HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Saurin ɗauka yayi don shi a tunanin shi Suhailan zata ƙara tambayar shi.

Yana ɗagawa kuwa tace”Allah ya isa Uncle Habib, Allah ya isa wallahi kuma bazan taɓa yafe maka abunda kayi ƙawata ba,fashewa tayi da kuka tana ƙara faɗin why Uncle Habib? Why? Saboda budurcin ta dama ka aure ta? To wallahi ka sani this is the end of our relationship i am no more your favorite daughter……………

*_Haba Suryyy baby your words are too harsh ooooo_*…

_*How far i am good today?*_????

*Faɗam Ahmad*✍????✍????
[6/17, 9:08 AM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

*Page2️⃣4️⃣to2️⃣5️⃣*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

*Falalar Da Ke cikin Ziyarar Mara Lafiya.*

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yace; “Idan mutum ya ziyarci dan uwansa Musulmi (da ba shi da lafiya) to yana tafiya ne cikin lambunan aljanna yana tsinkar ‘ya’yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi. Idan da safe ne Mala’iku dubu sba’in za su yi ta yi masa salati har ya shiga maraice. Idan kuma da maraice ne mala’iku dubu saba’in za su yi ta yi masa salati har ya wayi gari.

 

_*New Start*_

“To wallahi ka sani i am no more your favorite daughter, babu ni babu kai duk wata alaƙa da take tsakanin mu na yanke ta ka je can ka nemi wata amma dai ba ni ba. Wallahi ka bani mamaki ban taɓa zaton haka kake ba”.

Zata ƙara magana yayi saurin cewa”Surayya don za Allah kiyi haƙuri ya isa haka please, sai in dawo da ita idan kina so amma don Allah kar kema kiyi fushi da ni haka please “.

” Hmm Allah ya kikaye wallahi mun kuma gama da kai wallahi, kuma in Allah ya yarda sai ta auri wanda ya ninka ka tunda har ka tozarta ta, ka watsa mata rayuwa ka barmata tarihin zama ƙaramar bazawara”.

Ta ƙarashe maganar tana kashe wayar ta haɗe da jefa ta kan one sitter dake gurin.

Kuka ta ƙara sakawa tana kwanciya akan cinyar Ishaq dake ta kallon ikon Allah.

Cikin rarrashi da tausayin ta yace”Please Habibaty don Allah kiyi shiru na roƙe ki don girman Allah kiyi haƙuri kinji ko”.

Gyaɗa mai kai tayi tana ƙara goge mai majina da ruwan hawayen da keta zuba daga idon ta a jikin rigar shi.

Ɗan ɗagowa tayi tana kallon yadda ta ɓata mai shaddar shi da ta sha guga, duk hawaye, ɗan taɓe fuska tayi kafin tace “Am sorry….”

Murmushi yayi mata sannan yace “It’s okay ai naki ne ki yi yadda kike so kin ji ko”.

Barin jiki shi tayi tana ɗakko wayar ta don kiran SUHAILA cikin faɗuwar gaba tace”Yanzu ya zanyi ta ina zan fara mata magana Habibi idan na kira me zance mata da wani idon zan kalle ta? “.

“Kar ki damu ki kirata kiji ya take tunda kinga yau kusan kwana haɗu da yin abun kar taga kamar baki kira ta ba ko”.

Ƙara goge fuskar ta tayi sannan ta dannan kiran SUHAILAN, nan taji wayar switched up.

Numfashi taja ta sauke ta kalli Ishaq tace:Wayar ta a kashe bari na gwada kiran na Ammi”.

“Okay” yace yana gyaɗa mata kai.

Kiran Ammi tayi ai kuwa bugu kaɗan ta ɗaga wayar, cikin sanyin murya Surayyan ta gaida Ammi tana jin kunyar abunda Habib ya aikatawa ƙawartata, Ammi kuwa da ta gane dalilin da yasa Surayyan take kameme tace”Kar ki damu Surayya na san baki da lefi ko kaɗan kuma baki sani da wuri ba shiyasa baki kira ba”.

“Haka ne Ammi wallahi nima yanzu hajiyan mu takira take faɗamun kuma na kira numbern Suhailan be shiga ba shine nace bari na kira ki ko tana kusa da ke”.

Ɗan gyara zaman ta Ammi tayi tace”Wallahi kuwa kinji yadda abu ya kasance har duka fa, ai abun ya bani mamaki.

“Duka Ammi!?” Surayya ta faɗa tana dafa ƙirjin ta”.

