HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Girgiza kai kawai Fatima tayi tana faɗin”Sai kin dawo”.

Bayan ta fita Suhaila ta motsa nan ta buɗe idon ta,ji tayi kanta yayi mugun sara mata gashi har yanzu tana ɗan ji ciwon marar.

Fatima ce tayi saurin daɗa matsawa kusa da Suhaila tace “Sannu, kin tashi?

Ɗan motsawa Suhailan ta ƙara yi alamun tana so ta zauna.

Saurin ɗaga ta Fatima tayi tana jera mata sannu.

” Ya Fatima me ya faru da ni?

“Hmmm SUHAILA wai ance miscarriage kika yi amma nasan Ammi ce ta zubar ta cikin babu makawa”.

“Aa ki dena faɗan haka kinji ko ai ba abunda ta bani kuma bata sa an yi mun wanki ciki ba fa”.

“Hmm ni dai na san akwai abunda ya faru kedai kawai kiyi shiru amma akwai sa hannun Ammi a cikin maganr nan,ina ji fa take bawa doctor wani labarin ƙanzon kurege kuma na san dai faɗa tayi kawai amma hakan be faru ba.

Nan take faɗa mata abunda Ammin tace.

Suhaila kuwa da saurin ta tace”Laaaa ai kuwa abunda ya faru kenan da gaske ba ƙarya take ba, amma abun da mamaki haka sai yasa mutum yayi ɓari?

Wani kallo Fatiman ta watsawa Suhailan tana tunanin anya ba ƙarya ta mata.

Nan dai Suhailan tayi ta convincing nata har sai da ta yarda.

Ita kuwa Ammi bayan ta fita gurin nurse ɗin nan taje tayi ta jera mata godiya.

Fatima ce ta kira Abbu ta faɗa mai abunda ya faru, don ko gida be isa ba yana hanya, shima dai da farko be yadda ba amma tunda Suhailan ta karɓi waya ta tabbatar mai da hakan sai ya yarda don yasa koma yaya ne maman shi zata faɗi gaskiya.

Bayan magreeb su Fatima suka shirya inda Mujahid ya zo ɗaukan ta ya taho tare da su Nihla.

Da gudu Nihla taje bakin gadon tana a ɗora ta taga Aunty Halan ta aikuwa babu wani ɓata lokaci ta ɗane tana rungume ta.

“Oyoyo my princess”. Suhaila ta faɗa tana daɗa rungume Nihla.

Saurin barin jikin Suhaila tayi tana taɓa jikin ta kafin tace”Aunty hala Abey yashe baki da lafiya ko?

Gyaɗa mata kai Suhaila tayi tana shafo kanta tace”Amma yanzu na warke my princess”.

Fatima ce tace”Dunkum kai baza ka mata sannun bane? Ta faɗa tana turo ƙeyar Walid.

Suhaila ce tace”Barshi village boy kawai”.

Nan dai suka gama wasa da dariya sannan su Fatima suka wuce gida.

Bayan sallar isha’i Ammi tayi shirin kwanciya Suhaila tace “Ammi don Allah ina so muyi magana”.

“Uhmmm inajin ki”. Ta faɗa tana ƙara gyara shimfiɗar ta.

“Ammi me nayi miki ne? Me yasa kika tsaneni? Me yasa ba kya son ganin farin ciki na? Me yasa kika zubar da cikin nan?

Kai Ammi ta ɗago ta kalli Suhaila kawai tayi murmushi kafin tace” tambayoyin ki na farko bani da amsar su a a halin yanzu, ta ƙarshe kuma, ba abunda zance miki sai for you own good saboda good future naki, sannan kuma da kin bari kin haifi wannan ɗan ko kinyi aure baki rabu da Habib ba kuma duk sanda kika ganshi sai kin tuna abunda yayi miki, shiyasa kawai na yanke duk wani abu a tsakanin ku. Duk yadda kika kai ga ɓoye masa ɗan shi watara na sai ya san da shi, so hakan be da amfani.Ki ɗau tab ɗin da nurse ta kawo ɗazu ki sha ki kwanta zuwa jibi za a sallame ki, ni kuma gata zan wuce kano, zaki zauna da Fatima har ki kammala service ɗin ki”.

Wasu hawaye ne masu zafi suka wankewa Suhaila fuska, wani zafi zuciyar take mata ita dai tana son jin dalilin da yasa Ammin nata take nuna mata banbanci sosai haka.

Komawa tayi ta kwanta tana share hawayen ta.

Sai kuma daga baya ta tashi tace”Ammi don Allah idan Abbu Nihla yazo gobe kice ya nemo me mota a kwashe kayan gidan Habib”.

“Karki damu nima ina da niyyar yin hakan gobe”.

Kwanciya tayi abunta, da ƙyar ta samu baccin wahala ya kwashe ta.

******

Washegari da safe Hajiyan Habib ce zaune akan kujera one sitter ta ɗora ɗaya kan ɗaya tana riƙe da jarida a hannun ta.

