ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Eh mana” ta faɗa tana ɗauraye lemon grass da na’a – na’a dake hannun ta”.
“Alhamdullilah”. Ya sake faɗa yana ƙara leƙa tukunyar.
“Kai Fatima mun zama ƴan gayu harda spicy tea za a bamu, masha Allah dama na gaji da madarar nan”.
Ɗan kallon Fatima yayi yaga ta ɓata fuska tana ƙoƙarin zare hanun ta a cikin nashi.
“Aaaa, me kuma ya faru Umm Nihla? “.
“Ni kawai ka barni na tafi yaushe rabon da nayi girgi ka yaba haka”.
Suhaila ce tayi saurin juyowa tana kwashewa da dariya tace”Hhh some one is jealous here”.
Dariyar da Mujahid yake riƙewa ce tayi saurin ƙwace mai ba tare da ya shirya ba, ɗan kamo ta ya ƙara yi yace”Am sorry Qalbi na, it was just that kin daɗe baki mun ba kuma kin san ina ƙoƙari tunda favorite food ɗin na ne,amma wane wata Aunty Hala ai babu haɗi ma”. ya faɗa yana janta zuwa palo.
Ita kuwa Suhaila dariya tayi kawai tana cigaba da aikin ta.
Bayan sun isa palo sun zauna akan kunjera kira ya shigo wayar Fatima tana dubawa taga Ammi ce ke kiranta. Ɗaukan kiran tayi tana tunanin me yasa Ammi ta kira da safe haka.
Bayan sun gaisa Ammin take tambayar ta wai yaushe SUHAILA zata dawo tunda jiya ta gama service ɗin ta, ɗan jimm Fatima tayi tace”Ammi jiya ne fa ta karɓi certificate ɗin zata dawo idan komai ya kammala”.
“Meye zai kammala Fatima? Sati ɗaya na baku SUHAILA ta dawo gida tunda ku baku da hankali mutumin nan yayi ƙoƙari fa, tunda Allah yasa ta gama ba sai a bashi fili ba”.
Cikin ƙosawa da maganar Ammin Fatima tace”Ammi kedai kawai akwai abunda kike so idan tazo ta miki idan ba haka ba ai kin san Abban su Nihla bashi da wata matsala”.
“Nidai na faɗa muku”. Ammin ta faɗa tana kashe wayar ta.
Ɗin jimm Mujahid yayi yana kullon yanayin Fatiman, da damuwa akan fuskar shi yace”Me ya faru Ammi na son Suhaila ta koma gida ne? “.
” Eh” ta faɗa tana gyaɗa mai kai.
“Kar ki damu kinji ko things will be okay” ya faɗa yana kwantar da kanta a ƙirjin shi.
Ita kuwa Suhaila tana kitchen har ta gama haɗa breakfast, a dining area ta jera komai sannan ta leƙo cikin palon tana faɗa musu komai is ready.
A tare suka nufi dining ɗin,nan suka fara cin abincin, Mujahid kam yaji daɗin abincin sosai sai yabawa Suhaila yake yana tsokanar Fatima.
Bayan sun gama cin abinci Mujahid ya wuce gurin aiki, Fatima take faɗa Suhaila abunda Ammi tace mata.
Ɗan jimm tayi sannan tace”Ya Fatima Allah yasa shi yafi alheri Allah kuma ya kaimu nan da sati ɗayan, ni wallahi yanzu na dena damun kaina akan duk wani abunda Ammi za tayi”.
“To Suhaila idan kinji me zaki yi mata ne wai?”
” Koma menene zan koma gidan”.
****
Da misalin ƙarfe 10 na dare Suhaila ta ɗakko letter ɗin da doctor Jibril ya bata tana kofe no. Na farko da ta fara gani wanda yake kama da no. nigeria bayan ta kofe no. Ta fara tunanin to idan ta kira me zata ce mai? tace ita ce Suhaila ko me, da ƙyar ta daure ta kira no. Amma switch off kwatakwata ma bata shiga, ɗayar no. Tayi dealing wanda tayi kama da no. Waje shima taji baya shiga sai dai ya mata ɗut ɗut kawai ya ɗauke, bata ji daɗi ba sam haka nan ta ajiye wayar tana maida lettern inda ta ɗakko ta…
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Suhaila kullum sai tayi trying no. Jibril amma sam baya shiga har sati ya zagayo, ranar kuma zata ɗau hanya zuwa Kano.
Tana zaune a kan gado tana ƙarasa haɗa kayan ta sai ga Nihla ta shigo ɗakin da gudo tana kuka.
Da sauri Suhaila ta ajiye abunda yake hannun ta tayi saurin ɗaukan ta tana tambayar ta me aka yi mata.
Cikin kukan su na shagwaɓa irin na yara tace”Aunty Hala wai tafiya zaki yi ki barmu inji Walid”.
