka nan dai su kayi sallama.

_Ohohoho wa yaga su Ammi a kaduna akwai shafta kenan_.

 

Bayan likita ya fito yake sanar da su abunda ya faru da Suhailan amma kar su damu an yi mata ɗin ki sannan kuma ta ɗan samu bacci ne she will be fine.

Ɗan shiru likatan yayi, da har zai tambayi ko me ya same ta sai kuma yayi shiru ganin babu kyau bincike.

Fatima kam har ta ɗan samu relief sai kuma yace”Sannan munyi nasarar dai-dai ta bleeding ɗin da take yi kuma Alhamdullilah babyn nata yana lafiya duk da cikin nata na kwana 21 ne, saboda haka a za a barta a nan asibiti har sai tayi sati biyu ta samu bedrest ana kula da ita idan ba haka ba abu kaɗan ne zai sa cikin ya zube, yanzun ma kawai Allah yayi zai zauna ne kun san yadda Allah yake al’amarin shi kana naka Allah kuma na tsara ikon shi”.

Tunda ya fara maganar cikin nan Fatima taji gaba ɗaya komai nata ya tsaya cakk numfashin ta ma kawai ƙoƙarin yadda za tayi controlling ɗin shi take.

Mujahid kuwa duk da be san abunda ke faruwa ba shima ji yayi kamar an watsa mai ruwan zafi a jikin shi tunda dai da kunnen shi yaji tace ya mata saki biyu, kuma yanzu ace ciki.

Jin shiru yayi yawa yasa doctor ya buga table ɗin shi, nan gaba ɗayan su suka dawo cikin hayyacin su.

” Me ya faru naga kunyi shiru?

Mujahid ne yayi saurin ɗaga Fatima yace babu komai mun gode likita sosai da sosai bari mu biya bill ɗin mu.ya ja hannun Fatima suna fita daga gurin.

Ɗakin da SUHAILA take suka shiga, Mujahid yana riƙe da Fatima, suna shiga ta fasa kuka me cin rai tana kallon yadda Suhailan ta rame lokaci guda.

Shi kuwa Mujahid ƙara rungumo ta yayi yana shafa bayan ta haɗe da kwantar mata da hankali.

“Abu Nihla wai ciki ne fa da ita, ciki fa, innallihai wainnailaihi raji’un, ya Allah ka kawowa wannan bewar taka sassauci, ya Allah ka fi mu sannin halin da take ciki ya Allah ka bata lafiya ka ba bata ikon cin jarabawar ta”.

Mujahid ne yace “Will you tell what happen a sati uku da suka wuce”.

Lumshe idon ta tayi hawaye na daɗa bin kuncinta tace”I will Abu Nihla me kuma zan ƙara ɓoye maka”.

Kujerar da take gurin ya janyo ya zauna a kai kafin ya ɗora fatiman akan cinyar shi yana me kwantar da kanta a ƙirjin shi.

“Am all ears ummun Nihla da Walid”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button