HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Yau take monday su Suhaila an wuce zauwa Aviation quarters inda a wannan satin ne kuma za su kammala class ɗin saboda dama sati huɗu ne daga nan kuma akwai bikin wata wadda suke class tare kuma a nan kusa da su aunty khadijan suke domin kuwa su aka bawa komai da komai na bikin wandda yake ɓangaren abinci.

Ita kuwa Hunaida amarya ana ta shirye shirye inda yanzu haka ma su Suhailan a gidan su suke ana ta shafta, kai idan ka ga Suhaila baka ce ta shiga cikin ƙuncin rayuwa ba, dama akwai ta da tsokana da kuma barkonci, yanayin yadda rayuwa ta kasance shi yasa ta zama shiru shiru kamar ba ita ba, yanzu kuwa da ta bar komai ya wuce gashi har ta fara dawowa daidai.

Suna zaune aka kira Hunaida a waya ai kuwa da sauri ta ɗaga tana faɗin”shegiya KAUSAR kun sauka a abuja ne? ” daga can ɓangaren Kausar tace” Eh mun sauka zuwa gobe zamu shigo kano ki tanadar mun abun daɗi don kin san hali na ba wasa yarinya”.

“Hmm kar ki damu duk abunda kike so za a baki, kayan daɗi har se kin gaji da su”.

“To shikenan zan gani ai”.

“Ke da su wa kuka zo? kuma da wa da wa zaku taho daga abuja? don na son akwai masu nace muku da yawa musamman ma dangin Baba *Umar me shadda* na san sai wannan me idon mujiyar ta biyo ku kamar mayya”.

Kausar ce ta kwashe da dariya daga can ɓangaren tace”Ke ma kin san dole ne don wallahi a gidan ma muka tarar da ita, a tunanin ta ya *AHMAD* zai zo, bata san shi ko a can hilton ya daɗe be ze zo gida ba ballantana kuma yazo Nigeria, yanzu ina tare da Hajiya, sai kuma ya *JIBRIL* da muka taho da shi amma har ya wuce kaduna ban sani ba ko zai zo bikin oho mishi kin san ban fiya son shiga sabgar shi ba can ta matse mishi shima duk ya wani canza, ummm kedai kawai sai mun haɗu akwai labarai wallahi sai munzo goben ki gaida Ummi”.

“Okk zata ji” Kashe wayar Hunaida tayi tana faɗin “Yeeee sai ni wallahi, kallon Zubaida tayi wacce take ƴa a gurin aunty khadija tace” guess what?

“Kausar zata zo ko”.

“Yess, yaushe rabon su da Nigeria kinsan shekara shida kenan yau gashi biki na zai kawo su amma naji daɗi sosai wallahi”.

Suhaila ce tace”Dama ai haka shi sha’anin biki yake akwai kiran jama’a”.

*****

Washegari bayan sallar azahar su Kausar suka iso garin kano inda farin ciki a gurin Hunaida kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha itama Ummi taji daɗin zuwan ƴar uwar tata sosai don bata taɓa zaton Hajiya *KULTHUM* zata zo bikin nasu ba.

Haka kwanaki suka wuce inda yau ne kuma za a fara event wato bridal shower, ranar kuwa su Suhaila ne suka yi serving komai kuma cikin akon su wanda yake white and light purple sai dai su amma jilbab suka ɗinka, suka yi rolling da white veil sunyi kyau sosai kai baka ce serving suke yi ba don a tsare cikin kuma nutsuwa suke komai nasu.

Washegari ma ranar kamu haka akayi, sunyi ankwansu kuma a haka suka yi serving cikin nutsuwa, tun ranar kamu Kausar da Suhaila suka fara sabawa saboda halin su yazo kusan ɗaya akwai tsokana da kuma barkwanci sai dai ita Kausar bata da Hakuri sam.

Washegari ranar dinner su Suhaila basu yi anko ba ita da wasu daga cikin ma’aikatan su saboda ankon ranar dinner na manyan yara ne kusan 30k haka ƴan ankon suka ɗinka shi, ranar kuwa black abaya suka sa su kayi rolling da pitch mayafi sun yi kyau sosai suka saka white apron ɗin su, sun bawa kowa sha’awa yadda suke abun su cikin tsari babu wata hayaniya, Suhaila ce taje table ɗin su Hajiya kulthum zata yi serving ɗin su.Tunda ta fara zuba abincin Hajiya take kallon yadda take abu a nutse babu wata hayaniya tun a lokacin taji hankalin yarinyar ya burge ta gashi kafin ta fara serving ɗin sai da ta gashe su.

