ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara magana a hankali”A shekarar da aka sa mana rana da kai wani iftala’i ya faru da Suhailan, nan ta faɗa mai duk abunda ya faru a shekarun baya har zuwa halin da suke ciki yanzu.
Allah sarki Mujahid har ƙwalla sai da yayi.
“This son of bitch Habib!!! Indai haka ne kuwa Let abort the child”.
Da sauri ta ɗago kai ta kalle shi tace “Not again Mujahid, wannan fa yana da uba ya za ayi a zubar da shi”.
Banbancin shi da wancan kaɗan ne kawai, waincan sun mata illegal abuse shi kuma yayi amfanin da ita ya mata legal abuse, ba zai san da wannan ɗan ba wallahi”.
“And what about SUHAILA? What about her? wani hali za ta shiga wancan karan fa har mutawa ta kusa yi, aa hakan ma bazai faru ba noooo there is no way za a ƙara mata abortion”.
“Then ki bari sai Ammi tazo kawai”. Ya faɗa yana ɗaga ta daga cinyar shi yayi hanyar fita daga ɗakin.
Cikin son jin ƙarin bayani tace”Ammi zata zo ne?
Be juyo ya kalle ta ba yace”Ita da Abbu suna hanya”.
Komawa tayi ta zauna kan kujera daɓas don ta san in dai Ammi taji maganar cikin nan sai ta sa an zubar da shi, but then baza ta bari hakan ya faru ba, Suhailan zata zauna a gidan ta har sai ta haihu kuma babu wanda zai san da cikin har shi uban ɗan.
******
Habib kuwa yana Shiga shagon Mustapha ya samu guri ya zauna duk jikin shi a saɓule duk yayi wani yaushi kamar ba shi ba.
Mustapha kuwa yana ganin shi ya san burin shi ya cika, nan yake tambayar shi me ke faruwa.
“Na sake ta saki biyu, Habib ya furta”.
Wani daɗi Mustaoha yaji a ranshi yace”Banza wawa kawai, kayi missing wallahi kuma zan nuna maka kayi babban kuskuren sakin matar ka me kamala da kunya da kuma kamun kai, dama abunda nake so kenan domin a zamanin nan kafin ka samu macen da take da hallayya irin na SUHAILA sai an tona”.
A fili kuma yace”Allah ya maka albarka, da ka tsaya kana sanya me za kayi da wannan abar.
Nan dai ya gama jinjina mai yana wani jin daɗin zai samu Suhailan a ɓagas.
_Ni kuwa nace me za tayi da kai, wallahi ta wuce ajin yara irin ku_????
*****
Da misalin ƙarfe uku na rana su Ammi suka iso garin kaduna, gidan Fatima suka wuce direct inda suka tarar da Mujahid a gidan har ya ɗakko su Nihla a makaranta ni kuwa nace bawan Allah yau ko gurin aiki ma be je ba.
Hankalin su a tashe suke abubuwa domin kuwa sai da suka ci abinci su kayi sallah sannan suka fara shirin zuwa asibiti, duka tare da yaran.
A can asibitin kuwa SUHAILA ta farfaɗo amma tunda ta tashi bata ce komai ba kawai dai ita gata nan ita ba a duniya ba ita ba a lahira ba, domin kuwa lokacin da suke hira tana jin su sama-sama kuma ta ɗan tsinci zancen cewar za a zubar da ciki, to idan ba ita ba wa za a zubarwa da ciki shine abunda yake damun ta wanda ya sa ta a cikin shock.
“SUHAILA kici abinci mana” cewar fatima.
Ba ta bata amsa ba tace”Waye yake da ciki? kuma wa za a zubarwa da ciki?
Da sauri Fatima ta kalle ta don ko Suhailan bata so taji zancen cikin da wuri haka ba.
Hannun ta Fatima ta dafa tana faɗin”Babu kowa a ina kika ji wannan zance?
“Ya Fatima ki faɗa mun kawai bana son ɓoye-ɓoye!! Yadda SUHAILA tayi magana har sai da ta girgiza ƙarfen da yake saƙale da ruwa da ake ƙara mata.
Da sauri Fatima ta riƙe ta tana faɗin” Ki yi a hankalin Suhaila you carrying a child!”.
A dai dai lokacin kuma Su Ammi suka buɗo ƙofar ɗakin kuma sunji abunda Fatiman ta faɗa.
Da sauri dukkan su suka kalli ƙofar ganin masu shigowa, Mujahid ne a gaba sai kuma Abbu na bin bayan shi sai Ammi da jikokin ta daga ƙarshe.
