ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

” Kinga alamar wasa nake ne?”
Ɗan shiru Suhaila tayi tace” Gaskiya Ammi bazan je ba kiyi haƙuri na saɓa miki wannan karan”.
“Baza ki je ba kika ce, to wallahi inda baki je sai na tsine miki albarka na ɗaga miki nono”.
Saurin ɗagowa Suhaila tayi tana kallon Ammin tace”Ammi as a cook fa? kin san wahalar da ake sha kuwa a irin ƙasashen nan, da ilimi na da komai na tafi yawan dafa abinci gidan wasu, gaskiya bazan je ba Allah ma ya sani”.
“In tsine miki kenan baki jin tsoro ko”.
Cikin ɓacin rai Suhaila tace”Eh Ammi! Ki tsine mun ban damu ba, dama kin tsane ni, ba kya son ganin farin ciki na, ba kya son gani na cikin farin ciki, kin ƙuntata mun rayuwa, kin haka ni sakat, Ammi me nayi miki? Me nayi ne ni? Me yasa baza ki tura Farida ba sai ni? me yasa baza ki samu wani a cikin dangin ki ba sai ni? Me yasa ni? Na fita daban a cikin ƴaƴan ki, lokacin da akayi raping ɗina har cewa kika yi gwara da Allah yasa nice, baki damu da ni ba, baki kula da ni a lokacin ba, sai Abba da ya Fatima ne suka kula da ni,Ammi baki san komai nawa ba, duk wani soyyaya da uwa take bawa ɗa baki bani ba, a iya sani na tunda nake baki taɓa mun tsarkin kashi ba sai dai Abba yayi mun, Duk kashin da zan yi sai ya dawo yake cire mun, me nayi Ammi? ko ba ke kika haife ni bane? a tsintoni aka yi? Ammi a ina kika samo ni? nasan da Abba na nake kama ko kuma samo ni yayi a gurin wata can ya kawo miki ni?”.
Tass tass tass Ammi ta wanke Suhaila da mari ta ɗaga hanu zata ƙara na huɗun Suhaila tayi saurin riƙe hannun ta tace” ki kashe ni kawai ban damu ba”ta faɗa tana fita daga ɗakin, kitchen ta shiga ta ɗakko wuƙa, ai da gudu Farida da biyo bayan ta, suna shigowa ɗakin tace”Ya Suhaila meye haka?”
“Ba ruwanki, idan kuma kika shiga wallahi zaki ɓatawa kanki rai sosai”.
Hannun Ammi ta kama ta saka mata wuƙar tace”Kashe ni! Ki kashe ni na huta kawai, idan ba a waje Abba ya samo ni ba, me nayi da kike mun wai’nnan abubuwan? “.
Shaƙe Suhaila tayi a jikin walldrop ta cillar da wuƙar hannun ta idon ta duk ya ciko da hawaye tuni ta fara kuka ciki kuka tace”Ƙarya kike wallahi duk abun shi be taɓa bin mata ba be taɓa ba, kuma bari kiji ko shi da kike gani be kaini son ki ba, Suhaila duk cikin ku nafi jin ki akan kowa saboda abunda na miki, nafi son ki akan kowa saboda da ke nake amfani wajen ƙuntatawa mahaifin ki, baya neman mata, amma tunda kince dole sai kin san abunda muka ɓoye shekaru ishirin da shida da suka wuce, to bari kiji shi mashayin giya ne kafin na haife ki! ”
Ta ƙarashe maganar tana sakin wuyan Suhailan haɗe fasa kuka me cin rai.
Zubewa Suhailan tayi a ƙasa tana jin zuciyar ta na mata nauyi ga kuma mugun sarawa da kanta yayi……….
********
_*Tofa ga abubuwa suna ta faruwa, ko ya abun yake oho, me ya haɗa Suhaila da shan giyar da Abbu yayi a baya da har Ammi take ɓata mata saboda haka? Sai a next page dai za muji*_
*_Ma’asalma, Faɗma Ahmad_*
[6/25, 8:40 PM] Ya Umar: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page 3️⃣2️⃣to3️⃣3️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.
*Addu’a Yayin Shigar Da Mamaci Kabari*
بِسْمِ اللهِ وَعَلَى سُنَّةِ رَسُولِ اللهِ.
Bismil-lahi wa’ala sunnati rasoolil-lah.
Da sunan Allah, kuma a kan sunnar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
_*The trip*_
Ɗan ɗago kai SUHAILA tayi fuskar ta duk a jiƙe da hawaye tace”Ammi kinji abunda bakin ki ya faɗa kuwa?”
” Ƙwarai da gaske naji”.
