HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Saurin tsayar da ita yayi yana ƙarasawa inda take, hannun ta ya riƙo yace”Kiyi haƙuri akan abunda kika ji jiya a kai na, duk abunda ta faɗa haka ne, kuma kinga ai na canza kuma komai ya wuce, amma ita har yanzu ta kasa mantawa, kiyi haƙuri Suhaila saboda ni komai yake faruwa”.

“Aa Abba kar kace haka, haka Allah ya tsara mana, kayi haƙuri ka bata dama as a Mother, ka barni na tafi kawai i will be fine Abbu mana, kuma komai zai wuce mun, indai har sunan maman ka gareni to ina me umartar ka da ka barni na tafi don Allah, ka ga haka wancan karan aka yi da naƙi binta auren nan yazo ya lalace, kayi haƙuri plss Abbu”.

Hawayen da ya zubo mishi yayi saurin gogewa yace”Mama na, na barki Allah ya miki albarka, ya kuma kare mun ke, in sha Allah zaki ga haske a rayuwar ki ko dan biyyayar ki”.

“Abbu ka zauna lafiya da Ammi don Allah kafin na dawo kuyi settling plss Abbu na, ku dawo normal life ɗin ku”.

“In sha Allah”.

Tana shiga palo ta tarar da Ammin, gaishe ta tayi, amma Ammin bata amsa mata ba tace”Kar abunda na faɗa miki jiya yasa kiyi tunanin abubuwa za su canza. Ki shiga ki ƙarasa shiryawa yanzu driver zai ƙaraso”.

Ɗan murmushi tayi tace”Ammi ko abubuwa basu canza ba, it’s a relief nasan ba tsana ta kika yi ba, you just have a reason”.

Tana gama maganar ta shige ɗaki, nan ta ɗauki purple box ɗin ta, ta buɗe kayan ta ta zura shi a ciki, jikin mirrorn su ta kalla, a hankali ta ƙarasa gurin ta cire dream catcher ɗin ta, “Am sorry Jibril can’t make it”. Ta faɗa tana zuge zip ɗin jakarta ta ta baya tazura shi.

Nan ta janyo akwatunan ta zuwa tsakar gida.

Mubarak ne a tsaye fuskar shi har ta kumbura saboda yadda yasha kuka, itama Farida da take tsaye a gifan ta kukan take, tana faɗin”Ya Suhaila yanzu tafiya zaki yi don Allah kar ki tafi ki bar mu don Allah”.

Ɓittttt ɓitttt suka ji horn na tashi alamar har driver ya iso, Abbu ne ya fitar mata da kayan yasa mata su a bayan mota, ita kuma daga cikin gida su Mubarak sun rungume ta suna kuka sosai.

Cikin kuka tace”Ku kula da kan ku, ku kula da Ammi da kuma Abba na, na tafi sai wata rana”.

“A sauka lafiya”. Ammi ta faɗa tana leƙowa ta window “.

Ɗan murmushi tayi tace “Amin”.

Tana fita ta shige cikin mota da gudu don bata son ta ƙara haɗa ido da Abbun ta.

Nan driver yaja mutar suka bar ƙofar gidan, suna cikin tafiya tana kallon Window, abunda ya faru tsakanin ta da Ja’afar ya faɗo mata, kwallar da take kwance a idon ta ce ta zubo mata, cikin zuciyar tace”Allah sarki Ja’afar nayi danasanin kiran ka ɗan shayeye a rayuwa ta, ashe nima Abbu na ya taɓa yi, in Allah ya yarda bazam ƙara kiran wani da ɗan shayeye ba.

 

*********

Tunda suka isa bakin Hajiya yaƙi rufuwa sai godiya take yi, ita kuwa Kausar kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha jin Suhaila ce sabuwar cook ɗin su, shi kuwa goga Jibril ya wuce kaduna don ba tare za su koma baa can london ɗin da shi ba.

Zainab kuwa ji tayi kamar zata kashe Suhaila don ta tsane ta, gashi wannan karan da ita za a tafi hutu can london dama ta saba zuwa.

Basu daɗe ba suka ɗau hanyar Abuja, bayan sati ɗaya kuma, suka fara shirye2 tafiya London inda Suhaila ta fara sabawa da Hajiya ita da Kausar kuwa ba a magana, Zainab kuwa kamar ta kashe ta haka take ji.

Yau kuma jirgin su ya ɗaga zuwa london, hilton….

