HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Shiru tayi bata amsa mishi ba sai da aka ɗau seconds sannan tace”Zainab ce, but let not talk about her. 6month to me birthday”. Ta faɗa tana jira taji me zai ce.

“Okay, now ya kike so ayi? kin san dai bazan zo ba ko, kuma kinga last ma Jibril be kawo ki ba ina ji Abba ne yace kar ya kawo ki guri na, kuma kin san abunda zai faru idan nazo gida”.

“Am leaving home too ya Ahmad”.

Dariya yayi daga cen ɓangaren yace”Ohhh Kausar rigima, yanzu dai kiyi haƙuri kinji ko”.

“Am serious ya Ahmad, wallahi am leaving home too indai har baka zo birthday ɗin ba wallahi”.

Jin ta rantse yasa ya zama serious”Waii wait Kausar, naji zan zo but kiyiwa baban ki magana, kar na zo ya wulaƙan tani”.

Ɗan murmushi tayi tace”I will talk to him, har naji duk wani ɓacin rai ya tafi, kana ina yanzu? “.

” Washington, wani aiki ne ya kai mu can amma zuwa jibi zan koma new yolk, next case ɗin na kuma a hilton ne”.

Ɗan tashi tayi tsaye tana buga wani uban tsalle”Da gaske ya Ahmad! A hilton?”.

Ɗan keɓe baki yayi yace” Yesss meye na murna haka?”

” Zan dinga ganin ka kullum mana”.

Haka dai suka cigaba da hirar su har ta gaji ta kashe wayar ta koma ciki wajen bikin.

Ita kuwa Zainab ji tayi kamar ta kashe kan ta saboda maganganun da Kausar ta faɗa mata.

Jibril kuwa gida ya nufa direct da ya bar wajen bikin, yana zuwa ya shige boys quarters, cillar da keys ɗin hannun shi yayi yana zame necktie ɗin dake wuyan shi, bango ya kaiwa naushi yana jin zuciyar shi kamar zata faɗo ƙasa.

Cikin damuwa ya fara faɗin”Why SUHAILA nace ki kira ni if you are read.

Ɗan shiru yayi haɗe da lumshe idon shi yace”Ahhh Kausar kin cuce ni, na san ma ta kira bata samu no. na ba, yanzu a ina zan ƙara ganin ta?

********

Suna shiga gida Ammi ta gansu kamar an jefo su kallon SUHAILA tayi da duk jikin ta ya ɓaci da abinci ga kuma hawaye tana zubarwa”Me ya faru? ta faɗa cikin damuwa.

SUHAILA kuwa banɗaki ta shige, don wanke jikin ta, ita kuwa haijaya Farida guri ta samu ta zauna tana korawa Ammi jawabi.

Tsaki Ammin tayi tace”Ita yarinya ce da baza ta iya ɗaukan mataki ba har sai ke ƙanwar bayan ta kin shigar mata, ita ta sani ku gama ku koma wallahi, tunda baku faɗa mata zaku taho ba ai ba daɗi”.

Kallon agogo Farida tayi tace”Ammi kalli fa 10:30 fa, ki bari da safe mun koma kawai.

Ɗan shiru tayi tana tunanin eh be kamata ace su fita yanzu ba, “Da wuri ku tashi ku shirya ta faɗa tana shigewa ɗaki”.

Ita kuwa SUHAILA bayan ta fita daga wanka sallah tayi ta kwanta. Farida ce ta shigo ɗakin ta dinga masifa tana bala’i.

Lumshe idon ta SUHAILA tayi tace”Ya wuce, bana son maimaita maganar, kanta tayi wa bani ba”.

Haka nan bacci ya ɗauke ta, washe gari da safe suka koma gidan, tunda ta shiga mutane suke bata haƙuri ita kuwa ko a jikin ta sai cewa take babu komai.

Bayan an ɗaura aure hajiya Kulthum ta sa aka kira mata Suhailan.
Ita kuwa suhaila tayi mamaki jin ance ana kiran ta.

Wani palo ne me shegen kyau aka kai Suhailan tana shiga ta hango ta ita kaɗai a palon kai baka ce gidan da ake biki bane.

Ƙarasawa tayi ta nemi guri ta zauna tana gaishe ta. Cikin sakin fuska ta amsa mata, kusa da ita hajiya ta kira ta, tashi tayi daga kujerar da take ta koma kusa da hajiyan ta zauna, ɗan riƙo hannun ta tayi ta sa shi a cikin nata, saurin ɗagowa SUHAILA tayi tana kallon ta da mamaki, a hankali hajiya Kulthum ta fara magana “Kiyi haƙuri akan abunda ya faru jiya Kausar duk ta faɗa mun yadda abun ya faru, ki mata uzuri, muna zargin kamar bata da lafiya ne”.

Murmushi Suhailan tayi tace”Haba dai saboda haka ne kika sa a kira ni har na”.