 

Farida ce tazo gurin Suhaila zata yi mata magana, da yake har da ita aka nemo a masu serving cikin son kar mutane su san me zata faɗawa Suhaila yasa tayi mata magana da larabci.

Tace”Ya Suhaila biddi haki minnek(ya Suhaila ina son magana da ke).

Kallon ta Suhaila tayi tace ” shunu? Lesh? Shu sar? (mene? Me yasa? Me ya faru)?

“Hunaka binit hunik hiya biddat ta’amil mashakil” (akwai wata yarinya a can tana so ta kawo mana mastsala) “.

” Wa lesh? (me yasa) ta faɗa tana kallon gurin serving ɗin).

Ganin jama’a sun ɗan taru a gurin yasa tayi sauri ƙarasa haɗa musu ta bar gurin.

Ita kuwa hajiya Kulthum ji tayi Suhailan ta ƙara burge ta “Ke nan she is well educated” ta faɗa cikin zuciyar ta. ɗan dariya tayi tana shan asir(pure juice) ɗin dake hannun ta.

Suhaila tana ƙarasawa ta tsaya tana kallon yarinyar da bata fi sa’ar Farida ba, idan ma zata girmi faridan be fi da shekara ɗaya ba tace”Lafiya me ya faru kuma?”

“Ina da baƙi ne shine nazo na karɓa musu abinci”.Ta faɗa a taƙaice.

“Kiyi haƙuri ko a ina suke za a kai musu bama bada abinci sai dai mu kai musu, kuma sai rabo yazo kan su, ba kya ganin ma rabon yayi nisa, saura kaɗan a gama bada abincin fa”.

“Ba ciki suke ba suna waje” ta faɗa tana wani yatsuna fuska.

“Bari na haɗa ki da wata sai ta kai musu, is that okay?”

Suhailan ta faɗa tana juyawa don fara zuba mata abincin, ɗan juyowa tayi tace”Su nawa ne?.

Zuba kawai ta faɗa tana wani yastuna fuska.

Sai da Suhaila ta gama zubawa ta juya tana bawa ɗaya daga yaran da suke tare tace” raka ta please”.

Saurin karɓar abincin *ZAINAB* tayi tana juyewa suhaila dukkan shi a jikin ta. Inculding juice, fried rice, pepper soup, shawarma, snacks, short cake and other stuffs.

Ƙamewa Suhaila tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa nan da nan kuma ƙarar kwanukan yasa hall ɗin yayi tsit dama cool music aka saka nan fa mutane suka fara kallon su, a dai lokacin kuma Jibril ya shigo cikin hall ɗin.

Cikin tsiwa da masifa Zainab tace”Kece matsiyaciya, server kawai wadda tazo cin arziƙi, nafi ƙarfin ki wulaƙantani akan wani banzan abinci wallahi shasha kawai ƴar gidan talakawa to ga tsiyar ku nan dangin matsiyat….

 

Bata ƙarasa faɗan abunda zata faɗa ba taji an wanke ta da mari, kafin ta ga wanda ya mare ta ta ƙara jin saukar wani marin.

Suhaila ce tayi saurin ɗagowa don ganin wanda ya mare ta nan suka yi ido huɗu da farida dake ta huci.

“Banza mahaukaciya kece ƴar gidan talakawa wallahi, kuma ke abinci ya dama idan da be dame ki ba, da baki zo kina making issues ba, haiwana mugaffala( dabba mara hankali).

Tana gama faɗa taja hannun Suhaila suka bar cikin gurin, sai da suka zo bakin ƙofa sannan Jibril ya samu damar ganin fuskar ta kafin yayi magana har Farida ta jata sun fice a gurin ga kuma mutane, cikin ɗaga murya yace”SUHAILA!!!!

Ɗan juyowa tayi don ganin fuskar shi don tayi mamakin wanda yasan sunan ta gurin kuma namiji, amma sai dai bata ganshi ba, kuma suna fita Farida ta tsare musu napep sai gida.

********

*_Yanzu muka fara wasan_*

_*Asslama alaikum, faɗam Ahmad*_✍????
[6/23, 2:32 PM] Ya Umar: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Page3️⃣0️⃣to3️⃣1️⃣*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button