ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

*Addu’ar Da Ake Yi ga Mamaci a Cikin Sallar Jana’iza.*
اَللَّهُمِّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدْ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا نَقّيْتَ الثَّوْبُ اْلأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَس، وَأَبْدِلْهُ دَاراً خَيْراً مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلاً خَيْراً مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجًا خَيْراً مِنْ زَوْجِهِ، وَأَدْخِلْهُ الْجَنَّةَ، وَأَعِذْهُ مِنْ عَذابِ القَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ.
Allahummagh-fir lahu warhamh, wa’afihi, wa’fu ‘anh, wa-akrim nuzulah, wawassi’ mudkhalah, waghsilhu bilma-i waththalji walbarad, wanakkihi minal-khataya kama naqqaytath-thawbal-abyada minad-danas, wa-abdilhu daran khayran min darih, wa-ahlan khayran min ahlih wazawjan khayran min zawjih, wa-adkhilhul-jannah, wa-a’izhu min ‘azabil-kabr, wa’azabin-nar.
Ya Allah! Ka yi masa gafara, Ka ji kansa, Ka amintar das hi daga bala’i, ka yi masa rangwame, kuma Ka girmama lafiyarsa, ka yalwata mashigarsa (kabarinsa), kuma Ka wanke shi da ruwa da kankara da ruwan raba, Ka tsaftace shi daga laifuffuka kamar lyadda Kake tsaftace farar tufa daga dauda, kuma Ka musanya masa gidan da yafi gidansa alheri, da mutanen gida da suka fi mutanen gidansa alheri, da mata da ta fi matarsa alheri, kuma Ka shigar da shi Aljanna, ka tsirar da shi daga azabar kabari da azabar wuta.
اَللَّهُمِّ اغْفِرْ لِحَيِّنَا وَمَيِّتِنَا وَشَاهِدِنَا، وَغَائِبِنَا، وَصَغِيرِنَا وَكَبِيرِنَا، وَذَكَرِنَا وَأُنْثَانَا. اَللَّهُمِّ مَنْ أَحْيَيْتَهُ مِنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى اْلإِسْلاَمِ، وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَّا فَتَوَفَّهُ عَلَى اْلإِيمَانِ، اَللَّهُمِّ لاَ تَحْرِمْنَا أَجْرَهُ، وَلاَ تُضِلَّنَا بَعْدَهُ.
Allahummagh-fir lihayyina wamayyitina washahidina, wagha-ibina, wasagheerina wakabeerina, wathakarina wa-onthana. Allahumma man ahyaytahu minna fa-ahyihi ‘alal-islam, waman tawaffaytahu minna fatawaffahu ‘alal-eeman, allahumma la tahrimna ajrah, wala tudillana ba’dah.
Ya Allah! Ka gafarta wa rayayyunmu da matattaunmu, da wadanda suke halarce tare da mu da wadanda ba sa nan da yaranmu da manyanmu, da mazajenmu da matayenmu, ya Allah! Wanda ka rayar das hi daga cikinmu, to Ka rayar da shi a cikin Musulunci, wanda kuma ka dauki ransa, to Ka dauki ransa a kan imani. Ya Allah! Kada ka haramta mana ladan (hakurin rashinsa), kada kuma ka batar damu bayansa.
اَللَّهُمّ إِنَّ فُلاَنَ بْنَ فُلانٍ فِي ذِمَّتِكَ، وَحَبْلِ جِوَارِكَ، فَقِهِ مِنْ فِتْنَةِ الْقَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ، وَأَنْتَ أَهْلُ الْوَفَاءِ وَالْحَقِّ، فَاغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ.
Allahumma inna (fulanin) fee zimmatik, wahabli jiwarik, faqihi min fitnatil-kabr wa’azabin-nar, wa-anta ahlul-wafa’, walhak, faghfir lahu warhamh, innaka antal-ghafoorur-raheem.
Ya Allah! Hakika wane dan wane yana cikin alkawarinka (na kiyayewa) da amanarka; don haka Ka tserar da shi daga fitinar kabari da azabar wuta. Kai ne ma’abocin cika alkawari da gaskiya; Ka gafarta masa, Ka ji kansa. Hakika Kai, Kai ne Mai yawan gafara, mai yawan jin kai.
اَللَّهُمِّ عَبْدُكَ وَابْنُ أَمَتِكَ، اِحْتَاجَ إِلَى رَحْمَتِكَ، وَأَنْتَ غَنِيٌّ عَنْ عَذَابِهِ، إِنْ كَانَ مُحْسِناً فَزِدْ فِي حَسَنَاتِهِ، وَإِنْ كَانَ مُسِيئاً فَتَجَاوَزْ عَنْهُ.
Allahumma ‘abduka wabnu amatik, ihtaja ila rahmatik, wa-anta ghaniyyun ‘an ‘azabih, in kana muhsinan fazid fee hasanatih, wa-in kana museean fatajawaz ‘anh.