Nan Ammi ta zage tana bata labarin abunda ya faru from a to z babu abunda ta rage.

Ita dai SUHAILA tana zaune akan gado Nihla na jikin ta Ammi take ta wannan zubar sai dai kawai ta kalle ta tayi dariya don abun nata ma yanzu ya dena bata haushi sai dai kawai tayi dariya.

Su Ammi kuwa harda cewa”Har nayi magana da me mota anjima nan zamu kira shi mara kunyar ya buɗe mana gidan mu kwashi kayan mu. Sannan kuma Maman shi ko kira bata yi taji ba’asin abunda ya faru ba”.

Surayya tace “Wallahi Ammi kunyar ku take ji ita da Hajiya ta amma na san za su kira ku, babu komai Allah ya bata wanda ya fishi Amin ya Allah, idan Suhailan tana kusa ki bata mu gaisa please”.

Ammi ce ta miƙawa Suhailan wayar tana faɗin”Yo aikin banza kawai ai gwara da na gaya mata abunda yake raina, yaushe zan ajiye wani ballantana ma abun ya dame ni”.

Suhaila na karɓa ta kara a kunnen ta tana mata sallama.

Ai kuwa nan da nan Surayya ta fashe da kuka tana faɗin “Don Allah kiyi haƙuri wallahi bansan abunda ya faru kenan ba, duk lefi na ne ki yafe mun dama sai da kika nuna mun ba kyaso amma na nace dole sai kin auri uncle ɗina ashe shi bake bace a gaban shi, kawai yayi amfani da budurcin ki shine abunda yake gaban shi, don Allah ki yafe mun Suhaila don Allah”.

 

Suhaila kuwa saurin mayar da ƙwallar dake idon tayi tace”Shhhh, ya isa haka kar ki ƙara cewa komai kuma kar ki ƙara mun wannan maganr, kuma abunda Habib ya mun kar yasa ki canza mai haka Allah ya ƙaddara, kuma babu yadda muka iya da lamarin ubangiji , shi ya fimu sanin dai-dai a duk al’amuran mu, ɗan adam kawai yana nashi burin ne amma Allah ya riga da ya tsara maka rayuwar ka tun kan kasan da za a haifa ka so don haka babu komai, yin Allah ne”.

Surayya kam yanzu ta kasa daurewa kukan ta take tsakanin ta da Allah,tana daɗa bawa Suhailan haƙuri.

Cikin muryar ta da ta fara dishewa tace”To yanzu ya jikin naki ummm? Amma dai da sauƙi sosai ko?”

” Yes da sauƙi Alhamdullilah kar ki damu bari naje, za muyi waya anjima ko, ki gaida man isyaku”.
Ta ƙarashe maganr tana
murmushi me sauti.

Ɗan dariya Surayya tayi tana goge hawayen ta tace”Wato me hali baya fasa halin shi ko”.

“Eh mana” SUHAILA ta faɗa tana kashe wayar.

Bayan sun gama waya Mujahid ya karɓi no. Habib nan suka kira zancen kwashe kaya jikin shi ba ƙwari yana kwance a kan gadon nata yace sai sun zo yana gidan.

Nan su Mujahid suka ɗau hanya zuwa kwasar kaya. Inda za a wuce da su Kano kawai.

Hajiyan Habib kuwa da ƙyar ta samu takira Ammi suka yi maganar, ta kuma bata haƙuri ta nuna mata bata ji daɗin abunda Habib ɗin yayi ba, kuma bata so ta takwarawa SUHAILA da wallahi ko zai mutu idan tace sai ya mayar da Suhaila dole ya bi abunda take so, amma sam bata so ta shiga haƙin tane shiyasa bata bashi umarnin yin hakan ba.
Itama Ammi ta fuskance ta nan suka yi sallama ssuna yiwa juna fatan alheri.

A ɓangaren Jibril kuwa flight ɗin shi 4:00pm zai ɗaga united Kingdom.

Shiri yake cikin sauri don yana so kafin ya tafi ya ƙara komawa gurin Suhailan saboda akwai saƙon da yake so ya bata.

Wani ɗan box naga ya ɗakko yayi kyau sosai purple in color shi kuma zaren da ya ɗaure jikin box ɗin pink ne.

Sauri-sauri gudu-gudu ya fito daga cikin mansion ɗin da yake don wani ƙaton gida ne na alfarma ya haɗu ya kuma ƙero kai tsayawa ma fasalta kyaun gidan ɓata lokaci ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button