HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Tau malama idan kin gama sai ki bani zan yi aiki a ciki”.

“Auuu kice har kin ɗauke kayan ki zaki shige ɗaki, tau ai ni ban yi miki satar ba, a bani ko guda biyu ne”.

“Ummm A’a gaskiya bazan baki ba”.

“Abbu kaji ta ko, gaskiya a dena mana ƴar ware, idan an siyo mata nata muma sai a siyo mana namu da ban, yadda ba ruwan mu da raƙo ballantana a yanƙwana mu”.

“Aaaa gaskiya kun sa mun mama na a gaba, tau daga yanzu za a dinga siyo muku naku in sha Allah. Mama na ki sammata, kaɗan kinji”.

“Yarinya kimci darajar Abbu da bazan baki ba”..

“Nidai naji a bani kawai”.

******

Washegari da asuba ita ta fara tashi kamar kullum, nan ta bugawa su Ammin ta ƙofa, kafin ta tashi Farida tayi alwala.

Har ɗakin Mubarak taje ta tashe shima.

“Wayyo Allah na ya Suhaila wai har garin ya waye?

” Ban sani ba, oya malam, tashi kaje ka yi alwala yanzu Abbu zai fito ku wuce masjid”.

“Wallahi ji nake kamar yanzu na kwanta. Amma dai yau babu subih recitation ko?

” Hmm wa yasan sanda ka kwanta, may be ma ka raba dare kana buga game, wallahi idan baka yi wasa ba sai na lalata kayan kallon da suke ɗakin nan Allah kuwa, baka da aiki sai na game ko Mubarak, da ka dawo daga makaranta nan zaka hau, idan zaka yi bacci shine azkar ɗin ka, idan ka tashi da safe kafin ka tafi school da shi kake breakfast.

“Sannan kuma subih recitation kasan is a must so, ka ma dena yaudarar kanka ka tashi kawai, kuma wallahi sai nayi wa Abbu maganar yau zaka sani”.

 

Bayan sunyi sallar asuba ita da farida nan suka fara karatun su har sai da su Abbu suka dawo, nan suma su kayi joining ɗin su.

Bayan kowa ya gama muraja’an shi, shi kaɗai sannan su kayi general wanda suke yi a tare, after sun gama ne kuma suka yi azkarru subih, bayan sun kammala Mubarak yace “Waye da addu’a yau??

” Ɗan rainin hankali ai kaine da addu’ar kake tambayar mutane”. Cewar Fadila.

“Ya Suhaila wai nine da addu’a? ba ni nayi shekaranjiya ba, ki ka yi jiya, yau kuma Fadila”.

“A’a Mubarak ni nayi shekaranjiya, jiya Fadila tayi, yau kuma kaine”.

Abbu ne yace”To ya isa haka, Mubarak dai yau baka son yi mana addu’ar nan, don haka na karɓe ka bari nayi mana”.

Nan Abba yayi musu addu’a sosai sannan suka shafa.

“Amm Suhaila don Allah a saka mun ruwan wankan nan da wuri, sannan a haɗa mun breakfast don da wuri zan fita, jiya na makara sosai a makaranta”.

“Okk Abbu in sha Allah”

Nan ya koma ɗaki.

“Ya Suhaila zan yi baccin 30minute ki tashe ni please, amma fa sai 30 minutes ɗin ta cika”.

“To ubana! Kana SS2 student amma kana behaving kamar wani ɗan junior, don ka ga ban yi wa Abba maganar ba shiyasa har kake da damar komawa bacci ko?

” Please mana, haba Aunty na kiyi haƙuri don Allah”.

“Hmm kai ka sani, for your own good am not killing my self ooo, kuma wallahi bazan tashe ka ba, duk sanda ka gama baccin kayi shirin makarantar”.

“Nima fa baccin nan zan koma gaskiya”.

“Ahan! Ke kuma am eager na ga kin fara makarantar nan, naga yadda za kiyi malalaciya kawai, wallahi wannan baccin idan akace kiyi baza kiyi shi ba, musamman ma kinje kin ɗakko physiotherapy, zaki gane baki da wayo wallahi”.

Kitchen ta shiga ta fara haɗawa Abbun su breakfast ɗin nashi, kafin ta gama ruwan da ta saka a kettle har yayi zafi, nan ta juye shi a flaks.

Laptop ɗin ta ta janyo ta cigaba da abunda take yi, tana nan a zaune taji muryar Ammin ta ya fara tashi da alamun kamar faɗaɗa take yi.

Rana ɗaya ɗaya ce zata zo basu yi irin wannan abun da safe ba, kuma yawanci akan abunda ba dole bane ake hayaniyar, tayi ta tada jijiyoyin wuya tana masifa akan abunda be kai ya kawo ba.

“Ohhh ni Suhaila yau kuma ko me ya haɗasu oho”.

Tana nan zaune Abbun nasu ya buɗo ƙofa ranshi a ɓace.

“Suhaila ina ruwan zafin?

