ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Tun daga wannan lokacin na fara muzguna mishi a kan ki ganin yadda yake bala’in son ki, baya so ki matsa ko nan da can, bayan kinyi wata uku da haihuwa Allah yasa aka samar mai teaching, albashin shi na wata ukun farko gaba ɗaya ya ɗauka ya biya bashin da ake bin shi kuma duk da haka saura 100k ya gama biya, a haka dai yayi covering bashin shi ya siyi fili har ya fara ginawa,ke kuwa ba ruwa na dake, bana kula dake hakan ne yasa ya rage shan giyar shi fiye da na da, duk don ya kula da ke, shi yake miki wanka ya baki abinci ya miki wanki, shine komai naki tsakani na dake kawai nono, kuma shima ina baki ne don kar kafin ya dawo ya baki abincin ki kin jigata, har kika yi wayo, tun da yaga kin shekara biyu kin fara wayo sosai ya dena shan giya kwatakwata, ya dawo Muhammad ɗin shi na da, ya nutsu ya dawo baku tarbiya sosai da sosai yasa ku a makarantar arabic me kyau, Fatima kuwa tun kuna yara take mugun sonki bata son ganin abunda zai sa ki kuka, ko a makaranta duk wanda ya dake ki sai ta rama miki, kullum sai an kawo ƙarar ta kan tana dukan yara”.
Sauke numfashi shi tayi me nauyin gaske tace”Kinji dalilin da yasa haka ta faru da ke,ba wai don bana son ki ba”.
Ciki kuka SUHAILA tace”Ammi duk da haka wannan ba uzurin da zai sa ki mun duk abunda kika mun ba, Ammi kin cutar da ni, ki bani wahala kin ƙyamace ni, kin nuna mun banbanci tsakanina da ƴan uwa na”.
Wani kukan ta ƙara fashewa da shi, ga kanta da take jin kamar zai faɗo ƙasa tsabar sarawar da yake mata.
Ɗan miƙewa tayi tanajin jiri yana ɗan ɗibar ta, kallon agogo tayi taga 8:12pm. Hijabin ta ta zura haɗe da ɗaukan wayar ta da kuma purse, kallon Farida tayi tace”Ki haɗa mun duk wani abu da yake cikin drawer ta wadda kika san zai mun amfani”.
Farida ce tace”Ya Suhaila ina kuma zaki je?”.
” Kar ki damu yanzu zanje na dawo”.
Tana fitowa palo taga Abba a zaune wanda tun lokacin da aka fara abun ya shigo cikin gidan amma tsabar hayaniyar su basu ji shi ba.
Saurin miƙewa yayi yace”Mama na ina kuma zaki je? Ki tsaya muyi magana pls”.
Ɗan kallon shi tayi tana jin wani son shi yana ƙara shiga zuciyar ta, Alhamdullilah ta sanadin ta Abban ta ya zama mutumin kirki.
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tace”Abba gidan Umman Sheka zanje, bazan iya magana da kai ba yanzu “.
Kallon ta yayi da mamaki jin tace gidan Umman sheka gidan da ta ɗibi shekaru bata je ba amma yau ita ce zata je.
Gyaɗa mata kai yayi don baya son takura mata.
Tana fita ta taka a ƙasa zuwa gidan Surayya kasancewar basu da wani nisa sosai amma duk haka akwai ɗan tafiya, yanayin ta ne kawai yasa ta tafi a ƙasan.
Surayya na zaune taji ana buga gidan ta, nan ta je buɗe don ganin waye don kuwa Abban Najwa ya dawo gida, ganin Suhaila yasa tayi saurin wangale ƙufar tana mata iso, tana shiga ta tsaya a tsakar gida.
Kallon juna suka tsaya yi, Surayya na shirin tambayar ta Suhaila tayi saurin rungume ta tana sakin kuka me cin zuciya haɗe da faɗin”Ƴar uwa ki yafe mun, zan tafi na barki, ki kula mun da kanki da kuma Najwa, ki kula da Abban Najwa kinji ko”.
Saurin ɗago ta Surayya tayi tace”Haba mana meye haka ne wai? Me ya faru?”.
Jin ɗan hayaniya yasa Ishaq ya leƙo don ganin abunda yake faruwa, nan ya hango su a tsaye, Suhaila na hango shi tace” Na tafi sai munyi waya”.
Ta bar jikin Surayya tana saurin fita daga gidan, ita kuwa Surayya sai ƙwala mata kira take amma ina bata tsaya sauraron ta ba gashi ɗan kwali ne kawai a kanta, ɗaki ta shiga ta ɗakko hijabi amma ina kafin ta fito har Suhaila ta samu abun hawa, haka ta koma cikin gida hankalin ta duk a tashe, haka Ishaq yayi ta tambayar ta ko me ya faru,”Wallahi ban sani ba Abban Najwa haka ta shigo ta fita”.
