HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Motar sa yayiwa key yana dannawa me gadi horn tuni ya wangale mai gate ya fice a gidan.

15minute ce ta kaishi asibitin na SAUDA clinic da yake unguwar tudunwada da take cikin garin kadunan.

Yana fita a mota ya wuce zuwa office ɗin shi yana kiran wata nurse, tana zuwa ya miƙamata box ɗin yace “ga wannan ki kaiwa patient ɗin da take room 05 zuwa anjima kaɗan idan na tafi, ki tabbar kin bata fa”.

Ɗan risinawa tayi tace “Yes sir, Amma meye sunanta kar a samu akasi?

Nuni ya mata da jikin box ɗin yana faɗin” Gashi nan, don Allah ki bata karki bari a samu matsala fa”.

“In sha Allah”. ta faɗa tana fita daga office ɗin.

Sai da ya zagaya asibitin ya shiga ko wani ɗaki ya duba duk patients ɗin shi, sai dai da yazo dai-dai ɗakin Suhaila ya tsaya yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga ne.

Zuciyar shi ce tace mai ka shiga mana tafi gane ka koda zuwa nan gaba ne.

A hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, can ƙarshen gado ya hangota suna ta wasa da Nihla amma sai dai kana ganin fuskar kasan kawai tana yi ne amma bata cikin walwala sam.

Ammi ce tayi saurin cewa “Aaa maraba da doctor Jibril ashe ka shigo yau ma, ai nazaci har ka tafi wallahi”.

“Na shigo wallahi hajiya, ya me jiki kuma?

” Me jiki da sauƙi ka ganta nan sai sabgar ta ma take yi jiki yayi kyau kam”.

Ɗan kallon Suhailan yayi yace”Sannu ko, ya jikin? Amma dai baki jin komai ko”.

One glace tayi mai ta mayar da kanta kan Nihla, cikin sakin fuska tace”Alhmadullilah, gashi nan princess ɗina ma ta dame ni da surutu sai kace parrot”. Ta faɗa tana jan Kumatun Nihla .

“Ayya Allah ya ƙara lafiya tau”.

Ya faɗa yana ƙara kallon ta.

“Amin, na gode sosai” ta faɗa cikin sanyin murya tana ƙara bashi wani one glance ɗin.

A hankali ya juya ya fita daga ɗakin yana barin ward ɗin gaba ɗaya, office ya koma ya haɗa abunda zai haɗa sannan ya ɗauki keys ɗin shi, yana shirin fita daga office ɗin
Saurin da yake yi shiyasa wani ɗan ƙaramin hutu dake kan desk ɗin shi faɗuwa ƙasa, saurin duƙawa yayi ya ɗakko shi yana duba ko wani abu ya same, sai kuma yaga ko ƙwarzene be yi ba.

Kallon hoton ya tsaya yi daga nan ne kuma na samu damar ganin mutanen da suke cikin hotan.

 

Wata beautiful and pretty na hango a cikin hotan wadda baza ta gaza 23 years ba, a iya kallon da nayi mata, daga gefanta kuma Doctor Jibril ne daga gani ƙanwar shi ce don sunyi kama da ita sosai, wani saurayi na hango a gefanta ta rungumeshi tana cuna baki ba ƙaramun kyau tayi ba, shi kuma jibril ya ɗan kwanto zuwa kafaɗar ta daga ganin su dai siblings ne don sunyi kama sosai. Ɗayan saurayin na ƙurawa ido ina kallon shi don harma yafi Jibril ɗin kyau sai dai shi ya ɗan fishi duhu amma fa handsome ne don yafi kama da black americans domin shi har shigar shi ma irin tasu ce, ya wani naɗe wuyan shi da mopler ga uban takalmi dake ƙafar shi, ya saka wata uwar jacket, kai yadda kasan black Americans ɗin nan haka yake.

Ɗan Murmushi yayi yace”Ummm *KAUSAR* rigima ko ya za ayi da birthday ɗin ta oho, don wannan karon kam wallahi bazan je new yolk ba, ya faɗa yana kife hotan.

Da sauri ya fita a office ɗin yana barin asibitin gaba ɗaya…..

 

****

Kayan Suhaila kam har an kwashe su sun ɗau hanyar kano.

Da misalin ƙarfe huɗu nurse ɗin tayi sallama cikin ɗakin su Suhaila hannun ta ɗauke da wannan box ɗin tana ƙarasa shigowa ta gaida Ammi tana faɗin”Hajiya nan ne ɗakin su Suhaila ko? ”

Ammi ce tayi saurin cewa” Eh nan ne, me ya faru nurse?”.

” Dama doctor jibril ne yace a bata wannan ta faɗa tana miƙa mata box ɗin”.

Da sauri ta karɓa tana ƙare mai kallo, Suhaila da Fatima da suke zaune akan gado suna taɓa hira suka yi saurin juyowa suna kallon ta jin tace wai saƙo kuma daga gurin doctor.