Ɗan goge mata hawayen fuskarta tayi tana ɗorata akan cinya tace”Aa my princess zanje na gaishe da Ammi ne, Amma ai zan dawo kar ki damu kinji ko”.
“Aunty Hala ki tafi dani mana”.
Ɗan jan kumatun ta Suhaila tayi tace”My princess rigima, to exams ɗin kuma wa zai miki ummm? ki bari idan kuka gama sai Ummin ki ta kawo ku kinji ko?”.
Daɗa gyaɗa mata kai tayi sannan ta sauka akan cinyar Suhailan tana faɗin” Bari naje na faɗawa Walid ba haka bane”.
Riƙe mata hannu Suhaila tayi tace”Kar na ƙara jin Walid ɗin nan, sunan shi ya Walid kinji ko”.
“To” ta amsa mata tana barin ɗakin.
Bayan ta fita ta ƙarasa haɗa kayan ta tana kamalle su guri guda, har dream catcher ɗin ta duk ta ɗauka.
Sakkowa tayi ƙasa tana kallon yadda suka yi shiru su dukan su harda Mujahid kuwa.
Cikin basarwa da son kawar da damuwar su tace”What is happening here? Naga kowa yayi shiru duk kunyi jigum kamar anyi mutuwa”. Ta ƙarashe maganar tana zama kusa da Nihla itama tana tagumin.
Ɗan zungurar Nihla tayi tana ɗan mata cakulkuli nan da nan ta fara dariya tana “Wayyo Aunty Hala ki bari don Allah”.
Nan da nan kowa ya sake ana wasa da dariya, bayan wasu ƴan awanni ta ɗebo kayan ta ta fito da su ta fara sakawa a mota har ta kammala.
Nan suka fara shirin raka ta zuwa tasha amma duk jikin su babu ƙwari yadda kasan ance musu ta tafi kenan.
Har tasha suka kaita nan Nihla ta fara kuka ganin da gaske aunty Halan ta tafiya zata yi,har sai da ta kusa saka Fatima kuka da ƙyar Suhaila ta samu ta rarrashe ta tayi shiru daga kuka kuma bacci ya ɗauke ta.
Nan suka yi sallama Fatima tace mata ta gaida gida ta gaida su Ammi da kowa da kowa.
Awa uku ne cass ya kai Suhaila gida saboda yanayin yadda hanyar ta lalace bata da kyau sam.
Tana shiga unguwar su taji wani daɗi yana ratsa ta, yau ita ce a kano, a kanon ma a unguwar su, kuma gidan su zata je taga kowa nata, Abbun ta Maubarak da kuma Farida.
Suna ƙarasowa da me napep ƙofar gidan su ta fara sauke kayan ta kafin me napep ɗin shima yazo ya taya ta.
Mubarak kuwa da yake kwance a ɗakin shi yana buga game yaji tsayawar napep da gudu ya fito yana buɗe ƙofar,ai nan ya buga wani uban tsalle yana rungume Suhailan yace”Oyoyo my ya Suhaila, oyoyo”. Ya faɗa yana daɗa ƙwaƙume ta a jikin shi har ya kusa yarda ita.
Ɗan fara rabashi tayi ta jikin tana faɗin”Wayyo Mubarak don Allah ka sake ni karka yarda ni”.
Ɗan sakin ta yayi nan tayi smacking goshin shi tace”Seee you wani ƙato da kai saura fa kaɗan ka yarda ni”.
. “A haba ya Suhaila wane ni”. Ya faɗa yana fara ɗaukar mata kayan ta zuwa cikin gidan.
Farida ma da gudu ta fito jin alamun Suhailan ce ta dawo ai kuwa nan suka haɗe a tsakar gida, itama tsallen tayi tana faɗin” Ya Suhaila Oyoyo”sannan ta rungume ta tana jijjiga ta”.
“Wayyo Allah na yau yaran nan kam sai kun ɓalla ni hankalin ku zai kwanta”. Farida kuwa bata sake ta ba har sai da Suhailan ta raba jikin ta da nata, nan suka shiga cikin gida.
Ammi ta samu akan kujera tana zaune tana kallon bollywood, zama tayi akan kujerar tana faɗin “Ammi sannun mu da gida”.
Ɗan kallon ta Ammin tayi tana ganin yadda tayi ƙiba ga wani fresh da tayi kamar ba ita ba.
“Yauwa sannun ku da zuwa mutanen kaduna, kun sha hanya”.
“Wallahi kuwa Ammi”.
“Bari na shiga toilets na fito wani mugun fitsari nake ji wallahi”.
Shiga toilet tayi bayan ta gama fitsarin ta fito tana gaida Ammin nata, nan fa hira ta kacame tana ta basu labarin yadda abubuwa suka kasance har certificate nata da ta karɓo.
Ammi taji daɗi sosai ganin babu wani damuwa a tattare da Suhailan sai ma farin ciki da kuma annashuwa.
Farida ce ta shiga kitchen ta ɗebo musu abinci suka ci.
*******