ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Itama riƙe hanun shi tayi tace “Abbu kasan maman ka dai ko?
Dariya yayi yace” Ni kuwa nasan mama na”.
“To ka barshi a yadda ka sanni it will be okay kar ka damu kaji”.
“To mama na. Ammm kina ji ba?
” Ummm”ta faɗa tana gyaɗa kai”.
“Duk abunda Ammin ki zata baki karki sha kinji ko, duk abunda tace kiyi kar kiyi karki sake tasa a zubar miki da ciki ki yarda”.
Ɗora ɗayan hannun ta tayi akan nashi tace”Abbu karka damu ummm babu abunda zai faru”.
“Mama na please don Allah karki biye mata kinji ko”.
Gyaɗa kai tayi tana saurin goge hawayen da yake zubo mata.
“In sha Allah Abbu”.ta faɗa tana rungume shi,shima rungume ta yayi yana shafa kanta.
Ita kuwa Ammi da ta fita a ɗakin direct gurin nurse ɗin da suka haɗu da Fatima ta nufa tana zuwa babu wani ɓata lokaci ta sanar da ita abunda take buƙata.
Nurse ɗin kuwa cikin tashi hankali tace ai me asibitin ya hana zubar da ciki don haka baza ta iya ba gaskiya saboda zata iya rasa aikin ta.
Babu yadda Ammi bata yi da ita ba amma taƙi bata haɗin kai.
Ɗaki ta dawo ka tambayi Abbu kuɗi babu yadda ya iya ya ciro 20k ya bata yace gashi nan su riƙe ma a hannun su idan suna buƙatar wani abu.
Ƙara fita tayi ta koma gurin nurse ɗin ta bata 5k akan ta temaka mata, nurse ɗin dai da ƙyar ta karɓa amma da sharaɗin zata rubuta mata maganin ne a jikin card yadda zata je chemist ta siya.
“Amma kina ganin baza a gane ba?
Ammi ta tambayi nurse ɗin.
“Kar ki damu zanyi amfani da card ɗin doctor Jibril yadda kina zuwa chemist ɗin asibitin za su baki maganin yana da ƙarfi kina bata zai zube tunda weeks ne.
” Bari na shiga office ɗin na fito, don ya kusa tafiya gobe zai koma london”.
Kuma idan ya tafi ba da wannan office ɗin other doctors suke amfani ba sai za a ɗau abu me mahimmanci ake buɗe shi.
“Yaje gida ya dawo ne ina zuwa”.
Shiga office ɗin tayi ta ɗakko card ɗin ta rubuta mata sunan maganin ta bata, ai kuwa Ammi babu wani ɓata lokaci ta wuce zuwa chemist ɗin tana zuwa kuwa babu wani ɓata lokaci ya bata.
Bayan ta dawo ɗaki ta zauna tayi shiru kamar wata wadda ta aikata abun ƙwarai.
Nan dai suka cigaba da hirar su sama sama har Abbu yayi shirin tafiya sai da ya ƙara jaddawawa Ammi akan kar ta yi wani misbehaving ba ruwan ta,ta bar zancen zubar da cikin nan, uhmmm ta amsa mai amma yasan ba har zuci ba kawai dai abunda ya sani yajawa Suhailan kunne.
Nan ya ƙara musu sallama ya tafi abun shi.
****
Da misalin 40:00 na rana Fatima ce zaune akan kujera sai Ammi da take gefan SUHAILA tana ta faman tura mata abinci ita kuwa Suhaila sai mamaki take wai yau Ammi ce zaune tana bata abinci a baki ita dai tasan ko tana yarinya sai dai Abbun ta ya bata ba dai Ammin ta ba.
Bayan ta gama cin abinci ta ɓallo magunguna ta bata harda wanda zai sa cikin ya zube ai kuwa babu musu Suhaila ta karɓa ta sha.
Tunda Suhaila tasha maganin nan taji marar ta na murɗa mata, daga baya taji har ƙasan ta abun dai ba a cewa komai.
Tun tana daurewa har ta faɗawa Fatima nan dai ta kwantar mata da hankali tana mata sannu.
Bayan sallar magrib dai Suhaila har kusan zama tayi bata san inda kanta yake ba.
Daga baya ma sai jini ya ɓalle mata yana fita gudada. Da gudu Fatima taje ta kira Nurse yanzu kam ba wannan wanda suka haɗu bace watace daban. Tana duba ta tace ai tayi miscarriage ne amma aje ayi scanning don a tabbatar da cikin ya gama fita duka ko akwai ragowa.