Tana miƙawa Ammi tace “Sai anjima hajiya”.

“To to….” Ammi ta faɗa tana ƙara kallon box ɗin, saurin miƙawa Suhailan tayi tace “Yi sauri ki buɗe muga meye a ciki”.

Karɓa Suhailan tayi tana ƙarewa box ɗin kallo nan ta hango wani rubutu me shegen kyau an rubata shi da irin glitters pen ɗin nan, *DEAR SUHAILA* shine abunda ta gani daga saman box ɗin cikin wannan ƙayattacen rubutun.

Fatima ta miƙawa tace”Ki tafi da shi gida mun buɗe shi a tsanake”.

Har Ammi ta haye sama zata fara masifa sai kuma naga tayi shiru ko me ta tuna oho.

Fatima kam karɓa tayi tana ajiyewa a gefan ta.

Haka rayuwa ta cigaba da dafiya har ranar sallamar Suhaila tazo nan aka sallame su suka koma gida, tunda suka koma Ammi take nacin sai an boɗe mata box ɗin nan ta ga meye a ciki kafin ta wuce gida ita kuma Suhaila tace gaskiya baza ta buɗe ba sai ta nutsa kuma tayi mata alƙawarin ko meye aciki zata sanar da ita.

Haka nan dai Ammin ta haƙura saboda bata son takurawa Suhailan ko meyesa yanzu kuma oho.

Washegari da wuri Ammi ta shiraya zata tafi gida, nan suhaila take ce mata ta tafi da kayan lefan ta ita ba abunda zata yi da su bata son ganin su idan taje ta bawa Farida ta zaɓi abunda take so, sauran kuma sai a bawa su Bahijja itama kuma idan akwai abunda take so ta ɗauka.

Ammi kam bata mata wani musu ba ta ƙarɓi kayan.

“Ammi na amma ki bawa Mubarak duka turaren da yake ciki please, wanda ƙanshin yake na mata sai kuyi amfani da shi kawai”.

To Ammin ta amsa mata da shi.

Bayan Ammi ta shirya zata tafi take faɗawa SUHAILA da ta karɓo ɗan kuɗin da ake biya na NYSC ta raba biyu ta dinga aiko mata da rabi.

To tace mata tana komawa ta kwanta. Nan Fatima ta rakata titi ta hau napep.

Bayan Fatima ta dawo ta ɗan ja numfashi tace “Wow masha Allah we are free now, finally Ammi ta wuce gida wallahi bakiji daɗin dana ji ba”.

“Uhmmm” Suhailan tace tana ƙara gyara kwanciyar ta.

Ɗala mata duka Fatima tayi tace”Au abunda zaki ce kenan ƴar rainin hankali”.

Ɗan sosa gurin SUHAILA tayi tana faɗin”Kai ya Suhaila banfa gama warkewa ba”.

Dariya suka yi su duka biyun suna jin farin ciki mara misaltuwa.

*****

Suhaila ce zaune akan bed ta jingina da jikin fuskar gado hannun ta riƙe da littafi ga Nihla da Walid kwance a jikin ta hannun ta kuma riƙe da story book daga gani karatu take musu bacci ya ɗauke su.

A hankali ta gyara ta miƙa hannun ta ta ajiye littafin a kan bed side, gyara musu kwanciya tayi, sannan ta sauka akan gadon, drawer ta buɗe nan na hango wannan box ɗin a saman kayan ta, hannun ta miƙa ta ɗakko shi ta dawo ta zauna a saman bed ɗin tana ƙara kallon abunda ya rubuta a saman box ɗin. *”Dear Suhaila”*

Da mamaki take kallon the word dear, to me yasa zai kirata da wannan sunan don ita ko a hanya ta ganshi baza ta sheda shi ba.

A hankali ta fara kwance pink maɗaurin da ke jikin kwalin.

Tana gama buɗewa ta ga wani abu me shegen kyau black and white in color, saurin ɗakko abun tayi tana ƙare mai kallo kamar ta taɓa ganin shi a wani gurin nan ta shiga tunanin inda ta taɓa ganin shi.

“Na tuna” ta faɗa tana ƙara ɗaga abun da jikin shi duk ƙyalli yake.

Ɗan dariya tayi one side dimple ɗin ta yana fitowa”Uhmmm dream catcher ko, na THE HEIRS “. Ta faɗa tana ƙara faɗaɗa murmushin ta.

Ƙara kallon kwallin tayi nan ta hango wani littafi ɗan ƙarami purple in color sai kuma wani glitter pen shima purple in color, daga gefan littafin ta hango wata purple takarda me shegen kyau sai wani ƙaramun box shima daga gefe.

Purple takardar ta ɗakko wadda sai ƙanshi take bugawa ta buɗe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button