” Gashi Abbu, harda breakfast ɗin ma”.

“A’a ki barshi a nan, idan na fito daga wanka nan zan zo naci kawai”. Ya faɗa yana maida ƙofar ya rufe.

Bayan kamar 15 minute ya fito a shirye harda briefcase nashi da alama ya gama shiri tsaf kawai wucewa zai yi.

Nan Suhaila ta kawo mai breakfast ɗin.

Yana cikin yin breakfast ɗin
Ammin su ta fito daga ɗaki.

” Abban Suhaila naga har ka gama shiri, da alama wucewa kawai za kayi baka ce mun komai ba, kuma lokaci tafiya yake, ka ga yau saura kwana biyar abun nan nasu,gwara a fara shiri tunda akwai abubuwa da yawa”.

“Ohhhh!! Allah abun godiya, Asiya kin fiso muyi ta jinjina magana kamar cin kwan makwaniya, nace miki bani da kuɗi, iya abunda zan iya kenan, beside am just a principal, a teacher matsayi na be kai nayin duk wai’annan unnecessary abubuwan da ki ke lissafa wa ba, wani photo calender, memo da dai sauaran su, Allah na tuba ko bikin Suhaila ne za ayi ba lallai nayi wa’annan abubuwan da kike faɗi ba ballantana kuma kawai don za tayi graduating kice sai nayi abubuwan da basu da amfani ba”.

“So, don haka ki bari kawai bani da kuɗi yanzu gaskiya”.

“To ai indai rashin kuɗi ne yanzu ba sai ka damu ba, na faɗa maka akwai 50k ɗin hajiya Khadija a guri na, ba sai mu ranta ba, ka ga idan aka haɗa da 30k ɗin da ka bayar ya ishe mu dai muyi manage ko”.

“Kuma ka ga bata da wata matsala, zuwa ƙarashen wata idan anyi albashi sai ka biya ta ko?

” Haba Asiya 80k fa kenan duk a ƴar wannan hidimar”.

” To ai wallahi a haka ma na tsaigata abun ne don kar a kashe kuɗi da yawa, idan ba don haka ba ai har hall sai mun kama wallahi”.

Ita kam Suhaila tsabar baƙin ciki ma kasa motsi tayi a inda take, ballantana ta tashi ta bata waje.

“Hmm Allah ya kyauta , tunda kin ƙudiri niyya ko nace kar kiyi ma sai kinyi Asiya, Allah ya hore mun na biya, na fita sai na dawo”.

“Yauwa to, a dawo lafiya, haba yanzu naji magana da ka tsaya sai matse hannu ka ke”.

Bayan ya fita da kamar 10minute Suhaila dai ta kasa haƙuri har sai da tayi magana.

“Ammi nace miki ba sai an takura kai ba, duk fa ba wani abu bane, ko abinci akaci ai ya wadatar, albarka ake so, kuma indai biki ne ai yanzu aka fara tunda akwai wata hidimar a gaba”.

“To mara kunya! Ke ga me uba ko? Wato kina jin tausayin shi, wannan maganar ki ce da zaki saka bakin ki a ciki iyee! Ko an gaya miki saboda ke nake yi, to don na fita kunyar mutane zan yi souvenirs ɗin nan, kar ma kiyi tunanin don ke zan yi yauwa”.

“Ammi kiyi haƙuri, Allah yasa shine mafi alkhairi, bari naje na shirya nima zuwa 8:00 zan wuce, na gama abunda zanyi da wuri na dawo gida, amma daga makaranta zan wuce gidan Surayya muji yadda za ayi wajen shirya abubuwan”.

“Ahan! Ko ke fa, ai naki addu’a kawai, amma da kin tsaya kina wani iyayin banza, ki gaishe ta, amma gaskiya kar ki daɗe ki dawo da wuri”.

Bayan ta gama shiri ta wuce zuwa makaranta, tana zuwa bata wani sha wahala ba ta ƙarasa abunda za tayi nan suka haɗu da Abubakar.

“Asslama alaikum malamar mu kin wuni lafiya ya zafifi?.

Yau kam komai nata blue black ne sai niqab ɗin ta da yake black.

” Wa alaikum salam, Alhamdullilah”.

“Don Allah yau ina so ki ɗan bani lokaci muyi magana ba don hali na ba, don Allah”.

Ɗan jimm tayi, da tayi niyar baza ta kula shi ba, amma kuma sai tayi tunanin gwara kawai ta gama da shi one’s and for all.

“Okay bismillah” tayi mai nuni da students chair ɗin da take gurin wanda duk inda ka zagaya a makarantar akwai shi.

“Ina jin ka saboda sauri nake yi”.

“Wai me yasa don Allah kike wulaƙantani? ni a iya tarihin da na sani mata ustazai basu da ɗaga kai, sannan kuma basu da wulaƙanci, sa’annan kuma suna da ƙarancin girman kai, amma ni naga ina ta binki na haɗa da aminiyar ta ki amma abun ya ci tura”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button