_Ni kuwa nace ka ga mata ƴan boko an tsufa ba dena ba._

Abunda Habib ya aikata ya taɓa ta sosai da sosai kawai dai tana daurewa ne, tana zaune tunanin kiran maman Surayya ya faɗo mata, anya kuwa tasan abunda ƙanin nata ya aikata kuwa.

Cikin sauri da son sanin ko sun san abunda yake faruwa ta ɗakko wayar ta ta kira Hajiyan Suhaila.

Ai kuwa a bugu na huɗu ta ɗaga kiran”Hello hajiya ina kwana, kin tashi lafiya?

“Lafiya lau Alhamdulillahi Bilkisu ya mutan gidan?Hajiyan ta faɗa tana ƙara gyara zaman ta.

” Amm nace ba, ni kuwa Habib ya faɗa miki abunda ya aikata?

Daga can ɓangaren Hajiyayn Surayya tace”Wallahi ban sani ba, be faɗa mun komai ba ni rabona da shi ma tun washegarin bikin shi”.

“Hmmm to ai kuwa yayiwa ƴar mutane saki biyu, ni wallahi don kunya ma na kasa kiran yarinyar naji a wani hali take ciki, don ni dai bazan ce mai ya dawo da ita ba”.

“Wai Hajiya kina nufin maganr da kika faɗa kunyi da shi, shine dalilin da yasa ya sake ta ummm?”.

“Wallahi, kuwa to kin dai ji abunda ya faru”.

“Caɓɓ amma lallai yaron nan anyi ɗan iska, to wallahi sai naci ubanshi zai gane bashi da hankali wawa kawai, yarinyar ta sha wahalar rayuwa shine zai sake ta, daman abunda yasa ya aure ta kenan”.

“Ummm ummm Bilkisu ki rabu da shi kawai zai gane ai sai nan gaba tukunna, bana so ayi ta mishi maganar har yace ya dawo da ita, ki rabu da shi kawai ki saka mai ido sai yayi da na sanin sakin ta wallahi”.

“To shikenan Hajiya yadda kika ce haka za ayi bari na kira Surayya naji ya take don ni ko ita wallahi bata mun maganar ba”.

“To shikan sai anjima”. Hajiya ta kashe wayar ta.

Suna gama waya ta kira Surayya take tambayar ta, nan take ce mata ita anya bata san komai ba don ko kwana uku da suka wuce sunyi waya da Suhailan washegarin ranar ne ma idan ta kira wayar ta bata shiga, jiya kuma ta kira Uncle Habib yake ce mata baya gida ya ɗan fita idan ya koma gida zai kira ta wai wayar tata ce ta faɗa ruwa.

Hajiyan Surayya ce ta ɗura ashar tace”To wallahi ƙarya yake sakin ta yayi har saki biyu”.

Glass cup ɗin da yake hanun Surayya tana shan lemo shi tayi saurin saki ya faɗi ƙasa ya fashe tassa, Ishaq da yake cikin ɗaki yana saka kaya yayi saurin leƙowa don ganin me yake faruwa meye kuma ya fashe, saurin miƙewa tayi tana dafa ɗan cikin nata da ko tasowa be fara yi ba.
Tagaga tayi zata faɗi yayi sauri taro ta yana riƙe ta tsam a jikin shi.

Cikin kuka na fitar hankali tace”Hajiya saki fa kika ce, saki fa wayyo Allah na Suhaila na shiga uku, na lalace”.

“Kin lalace kuma”. Hajiyan tace daga can ɓangaren.

“To Hajiya me yasa, why uncle Habib? Why uncle Habib? me tayi mishi Suhaila me tayi mishi zai sake ta?

” Saboda matsalar ta wai ɗan iskan yaron nan ya sake”.

Lumshe ido tayi tana jin wani jiriri yana ɗibar ta tuni ta saki wayar tayi ƙasa ta faɗi ita kuma ta ƙara sulalewa a jikin ishaq, tuni nauyin ta ya rinjaye su suka zube a kan kujera su duka biyun.

Ishaq yayi saurin ƙara rungumota jikin shi yana me bata haƙuri don duk yaji abunda hajiyan take faɗa.

Babu abunda take cewa”Sai why uncle Habib why uncle Habib.

Barin jikin Ishaq tayi tana ɗakko wayar da ta faɗi a ƙasa nan da nan ta fara neman lambar Habib ɗin.

Tuni ishaq ya fizge wayar a hanun ta yana faɗin “Meyae hakan Surayya ki nutsu mana!?

” Bazan nutsu ba, bani waya ta Ishaq!!

Jin ta kira sunan shi gatsal babu Habibi yayi giving up kawai don yasan idan ya takura za ayi ba daidai ba.

Kiran Habib ɗin tayi, Habib kuwa da yake kwance a ɗakin shi abun duniya ya ishe yaga kiran Surayyan ya shigo wayar shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button