********

*_To! fans mu haɗu a london don jin yadda zata kaya_*

_*Asalama alaikum*_ ????

_*Faɗma Ahmad*_✍????

 

[6/28, 11:25 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page3️⃣4️⃣to3️⃣5️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

*_Mom Sadiq wannan page ɗin naki ne kiyi yadda kike so da shi, ki mai gunduwa2 ki bawa duk wanda ranki yake so, na gode da kulawa_*…. ????

*Addu’a Yayin da Mutum ya juya a cikin kwanciyar Barci.*

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ الوَاحِدُ القَهَّارُ، رَبُّ السَّمَوَاتِ وَاْلأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا، الْعَزِيزُ الْغَفَّارُ.
La ilaha illal-lahul-wahidul-qahhar, rabbus-samawati wama baynahuma, al’azeezul-ghaffar”.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, makadaici, marinjaye, ubangijin sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu, mabuwayi, mai yawan gafara.

 

_*LONDON ENGLAND*_

Jirgin su na sauka a London wasu manya-manyan motoci guda biyu suka zo ɗaukar su, irin motocin nan da ake ce musu masu numfashi.

Suhaila kuwa tunda tasa ƙafar ta a garin taji wata muguwar ni’ima na ratsa ta, a ɓangare guda kuma gaban ta sai faɗuwa yake yi.

Mota ɗaya suka shiga ita da Kausar sai Zainab da ta hakimce a gaba, ita kuma Hajiya ta shiga ɗayar motar ita kaɗai.

Ɗan zuge glass Suhaila tayi tana kallon garin, ga wata iska mai mugun daɗi haɗe da sanyi-sanyi da ke ratsa mata jiki, ɗan lumshi ido tayi tana ƙara shaƙar iskar da ke kaɗawa, wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta, tana jin daɗi mara misaltuwa, wai yau ita ce a London, inda ko a mafarki bata taɓa tsammanin zata je ba.

Tafiyar kusan 30 minute suka yi kafin su iso wani ƙatoton mansion wanda tun daga waje kai ka san zai haɗu iya haɗuwa.

Zuge masu gate aka yi nan da nan motocin suka shige cikin gidan haɗe da fakawa a parking space wanda a ƙalla zai ci kusan motoci goma.

A hankali ta buɗe murfin motar ta fita bayan su Kausar duk sun fita.

Kausar ce tayi ɗan miƙa haɗe da buga tsalle tace; “Finally na dawo gida, zan ga ya Ahmad ɗina!”.

 

Zainab ce tayi saurin juyowa ta kalle ta tace; “Haba da gaske ya Ahmad zai zo!?”.

Harara Kausar ta ɓalla mata tace; “To uwar zaƙin baki, ba zuwa zai yi ba, ni zanje na ganshi kafin ki kaini gaba uwar magana da neman son a sani”.

Ita dai Suhaila tana gefe tana kallon ikon Allah, kausar ce ta kama hannun ta tana murmushi tace; “Muje ko, duk naga kin gaji”.

Murmushin yaƙe Suhaila tayi tana gyaɗa mata kai.

Ɗan juyowa tayi tace; “John can you please bring our luggage?”.

” Sure madam”, ya faɗa yana fara buɗe boot ɗin motar.

Cigaba da tafiya suka yi inda Suhaila take ta kashe ƙwarƙwatar idon ta.

Ƙaton compound ne mai girman gaske wanda ya ƙawato da furanni masu kyaun gaske, gashi sun sha gyara daga gani ana kula da su sosai da sosai, cigaba da tafiya suka yi inda suka shiga wata ƙofa mai kyan gaske, daga gefe kuma ga swimming pool nan amma ta cikin glass take hango shi, daga gani sai an zagaya ta wani gurin ake shiga wajen swimming ɗin.

Wani gini ta hango mai shegen kyau kamar yayi magana ga flowers duk sun zagaye shi, cigaba da tafiya suka yi har sai da suka wuce ginin, bayan sun ɗan ƙara tafiya kaɗan suka shiga wata ƙofa, sai gasu a wani mugun katafaren Palour wanda yaji kayan ƙyalƙyale na duniya. Komai na palon blue-black ne da kuma ash, kai palon ba ƙaramin kyau yayi ba domin kuwa ya haɗu iya haɗuwa, amma wasu abubuwan palon a rufe suke da farin ƙyalle daga gani jin za su dawo ne yasa aka buɗe wasu.

Suhaila kuwa sakin baki tayi tana kallon ikon Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button