HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Suna zaune suna hira da daddare Abbu ya dawo, ai kuwa yana shigowa Suhaila ta tashi da gudu tana rungume shi, tana farin cikin ganin Abbun nata, shima cikin farin ciki yake mata sannu da zuwa.

Nan fa shima yayi joining ɗin su don tare suka ci abinci ranar sai da suka kai kusan 12:00 na dare ana hira cikin jin daɗin dawowar Suhailan da kuma farin cikin ganin ta babu damuwa ko ɗaya a tattare da ita…..

*******

_*Hihihihi har yanzu dai muna good mood, alot of dramas are coming, ku dai kawai ku cigaba da bina, and also this is not a love story don cikin 100%the love scene be fi 30%ba*_

*_Thanks for your comment especially mijin bahaushiya and Ala’amarin Suhailat fans group i cherish you guys❤️. face book readers naga kuna ta tambayar whatapp group ɗina duk me son yayi joining zai iya tuntuɓa ta a wannan lambar 08144426415_*

*_ma’asalam faɗma Ahmad_*✍????

 

[6/22, 1:29 PM] Ya Umar: *????????AL’AMARIN *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page 2️⃣8️⃣to2️⃣9️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

*Addu’a Yayin da Ake rufe Idanun Mamaci*

اَللَّهُمِّ اغْفِرْ (لِفُلاَنٍ بِاسْمِهِ) وَارْفَعْ دَرَجَتَهُ فِي الْمَهْدِيِّينَ، وَاخْلُفْهُ فِي عَقِبِهِ فِي الْغَابِرِينَ، وَاغْفِرْ لَنَا وَلَهُ يَا رَبَّ الْعَالَمِينَ، وَافْسَحْ لَهُ فِي قَبْرِهِ وَنَوِّرْ لَهُ فِيهِ.

Allahummagh-fir li-fulanin (Bismahu) the dead- warfa’ darajatahu fil-mahdiyyeen, wakhlufhu fee ‘akibihi fil-ghabireen, waghfir lana walahu ya rabbal-‘alameen wafsah lahu fee kabrih, wanawwir lahu feeh.

Ya Allah! Ka yi masa gafara (sai ya ambaci mamacin da sunansa), Ka daukaka darajarsa a cikin shiryayyun bayi, kuma Ka maye masa bayansa a cikin wadanda ya bari; Ka gafarce mu da shi, Ya Ubangijin talikai! Kuma Ka yalwata masa a cikin kabarinsa, kuma ka haskaka shi gare shi.

*_Joning catering class_*

Washegari da safe bayan sunyi break fast kowa ya kama gaban shi ya zama daga SUHAILA sai Farida a gidan sai kuma Ammin tasu.

Suna zaune suna ɗan hira sama sama Ammi fa kalli SUHAILA tace”Kina ji ba SUHAILA “.

Ɗan kallon ta Suhailan tayi tana ƙara mayar da hankalin ta kan Ammin tace” Eh Ammi inajin ki”.

“Dama dalilin da yasa nace ki dawo ina so kiyi joining class ɗin da Hajiya Khadija take yi, saboda naga a can ɗin ba abunda kike yi sai zaman gidan, kinga gwara mutum ya kama sana’a a hannu kafin Allah ya kawo aiki ko ba haka ba”.

Ɗan shiru Suhaila tayi tana ɗan jan numfashi tace”Haka ne Ammi dama nima akwai wani cake class da nake so na shiga, amma tunda kinyi suggesting na Aunty khadijan sai naje natan ai babu komai”.

Kallon idon ta Ammi tayi tana son ganin akwai damuwa a cikin su kokuwa, duk yadda ta kai da ta gano wani abu babu abunda ta gani.

Haka dai aka cigaba da taɓa hira.

Washegari Suhaila ta shirya zuwa gidan Aunty khadijan dake aviation quaters dake nan garin kano don biyan kuɗin class ɗin nata kuma Ammi ko Asi bata ba ta ba, da ɗan kuɗin da take adanawa da su ta je ta biya sai dai Amma ita anyi mata ragi 50k ake joining ita kuma aka bar mata 40k, class ɗin ana koyan abubuwa da yawa cake, doughnut, meat pie, spring roll, samosa, cinnimon roll, leches cakes, frusting na cake, da kuma decorations and other food stuffs duk ana koya a gurin ta.