“Eh mana”.

“Ba komai wallahi ya riga da ya wuce a guri na tun jiyan ma”.

“Allah ya miki albarka to”.

Amin ta amsa mata, sannan ta nemi izinin tafiya.

Bayan ankai amarya ɗakin ta ƴan biki suka fara watsewa inda su SUHAILA suka fara haɗa kayan su suma don komawa gida tunda komai ya kammala.

Suna zaune suna hira Kausar tace”Ƙawata don Allah kar ki tafi, yanzu idan kika tafi wa zai zama abokin tsokana ta”.

Dariya SUHAILA tayi tace”Haba kar ki damu mana ana tare ga waya sai mu dinga gaisawa.

Fitowa suka yi Kausar ta raka ta har gidan Aunty khadija, sallama suka yi suka karɓi no. juna.

Mota aka fito da ita don kai su gida.

Jirbril ne tsaye a jikin balcony yana kallon waje hannun shi guda ɗaya cikin wandon shi ɗayan kuma riƙe yake da lemo yana sha, a dai dai lokacin Farida da SUHAILA suka fito daga cikin gidan, sai dai kash fuskar SUHAILA a rufe take da niqabi, kamar ance ta ɗaga kanta nan suka yi two eyes da shi, ji tayi gaban ta yayi mummunar faɗuwa cikin sauri ta shige mota tana sauke numfashi, shima ana shi ɓangaren ji yayi gaban shi ya faɗi da suka haɗa ido, sai kuma ya basar.

SUHAILA ce ta faɗo mai a rai nan ya fara tunanin anya kuwa ita ya gani jiya wanda take kaduna me zai kawi ta Kano.

Numfashi ya sauke yace”Ahhh! anything is possible”.

******

Bayan sati ɗaya su Kausar suka fara shirye shiryen komawa abuja daga can kuma za su wuce hilton.

Ita dai hajiya ta kamu da son SUHAILA har take tunanin haɗa ta da ɗan ta, don ta ga yarinyar akwai hankali ga haƙuri zata iya zama da shi.

Ummi ta tambaya ko wacece SUHAILA nan take bata labarin abunda ta sani.

Ummi ce ta raka ta gurin Aunty khadija don jin ƙarin bayani,ai kuwa aunty khadija sai da ta faɗa musu komai har raping Suhaila da akayi zuwa auren ta da Habib.

Hajiya da ummi kuwa sunji tausayin ta soaai, ɗan shiru hajiya tayi can ta nisa tace”Duk da haka ina son ta kuma shima zai so ta dumin abunda nake so shi yake so kuma babu namijin da zai ga Suhaila yace bata mai ba, sai dai idan dama son zuciya ya saka”.

“Haka ne” Aunty ta faɗa tana jin daɗi mara misaltuwa.

“Amma fa ina so ki bani ita a matsayin house cook ɗina tunda tana da certificate a ɓangaren, so nake su haɗu har ya fara son ta saboda bana so na mishi dole ko na mata dole”.

Tofa Hajiya dai kawai ta faɗi wannan batu ne don a bata Suhaila don bata san ta yadda za su saba ba.

Ɗan shiru Aunty tayi tace”Wai daga nan har london? “.

“Ba fa me aiki zan maida ta ba kawai dai na faɗa ne don kar a san me yake faruwa”.

“Na gane, amma ni yanzu bazan yanke hukunci ba sai sai na samu iyayen ta”.

“To babu matsala don Allah ki mana ƙoƙarin samun ta”.

“In sha Allah”.

Washegari da wuri Aunty khadija taje wa da Ammi zancen, wayyo Ammi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha musamman ma da taji an ambaci london.

“Kin yarda dasu dai ko?” Ammi ta faɗa tana kallon Aunty khadija.

“Sosai ma kuwa, wallahi indai da hali ta bisu, gidan arziƙi”.

“To ki sa a ranki Suhaila ta gama zuwa London”.

“Allah ko” shiyasa nake son ki bakya sanya wallahi”.

“To wa zai tsaya sanya a wannan lokacin ga opportunity yazo”.

Hajiya Khadija na komawa gida ta sanar da su, ai kuwa sunyi farinciki sosai da sosai nan suka fara shirye shireye akan jibi za su wuce.

Hajiya kuwa tunda ta samu Abbu da maganar yace bazai yiwu ba.

Ko maganar ma bata ƙara mai ba tace ai zuwa Suhaila kamar taje tunda ba shi ya haife ta ba.

Koda ta faɗawa Suhaila daga ita har Farida ɗaukan abun suka yi kamar wasa.

Ana gobe za su wuce abuja Ammi ta shigo ɗakin nasu tace”Ha’a ya naga baki fara haɗa kaya ba tafiya za kiyi me tsaho, ki tashi maza ki haɗa kayan ki”.

Ɗan kallon ta tayi tace”Ammi wai da gaske kike ko wasa? ”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button