Ammi kam ji tayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ita kuwa Fatima saurin juyowa tayi ta kalli Ammi don ta san wannan aikin nata ne.
Runtse ido tayi hawaye na zubo mata tace”Ya Allah yanzu sai da Ammi ta zubar da cikin nan”…………
_*Finally, ayya my SUHAILA*_????
_*ma’asalma*_
*Faɗma Ahmad*✍????
[6/14, 2:55 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*page2️⃣2️⃣to2️⃣3️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.
Addu’ar Korar Shaidan da Wasuwasinsa:
Ya nemi tsarin Allah daga shaidan.
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ.
A’uzu billahi minash shaytanir rajeem (3)
Ya yi kiran sallah.
Yin zikiri (ambaton Allah) da karatun Alkur’ani.
*_Why Uncle Habib?_*
Sauri sauri gudu gudu aka kwashi Suhaila zuwa gurin scanning suna shiga gurin babu wani ɓata lokaci akai mata scanning wanda ita bata ma san inda kan ta yake ba, takardar aka basu don su kaiwa likita, aikuwa suna dawowa suka yi sa’a shima doctor Jibril ya dawo ana bashi takardar yace ai ta riga da tayi miscarrying babyn, nan da nan hankalin Fatima ya tashi sosai don ita ko yaya ne taso ace ta haifi ɗan ko ɗan Habib ne itama ai nata ne.
Doctor Jibril ne yace”Kai amma fa nayi mamaki, tunda a bedrest take”.
Ammi ce tayi saurin cewa”Doctor ina tunanin ɗazu da safe ne munje banɗaki zan mata wanka sai na manta soso ban ɗauka ba to da na fito ɗauka shine jiri ya ɗebeta ta, to inaji a nan aka samu matsalar”.
Girgiza kai Jibril yayi yace “Ayya Allah ya kiyaye, tabbas ina tunanin wannan shine dalilin miscarriage ɗin nata, Allah ya bata lafiya”. ya faɗa yana kallon Suhailan.
Har ya juya zai fita daga ɗakin sai kuma ya juyo yace” Don Allah ina da tambaya”.
Ammi ce tayi saurin cewa “Allah yasa muna da amsar likita”.
“Ammm ni kam wai bata da miji ne don tunda aka kawo ta ban ganshi yazo ba duk da ba zama nake sosai a asibitin ba”.
“Uhmmm likita kenan ka ganta nan sati uku da aure mijin ya sake ta wallahi don kawai ƙaddara ta faɗa mata”.
Fatima ce ta saki baki sakatoto jin Ammin nasu tana neman ta musu tonan silili a bainar jama’a.
Jin haka yasa tayi saurin karɓe zancin tana faɗin”Wallahi kuwa likita mun gode sosai da sosai, yaushe za a bamu sallama?
Jibril ne ya ɗan yi murmushi har sai da dimple ɗin shi suka lotsa kyaun shi da haibar shi suka ƙara fita sosai. Chocolate color ne shi daga ganin fatar jikin shi kasan ta sha hutu babu ƙarya yadda kasan irin black american nan, gashi da faɗi daga gani yana ɗaga ƙarfe sosai idan ma baya ɗaga ƙarfe to fa yana jiming sosai, haƙoranshi da suka jero reras a bakin shi ne suka fito sosai abun sha’awa gasu farare tassss don su suke ƙara mai kyau ma.
Ɗan dawowa yayi cikin ɗakin zuwa bakin gadon yace”Bari ta farfaɗo, za a bata wani tablet ta sha duk abunda yake ragowa zai fita, ba sai an yi mata wankin ciki ba tunda weeks ne babu wata matsala. Sannan kuma gobe in sha Allah zan bar gari so akwai likitoci da za su yi taking over ayyukan, nan da kwana uku idan ta warke za a baku sallama, shikenan”.
Ya faɗa yana ƙara faɗada fara’ar shi.
“Eh shikenan”. Fatima ta faɗa tana komawa ta zauna a gefan gadon kusa da Suhaila.
“Sai anjima ya faɗa yana fita daga cikin ɗakin”.
Yana fita Fatima tace “Haba Ammi ya zaki faɗa mai, mutumin da ba mu san shi ba kawai sai mu kama faɗa mai sirrin mu ummm?
” Ke! malama Baza ki gaya mun abunda ya kama ta nayi ba”Ammi ta dakawa Fatiman tsawa tana neman fita daga ɗakin, sai da taje bakin ƙofa sannan ta juyo tace”Kika sani ko yace yana sonta don daga ganin shi ɗan babban gida ne”.