HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Fatima ce tace”Haka ne Ammi don Allah kiyi haƙuri ki barta, ba sai ta zauna a gida na ba har ta haihu tunda kinga ko rabin service ɗin ta bata yi ba, sai kawai mu zauna tare don Allah Ammi”.

Fatima ce ta kalli SUHAILA tace “Kiyiwa Ammi magana mana kin fi kowa sannin irin wahalar da kika sha wancan karan”.

Bata ce uffan ba ta koma ta kwanta abunta don kamar ba a duniya ba haka take jinta, ita koma menene tayi giving up ɗin shi ɗa ne wani aure duk baya kanta yanzu, bata damu ba idan cikin ya zauna ko kar ya zauna duk damuwar shi ce, kai idan Ammi cewa tayi ayi mata wankin ciki a murje ɗan zata yarda, ba abunda ya sha kanta ita kam yanzu.

Ammi kuwa ko kallon inda su Fatima da Abbu suke bata yi ba ta cigaba da sabgar gabanta, don wallahi babu fashi sai ta zubar da cikin nan.

Abbu dai yayi yayi magana amma tayi banza kuma ba reaction ɗin komai a fuskarta sai ma sabgar gaban ta da ta cigaba da yi kamar ba da ita yake ba.

“Asiya ya kamata ki dena abunda kike mun don Allah, komai ya wuce na roƙeki kar ki muzgunawa SUHAILA saboda ni don Allah”.

Kallon shi tayi kawai tana murmushi kafin tace”Hmmm nidai ba a baki na ba”.

Girgiza kai kawai yayi ya fita a ɗakin zuciyar shi tana mai zafi ya rasa ya zaiyi da ita ta zame mai ƙarfan ƙafa shi ba abun yasake ta ba yasan ko da wasa bazai iya hakan ba, amma wallahi ta kuskura wani abu ya samu SUHAILA a shirmen ta na banza sai ya ɗau mataki akan ta.

Bayan fitar Abbu Fatima ta daɗa lallaɓa Ammi amma yadda kasan ba da ita take magana ba, daga baya ma sai ce mata tayi taje gida ta kawo musu abubuwan amfani tunda yanzu suka fara zama ma.

Haka nan Fatima ta shirya tana fitowa ta haɗu da Mujahid nan suka koma gida.

Sai da tayi wanka tayi sallah kafin taci abinci da misalin 8:00pm suka koma asibitin haɗe da abubuwan amfani har da abinci ma duk ta kawo musu. Bayan anci abinci an nutsa Suhaila tace”Ya Fatima an kwashe kayan?

Abbu ne yayi saurin cewa “Wasu kayan kenan?

” Hmm Abbu wai kayan ta ne take ce mun tayi mai alƙawarin yau zata kwashe shine take tambaya ta”.

Hannun ta ya kama yace”Mama na, da wuri haka? Ki bari mana tukunna”.

Ɗan juyowa tayi ta kalle shi tana daɗa riƙe hannun shi sosai cikin nata kamar ance mata za a raba ta da shi, ahankali ta fara magana”Abba meye amfanin barin kayan? gwara kawai a kwashe su, baya so na, baya son gani na, to me zan yi a gidan shi? Kar ku damu da ni na san soon komai zai wuce”.

Shafa kanta yayi yace” Allah ya miki albarka kinji ko”.

Da Amin ta amsa sannan ta koma ta ƙara kwanciya tana jin zuciyar ta na mata zafi, yanzu kam ta dena zubar da hawaye sai dai na zuci.

*****

Bayan Habib ya bar kasuwa ko da wasa be yi gigin komawa gidan shi ba, ga shi abun ya dame shi har yanzu babu wanda ya kira shi yayi mai zancen sakin don yasan dai a halin da ake ciki dangin Suhaila sun san ya sake ta.

Da sallama ya shiga palon hajiyar tashi inda take sanye da farin gilashi a fuskar ta tana karanta jarida,jin sallamar shi yasa ta ɗago kai ta kalle shi tana mamakin daga ina yake a wannan lokacin.

Guri ya samu ya zauna yana me sunkuyar da kai idon shi duk ya faɗa ga kuma rashin kuzahari a tattare da shi.

Be yi mata maganar sakin ba itama kuma bata tambaye shi ko me ya kawo shi ba sai hira kawai suke samama.

“Ni kuwa Habib yaushe zaka ƙara kawo mun Suhaila? sau ɗaya fa ka taɓa kawo mun ita, yarinya me hankali da nutsuwa”.

Ras ras yaji gaban shi ya faɗi, ta ina zai fara faɗawa hajiyan shi ya saki Suhaila shi kam yanzu ya zai yi.

Ɗan sosa ƙeya yayi kafin yace”Uhmm zan kaw…. o ta… ai Hajiya”.

“Hmm Allah ya kaimu to Habib”.