Aunty khadija kuwa taji daɗin ganin Suhailan yadda ta koma ba wani damuwa a tattare da ita, da ace ƴaƴa maza gare ta da sai ta haɗa ta da ɗan ta saboda yadda Suhailan take da hankali ga kuma nutsuwa da girmama na gaba.

Bayan ta biya take sanar da ita ai next monday za a fara class ɗin kafin nan duk wainda za su biya sun biya.

Cikin jin daɗi Suhaila ta koma gida tana sanar da Ammin nata yadda suka yi da Aunty khadija.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda har yanzu dai Ammi bata yiwa Suhaila wani abu da zai ɓata mata ba, itama Suhailan tana kiyaye ɓacin ran Ammin nata.

Kusan kullum sai sunyi waya da princess ɗin ta inda koda yaushe take tambayar ta yaushe zata dawo gidan.

Kwanakin ba wuya gashi har monday ta zagayo inda yau ne su Suhaila za su fara class ɗin su.

Haka Aunty khadija ta koya musu abubuwa da yawa wanda Suhaila tun a sati na biyu ta iya baking cake haɗe da decorating ɗin shi don a cikin wainda suke koya ita ce ta uku a wainda suka iya har ake basu su koyawa wainda basu kai su ba, aunty khadija tana jin daɗin aiki da su sosai don wani zubin su take barwa komai, ko kwangilar biki aka bata, su take kira su haɗu da yaranta suyi komai, don wata ran ma Suhaila har kwana take a gidan.

Yau kusan satin ta huɗu da dawo daga kaduna amma bata sanar da Surayya ta dawoba, abun yayi wa Surayya ciwo sosai itama shi yasa ko sau ɗaya bata kira ta ba kuma bayan ta san ta haihu ai ko barka ta kira ta mata.

Yau SUHAILA tana gida kasancewar week ends ne suna zaune a palo ita da Farida sai jin sallamar Surayya suka yi.

SUHAILA tana jin muryar Surayya taji gaban ta yayi munmunar faɗuwa saboda ta san bata kyauta mata ba.

Tana shigowa palon ta tsaya tana kallon SUHAILA ta saki baki tana kallon irin kallon da Surayya take mata.

Ɗan miƙewa Suhailan tayi da niyyar tarbar Suryyan amma ta ɗaga hannu tana faɗin”Ba gurin ki nazo ba, wucewa nazo yi nace bari na zo na gaishe da Ammi”.

Farida ce tayi saurin tashi tana karɓar babyn hannun Surayya tace “Haba mana ki shigo ki zauna, ai ko Ammin ma ba kya jira ta a tsaye ba”.

“Tana nan ko bata nan naji gidan shiru kamar ma bata nan ko?”.

“Wallahi bata nan” Farida ta faɗa tana miƙawa SUHAILA babyn ita kuma ta shige ɗaki don basu guri.

Miƙo hannu surayy tayi zata karɓi baby Najwa SUHAILA tayi saurin janye hannun ta tana ƙara rungume yarinyar a jikin ta.

Juyawa Surayya tayi zata fita a palon tace”Ai kin san gida na duk lokacin da kika gama zaki iya kawo ta”.

Da sauri SUHAILA ta tashi ta riƙo hannun ta tana juyo da ita tace”Haba mana Surayya meye haka?”

Cikin masifa da tsiwa Surayya tace” Haba mana Surayya meye haka kike cewa, ke baki ji kunyar abunda kika faɗa ba, har wani zai iya shiga tsakanin mu ummm Suhaila? Har Habib zai iya sa ki mun abunda kika yi mun, am so disappointed, ko kuma baki da lefi duk ni naja miki abunda ya faru, da ban yi insisting na takura miki ba da duk haka bata faru ba, amma kiyi haƙuri don Allah idan haka kike so mu cigaba da tafiya fa ni’ima shikenan kawai”. Ta ƙarashe magnar tana zama akan kujera haɗe da fasa kuka me cin zuciya.

Kwantar da Najwa tayi akan kujerar da ta tashi ta koma kusa da Surayya ta zauna tana me rungume ta tace “Bazan iya ce miki komai ba yanzu, ba abunda zan iya faɗa Surayya amma kiyi haƙuri, and let go back to normal, let pretend kamar Habib be taɓa shiga tsakanin mu ba.

Daɗa fashewa da kuka Surayya tayi tace” Kiyi haƙuri ni naja miki komai ki yafe mun please”.

“Shhhh” Suhaila tace tana ƙara rungume Surayya. Tun daga nan komai ya wuce tsakanin Suhaila da Surayya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button