Tana haɗa ido da Abbun ta tace”Abbu…… Ammi…. “.
Shi kuwa alhaji Muhammad da gudu ya ƙarasa bakin gadon yana me rungume Suhailan a jinkin shi tsam ganin yadda ta koma in one glance ɗin da yayi mata.
” Mama na”ya furta a hankali.
Ita kuwa Ammi kawai take kallo yadda ta wani haɗe rai kamar ba ita ba, nan kuwa deep inside her ji take kamar ta fasa ihu ganin irin halin da ƴar tata take ciki.
A hankali Suhailan ta miƙa mata hannu tana daga jikin Abbun ta tana faɗin”Ammi am sorry is your du’a naje kuma na gani Ammi, Ammi please”ta faɗa tana ƙara miƙa mata hannu haɗe fasa kuka me cin zuciya.
Tuni zuciyar Ammi ta karye ta ƙarasa inda Suhailan take tana rungume ta itama.
“Me ya same ki haka ummm Suhaila? Ta faɗa tana Shafa fuskar ta.
” Ammi addu’an ki ne, Ammi naƙi jin maganar ki na dage kuma kika mun addu’a gashi nan na gani wallahi, ki yafe mun”. ta faɗa tana kuka me cin zuciya.
“Shhhh oya tell me, me ya faru dake gashi nan jikin ki duk ciwo”.
Cikin kuka ta raba jikin ta da na Abbun ta tace”Habib ya sake ni saki Biyu Ammi , because am not a virgin”.
Daga Abbu har Ammi babu wanda ya kawo wannan a ranshi duk da cewa da suka shigo basu ga Habib ɗin ba amma hankalin su be kai kan wani abu ne a tsakanin su ba.
Lumshe ido Ammi tayi ƙwallar da take kwance a idon ta zubo.
Wayyo Suhaila wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta yanzu ace Ammin ta ce take kuka saboda tausayin ta.
Abbun ta kuwa rungume ta yayi yana ƙara rarrashin ta.
Ita kuwa Ammi tuni hankalin ta ya kai kan maganar da suna shigowa suka ji Fatima tana faɗa.
“Then naji kina maganar ciki Fatima?
Jikin Fatima na rawa tace” Ehhhh…. Ammi… Haka n…e.
Cikin kakkausar murya tace”Then she must abort the child”.
Fatima saurin kallon Ammi tace “Ammiiiiii….
Shikuwa Abbu saurin sakin Suhaila yayi yana kallon ta da mamaki kafin yace” Asiya?!!! ???? Yana wani zaro ido kamar wanda zai iya tsare gida.????
Mujahid kuwa cewa yayi”Goodd Ammi” a can ƙasan maƙoshin shi…….
*_Huuuuuhh here we are_.*????
_*We have alot of dramas*_????
*Comment and share.*
*Facebook readers if you want to join my WhatsApp group contact. me@08144426415*
*Assalama alaikum*
*Faɗma Ahmad*✍????✍????
[6/13, 2:43 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*page2️⃣0️⃣to2️⃣1️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.
*Abin Da Wanda Ya Aikata Wani Zunubi Zai yi kuma Ya Fada:*
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa da zai aikata wani zunubi, sannan ya kyautata alwala, ya tashi ya yi sallah raka’a biyu, sannan ya nemi gafarar Allah, face Allah ya gafarta masa.
_*Abortion*_
Barin jikin gadon yayi ya dawo kusa da ita yana kallon ta alamar tayi shiru.
Ɗan taɓe baki tayi kafin ta nemi guri ta zauna a bakin gadon, shi kuwa Mujahid da ya gane saboda shi su Ammi suka yi shiru tuni ya kama hannun yaran shi za su fita a ɗakin.
Nihla ce cikin tsamin bakin ta na yara tace “Abee Aunty Hala tazo ka barni naje guyin ta”.
Ɗaukanta yayi yace”Ki bari muje mu siyo alawa sai mu dawo gurin Aunty Hala kinga bata da lafiya ko”.
Ɗan taɓe baki tayi sannan ta gyaɗa mai kai.
Bayan ya fita Abbu ya kalli Ammi yace”Wallahi Asiya karma ki soma tunanin nan, kin san wancan karon ma haka kika yi kika kusa kashe ta, to baze yiyu ba idan wancan kinyi don kar mutane su san abunda ya faru da ƴar ki wannan fa? Iye, yana da uba ba wai ba shi da uba ba don haka ahir ɗin ki kinyi na farko kuma kinyi na ƙarshe.