Farida ce ta fashe da kuka jin abunda yake shirin faruwa a gidan nasu.
Cigaba da magana Ammi tayi tana jin zuciyar ta kamar zata faɗo ƙasa tsabar tsananin baƙin ciki.
“Auren soyyaya mukayi da Abban ku kamar zamu cinye junan mu, kuma lokacin da ya aure ni bashi da komai hasali ma a gidan haya muka fara zama,bayan wasu ƴan watanni da yin auren mu ya samu aiki a wani company na sarrafa atamfofi, daga nan kuma komai namu ya canza muka fara samun rayuwa me daɗin gaske har Allah yasa na samu cikin Fatima, bayan na haifi Fatima da shekara ɗaya baban ku ya haɗa kai da mutanen garin su akan za su yi noma, abunda aka samu sai a raba ribar, to a lokacin bashi da kuɗin da zai yi nomar hakan ne yasa yaci bashi a company akan idan an gama zai mayar musu da kuɗin su, kullum cikin addu’a yake Allah yasa abunda aka shuka yayi albarka, haka dai aka cigaba da tafiya har Allah ya kawo lokacin da za’a cire amfanin gona, domin kuwa noma tayi kyau sosai da sosai, don a 1 million ɗin da suka zuba sai da aka samu ribar kusan dubu ɗari tara akai, sai dai fa a lokacin ne mutanen ƙauyen nasu suka mai halin su, domin kuwa siyar da amfanin gonar suka yi ba tare da ya sani ba, in taƙaice muku, dubu ɗari biyu ya samu a cikin kuɗin gashi kuma lokacin da yace zai biya kuɗin ya ƙarato. Tun daga wannan lokacin Abban ku ya shiga cikin damuwa ga albashin na shi 90k ne ba wani yawa ne da su ba, ni dai ban san yadda aka yi ba sai ji nayi an kore shi daga aiki a company, suka kuma bi duk wata kadara tashi suka siyar suka karɓi kuɗin su, kuma duk da haka akwai ragowar kuɗin kusan dubu ɗari uku, nice na ɗauki ɗan kunne na na siyar da shi dubu ɗari aka ƙara basu wani abun mu kuma muka koma gidan jiya, gidan haya, talauci yazo yafi na da ga barazana da suke masa akan idan be ƙarasa biya ba sai sun sa an kaishi prison, tun daga wannan lokacin na dena gane kanshi ya dawo gida a buge tun ban gane ba har nazo na gane, kuma na rasa wa ya koya mai wannan ɗabi’un, kai wani zubin ma idan ya dawo haka zai zo yayi mun aman giya a jiki na babu yadda na iya da warin ta da ƙazan ta haka nake haƙuri na kwashe, kai har takai ga idan zai karɓi haƙin shi sai yayi mun dole wani zubin ma sai ya lakaɗa mun duka tukunna, haka na jure nayi haƙuri ban taɓa kai ƙarar shi ba har Allah yasa na samu cikin SUHAILA, a wannan cikin kuwa babu irin azabar da ban sha ba, duka ne zagi ne babu wanda be mun ba, shi a ganin shi muna cikin wannan yanayin zan kama ɗaukan ciki, yayi2 da ni in zubar da cikin nace bazan zubar ba, ya dake ni, ya daki cikin amma ciki sam yaƙi zubewa, a cikin matan da muka zauna da su kullum cikin yi mun habaici suke da kiran miji na mashayin giya”.
Numfashi ta sauke tana daɗa goge hawayen da suke zuba mata ta cigaba da cewa”Sai daga baya Inna tasan abunda yake faruwa, tun daga wannan lokacin ta fara mai faɗa tana takura mai haɗe da sawa ayi mai magani a cen garin nasu ko Allah zai sa ya dawo cikin nutsuwar shi.
“Haka kuwa akayi tun daga wannan lokacin aka fara samun sauƙi ya rage dawowa gida a buge sannan ya dena duka na, a wannan lokacin ne kuma na haɗu da Aunty khadija tun bata gane matsala ta ba har tazo ta fahimta, ita ta bani shawarar na dena nuna mai ina tsoron shi, tun daga nan nima na fetsare da ya fara duka na zan ɗau abu ince idan ya ƙara sai na kwaɗa mai, ai kuwa nan na samu canji ya kuma kiyayi kan shi, bayan na haihu ya sa miki sunan mahaifiyar shi,SAKINA, ni kuma nace wallahi sai na goge sunan duk don na ɓata mishi, ai kuwa nan na samo suna me daɗi na sa miki SUHAILA shikenan ya kama bakin mutane har mantawa ake da sunan ki Sakina kuma kema haka kika taso”.