Ya Allah! Bawanka kuma dan baiwarka ya bukatu ga rahamarka, kuma mawadaci ne ga barin azabarsa, idan mai kyautata aiki ne, Ka yi kari a cikin kyawawan ayyukansa, idan kuma mai mummunan aiki ne, Ka yafe masa.
*_EMBER 2_*????
Gida suka wuce direct ko gidan Aunty khadijan basu koma ba.
Shi kuwa Jibril da ya koma cikin hall direct gurin Zainab ya nufa yana zuwa ya riƙo mata hannu ya fito da ita daga cikin hall ɗin, Kausar ce ta biyo bayan su saboda itama bata ji daɗin abunda tayiwa Suhailan ba.
Cikin ɓacin rai ya fara zazzaga mata bala’i”Wai ke me yasa Zainab baki da hankali ne, baki da kamun kai, daga zuwa gurin biki da ke kin zo zaki ɓata musu biki, akan wani dalili? me tayi miki?”.
Ɗan shiru Zainab tayi tana turo baki gaba,sai da Jibril ya daka mata tsawa sannan tace” Ya Jibril daga nace a bani abinci shine za a tsaya ana mun bincike har da wani a raka ni”.
Ɗan kallon ta yayi yana cize baki cin uzurin nata be kai a ɗauka ba.
Ji yayi zuciyar shi tana wani tafasa, “Get lost” ya faɗa yana juya mata baya idan ba haka ba sai ya mata bugun da sai tayi sati tana jinya.
Kausar na ƙarasowa ita kuma Zainab tana juyowa, har ta zo zata wuce Kausar tayi saurin riƙe mata hannu, ɗan kallon Zainab ɗin tayi tana wani haɗe rai, har ta buɗe baki zata yi magana Kausar ta sa yatsa biyu ta mari bakin nata, nuna ta tayi da hannu tace”Wallahi, wallahi kika ƙara janyo mana magana sai kin koma abuja Allah kuwa, wai sai yaushe zaki kama kanki ne Zainab? kina da hankali kuwa mutane ana ganin mutunci su haka
Kawai zaki zo ki dizgata a cikin mutane”.
Ɗan shafa bakin ta Zainab tayi tana sakin murmushin da yafi kuka ciwo, dafa kafaɗar Kausar tayi tace”Uhmmm idan banda ke abun Son ya Ahmad ce ko, da wallahi wallahi rashin mutuncin da zan miki ba kaɗan bane kuma kema kin san hali na, bana son ya Ahmad yayi fushi da ni amma wallahi da sai na nuna miki shekarunki na banza ne dumin kuwa ajiye su zanyi a gefe na tata miki rashin mutunci, kuma duk tsanar da zaki mun sai na auri yayan ki”.
Ta ƙarashe maganr tana karkaɗe jikin ta sannan ta juya zata wuce zuwa cikin hall ɗin.
Saurin ƙara riƙo hannun ta Kausar tayi ai kuwa tana juyowa ta ɗauke ta da mari.
Nuna ta da yatsa Kausar tayi tace”Wallahi ƙaryar ki, kema kin san yaya na yafi ƙarfin ki nan gani nan bari, kuma koda mata za su ƙare a duniya kema kin san bazai taɓa auren ki ba, ke wallahi ya Ahmad da ya aure ki gwara ya auri mahaukaciya yayi jinyar ta idan baki sani ba to ki sani yau, sha-sha kawai mara kamun kai”. Tana gama maganar ta ta saki hannun Zainab ɗin tana barin gurin gaba ɗaya.
Waje ta ɗan fita ta samu wani dakali ta zauna tana kallon yadda motoci suke wucewa, hawaye ne ya taro a idon ta, saurin goge su tayi tun kafin su kai ga sakkowa, wani abu ne taji ya tsaya mata a maƙogaro gashi yaƙi wucewa wani tuƙuƙin baƙin ciki ne yake ƙara taso mata, ta rasa yadda zata yi, me zata yi ya Ahmad ɗin ta ya dawo gida? me zata ce mai? ba wanda yake sa ta farin ciki a duk gidan su kamar shi, gashi yanzu fafur ta dena ganin shi sai tayi da gaske take iya sashi a idon ta.
Ƴar jakar da take hannun ta ta buɗe ta ɗakko wayar ta.
Wata no. Naga tayi searching, big bro na gani a jikin screen ɗin wayar, bata wani ɓata lokaci ba ta danna kiran nashi, ai kuwa be daɗe ba ya ɗauka, cikin zazzaƙar muryar shi yace”Lil sis how are you doing, ya Nigeria?” ya faɗa cikin hausar shi da ta fara canzawa saboda yadda ya daɗe be zo nigeria ba,kuma bashi da kowa da zai mai hausa a inda yake sai dai idan sunyi waya da Hajiyan su ko kuma ita Kausar ɗin.
Cikin muryar kuka tace”Fine, am fine ya Ahmad, ya aiki?”
Ɗan shiru yayi yana karantar yanayin nata” ajiye biron da yake hannun shi yayi haɗe da rufe file ɗin da suke gaban shi yace”Gaya mun me ya faru? Waye ya taɓa mun ke ummm?