Sai da suka kai tara da rabi suna hira ganin dai bashi da niyyar tafiya yasa tace mai”Habib dare yayi ka tashi ka tafi ka baro ƴar mutane a gida”.

Ɗan shiru yayi kafin yace”Hajiya a nan zan kwana yau”.

Da sauri ta ajiye jaridar hannun ta haɗe da cire glasses ɗin idon ta tace”Mene!? A nan zaka kwana kuma? Akan wani dalili? Kai wai me yake faruwa ne? dama tunda kazo na ganka wani iri”.

Sauka yayi daga kan kujerar da yake ya zauna a saman rug yana wani mutsi- mutsi da ido yana tunanin ta inda zai fara kora jawabi.

“Ba magana nake maka ba wai Habib ka mun shiru kana wani matse ido, malam talk to me!”

 

Cikin inda inda yace”Ammm amm hajiya dama maganar da muka yi da ke washegarin biki na shine……. Shine……. “.

Sai kuma yayi shiru.

” Uhmm ina jinka shine me? Ƙarasa mana”.

“To daman kin san kin bani zaɓi to shine naga gaskiya bazan iya…. Bazan iya….”.

“Baza ka iya me ba? Wallahi zanci ubanka kayi mun magana nace maka ko!

” Hajiya don Allah kiyi haƙuri wallahi ban san me yasa ba amma na kasa daurewa, na saki Suhaila saki biyu”.

Wani irin wawan kallo ta watsa mai tana folding hannun ta a jikin ta, komawa tayi ta jingina a jikin kujerar tana maida glasses ɗin ta”Uhmmm ka sake ta fa ka ce Habibi?

 

Shiru yayi be amsa mata ba.

“Bazan ce maka komai ba wallahi, tunda kaine da kanka Habib, duniya ce dai gata nan Allah ya bada sa’a sai kaje ka nemo wacce take da budurcin ta ka aura, sannan kuma ka nemi kawun ka ka faɗa mai wannan zancen don ba ruwa na. Tashi ka bani guri wawa kawai mara hankali, wanda be san inda yake mai ciwo ba”.

Sunkuyar da kan shi yayi sannan yace”Hajiya kiyi haƙuri don Allah”.

“Rufe mun baki wawa kawai, dalla bani guri, kuma ka sani yau kaɗai zan maka alfarmar kwana a gidan nan ai kana da gida sai ka je can ka ƙarata tunda baka jin magana, duniya kawai ka sa a gaba Habib”.

“Hajiya don Allah yi haƙu…….

Be ƙarasa faɗan abunda zai faɗa ba tace” Hold it Habib, kar ma ka soma bani haƙuri ka fitar mun a palo nace! mara kunya kawai!”

Sum sum ya tashi ya bar palon jikin shi a sanyaye kamar wani mutumun kirki.

Washegari da safe Fatima ta dawo ta kawo musu breakgast jikin ta kam Alhamdullilah yayi sauƙi sosai don yanzun babu wani abunda yake damun ta sai ciwon kai da kuma fargaba.

Abba be zo da wuri ba sai wajen 10:00 su ka taho tare da Mujahid, mujahid be daɗe ba ya wuce gurin aiki.

 

Suhaila ce kwance ta rafka uban tagumu tayi nisa a tunani taji hannun Abbun ta yana shafa kanta”Mama na, me ya faru ne? Don Allah ki rage tunani kinji ko, you will be fine tun jiya Farida da Mubarak suke kira na ina ce musu baki nutsa ba tukkunna, in kira miki su ne yanzu?

“Eh ka kira”.

Bayan sun gaisa a waya Ammi ta zuba mata abinci da ƙyar ta samu taci shima kuma ba da yawa ba.

“Mama na”. Abbu ya ƙara faɗa.

Ɗan kallon shi tayi kafin tace”Abbu na kar ka damu fa zan samu sauƙi kuma komai zai wuce, jarabawa ce, Allah ne yake jarabta ta yaga ya zanyi don haka kar ka damu, kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin cin jarabawar Abbbu”.

“Allah sarki Allah ya miki albarka lokaci ne wallahi, amma ina tabbatar miki da cewa zaki ji daɗin rayuwa”.

Wani ƙayataccen murmushi tayi wanda har sai da haƙoran ta suka ɗan fito sannan tace “Abbu…. In sha Allah”.

Ɗan riƙo hannun ta yayi yana kallon maman nashi ji yake kamar kar ya tafi ya barta da Ammin ta amma ya zai yi dole ya koma bakin aiki.

_Ni kuwa nace duk abun ta dai baza ta kashe ta ba_

A hankali ya fara magana ganin Ammin ta ɗan kauce ko ina zata je oho”Mama na ni zan koma gida, kinga mun bar su mubarak a gida don ma Allah ya temaka munyi waya da Hajiyan sheka ta tura musu su Bahijja amma duk da haka ya kamata na koma saboda makaranta kinga ko excuse ban ɗauka ba sai kira nayi nace bazan samu damar zuwa ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button