Sheka ta nufa direct tana shiga gidan taji tayi karo da mutum, ɗan tsayawa tayi ta kalle shi daga shi sai gajeran wandon ƴan ball a jikin shi sai wata ƴar yaloluwar vest, ɗan kallon shi tayi nan taji gaban ta yayi mummunar faɗuwa, ratsawa tayi zata wuce shi yace”Ha’a ka ga ustazai wa’inda baza su auri ƴan shayeye ba, ya aka yi shi wanda ba ɗan shayeye ba ya sako ki, wallahi da ni kika aura da kina zaune lafiya kuma wata ƙila ma da yanzu na dena, ɗan murmushi yayi yace”Na gama da ke wallahi, yanzu ma kika fara gani”.
Bata ce mai komai ba ta ƙara canza hanya zata wuce yayi saurin fizgo ta yana haɗa jikin shi da nata, rungume ta yayi tsam a jikin shi yana faɗin”Suhaila kenan har yanzu ina son ki, duk sanda na ganki sai naji tsohuwar soyayyar ki ta taso mun. You should congrat me na kai kuɗin aure, kuma wata tsaleliyace wanda tafi ki kyau tace zata auri ɗan shayeye taji ta gani”.
*”JA’AFAR* ka sake ni kana da hankali kuwa!?”
Bugun zuciyar ta ne ya ƙaru wani mugun tsoran shi ya kamata, nan da nan jikin ta fara kirma, ga wani gume da ya haɗar mata lokaci guda.
Cikin kuka tace”Don Allah Ja’afar ka sake ni wallahi inajin tsoran ka, don Allah ka barni naga Umma ina son na huta please”.
Murmushi yayi yana kwantar da kan ta akan kafaɗar shi yace”Nan ma ai zaki iya hutuwa”.
Ƙoƙarin fizge jikin ta tayi amma ya ƙara rungumeta yana matse ta a jikin, a hankali ya fara shafa kanta yana faɗin”Shhhhhhh kiyawa mutane shiru malama”.
Shirun tayi don ta san Ja’afar ya wuce nan, ya wuce inda take tunani, idan zata mutu in ba kwantar da hankalin tayi ba bazai fasa abunda yayi niyya ba.
Sunfi ƙarfin 10 minute a haka har bacci ya fara ɗaukan ta, jin jikin ta ya fara saki yasa ya ɗan jata a hankali zuwa dakalin da ke jikin ƙofar shiga ɗakin shi kuma yana riƙe da ita, tana jin shi sama sama ga tsoron da ke ziyartar ta, amma haka nan tayi kamar bata jin shi don tasan duk abunda ya gadamar yi sai ya yi.
Bayan sun zauna da minute kaɗan bacci ya ɗauke ta, ɗan ɗago ta yayi yana kallon innocent face ɗin ta saurin goge hawayen da suka ciko mai ido yayi yana haɗiye kukan da yake shirin taso mishi.
Ɗaukan ta yayi cakkk ya shiga cikin gida da ita, nan su Bahijja da ke palo suka yi saurin tashi tsaye suna kallon shi, Umma kuwa tana kitchen daga tsakar gida amma tana hango shi ta biyo bayan shi, tana shigowa yana kwatar da ita akan kujera juyowar da zai yi ta ɗauke shi da mari tace”Daga ina kai kuma? a ina ka janyo mun magana yau?”.
Ɗan shafa gurin yayi cikin basarwa da haɗiye damuwar shi yace”Haba Umma na, Suhaila ce fa, tazo kuma tayi bacci shine na kawo ta”.
Ture shi tayi tana duba Suhailan, nan ta juyo ta kalle shi tace”Ai nazaci magana ka janyo mun ne, zaka iya tafiya”.
******
Washegari da safe Suhaila na tashi ta ganta a ɗakin su bahijja nan da nan ta tashi, sai da tayi wanka sannan ta ɗoro alwala tana fitowa tayi sallah, nan take tamabayar su Bahijja ina Umma, kiran Umman aka yi, nan Suhaila ta faɗa mata abunda ya faru tsafff from A to Z.
Umman ce tace”To yanzu ke kin yarda ayi wannan tafiya? “.
” Umma Ammj ko kaini zata yi a siyar da ni wallahi zanje”.
Ɗan shafa kanta Umma tayi tace”Allah ya miki albarka nasan ma baza ta siyar da ke ba, ki cigaba da haƙuri zaki ji daɗin rayuwa, yi nayi bari na bari, ba ruwanki da shiga sabgar da ba taki ba idan kika je garin, kin ji ko, kiyi aikin ki kawai ba ruwanki da kowa, ba runwaki da maza don kin san mazan can ba kamar na nan suke ba”.
“In sha Allah Umma”.
7:00cif ta fito daga gidan, tana fitowa titi ta samu abun hawa nan ya kawo ta ƙofar gidan su, Abbu ta samu a tsakar gida Riƙe da alkur’ani yana karantawa, gaishe shi tayi zata wuce.