ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Upstairs suka nufa yayin da Hajiya Kulthum ta ɗau hanyar nata ɓangaren.
Zainab ce ta saki baki tana kallon ikon Allah ganin Kausar na shirin jan Suhaila har cikin ɗakin ta.
“Dakata”. Zainab ta faɗa.
Jin haka yasa Hajiya tayi saurin tsayawa don tasan Zainab sai tayi making issues a gurin.
“Wannan ba a gurin ma’aikata zata zauna ba naga kina ƙoƙarin shiga da ita ɗakin ki”.
Hajiya ce tace; “Kausar Suhaila zata zauna a kusa da ɗakin ki, ke da Zainab ku zauna tare yadda kuka saba”.
Ɗan kallon Zainab tayi tace; “Ke kuma Suhaila ba kamar normal maids take ba, don haka ban yarda ki wulaƙanta ta ba”.
“Ni gaskiya Tare da Suhaila zan zauna ita Zainab ta koma next room ɗin”.
Ɗan taɓe baki Zainab tayi tace; “Ni wallahi da yafi mun ma”.
Ko kallon inda take Kausar bata ƙara yi ba suka shige ita da Suhaila cikin ɗakin.
Tsayawa ma faɗar kyaun ɗakin Kausar ɓata lokaci ne domin kuwa duk abunda kake buƙata babu wanda baza ka samu ba.
Ita dai Suhaila har yanzu tana jimamin yadda Zainab take tashen rashin kunya, yarinyar da bata kai ta kawo ba.
Kayan da aka rufe Kausar ta ɓuɗe, ai kuwa nan kyaun ɗakin ya daɗa fitowa sosai.
Kallon Suhaila tayi tace; “Feel at home kinji ko, naga kamar kina jin tsoro ne”.
Murmushi Suhaila tayi bata ce mata komai ba.
Wata ƙofa Kausar ta buɗe wanda nake tunanin nan ne toilet, shiga tayi ta rufo ƙofar, a lokacin ne kuma Suhaila ta samu damar ƙarewa ɗakin kallo tsaf.
Hoton da yake jikin bango naga Suhaila tana kallo, wani handsome guy ne riƙe da hannun Kausar fuskar shi cike da fara’a, sai dai hoton daga gani Kasan ya ɗan kwana biyu saboda yanayin Kausar ɗin.
Tana cikin kallon hotan Kausar ta fito daga toilet ɗaure da towel a jikin ta, ɗan murmushi tayi ganin SUHAILA na kallon hotan tace; “Big bro kenan, ya Ahmad, munyi kyau ne? Tun ban fi 15 ba muka yi hoton”.
Ɗan murmushi Suhaila tayi tace; “Ayya ai gashi nan kuna kama sosai da sosai, sai dai yafi ki kyau”.
Dariya sosai KAUSAR tayi tace; “Caɓɓ ai kuwa kin cuce ni!”.
“Ki shiga kiyi wanka”. Kausar ta faɗa tana goge jikin ta da towel.
Ɗan kallon Kausar ɗin tayi tana son tambayar ta ina towel, sai ji tayi Kausar ɗin tace; “Akwai a ciki ki shiga kawai”.
Kallon ta Suhaila tayi da mamaki tana tunanin yadda aka yi ta gane abunda take son tambayar ta.
Suhaila kuwa da ta shiga cikin toilet ɗin sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, banɗaki kaɗai ya kusa bedroom ɗin su na can Nigeria, ɗan tsayawa tayi tana tunanin ta yadda zata fara wankan, gashi toilet ɗin ba mai jaccuzzi bane, numfashi ta sauke ta kalli kanta a madubi tace; “Haba mana sai kace ba ki kallon Korean da indian movies, baki ganin yadda suke wanka cikin bath tube musamman ma ƴan Turkish ɗin nan”.
Matsawa tayi tana ƙoƙarin kunna tap amma ta rasa yadda zata murɗa shi saboda ba kamar normal tap yake ba.
Ganin zata bawa kanta wahala yasa ta yanke shawarar amfani da hand shower ɗin da take gurin, to fa shi ma dai tap ɗin showern bata iya kunna shi ba, a hankali ta dinga ƙoƙarin kunnawa sai jin ruwa mai mugun sanyi tayi a fuskar ta, nannauyan ajiyan zuciya ta sauke tana ɗan ja baya, kallon kanta tayi sai kuma tayi murmushi, wai ita ce yau take koyan kunna fanfo saboda tazo London.
Wankanta tayi cikin kwanciyar hankali, tayi amfani da shower jell masu ƙanshin gaske taji daɗin jikin ta sosai, towel ta ɗauro ta fito daga toilet ɗin, sai dai bata ga Kausar a ɗakin ba, gaban dressing mirro taje zata shafa mai, nan taga stick note a jikin mirror.
_”Ga kaya nan a kan gado ki saka ki sauko ƙasa zamu shiga kitchen”_
Murmushi SUHAILA tayi tana kallon kanta a mirro nan ta ƙara hango hoton Kausar da Ahmad.
Saurin ɗauke idon ta tayi, kayan taje ta ɗauka dogon wando ne sai kuma rigar sanyi me ɗumin gaske har gwiwa sai ƴar mofula ta ɗaurawa a wuya saboda yadda garin ya ɗau sanyi sosai gashi yamma tayi.
A parlour ta tarar da su har da Hajiya kowa ya saka kayan sanyi.
Hajiya ce tace; “Yauwa ɗiya ta sannu da fitowa, ya gajiyar hanya?”.
“Alhamdullilah Hajiya, ya naki gajiyan?”.
“Babu gajiya SUHAILA, sannan kar na ƙara jin bakin ki ya kira ni da sunan Hajiya, ki nemi wani sunan dai, ko Ammi, Ummi, Umma, Mama, momy, Mamy, duk wanda kika zaɓa amma banda hajiya, so kike kema ki zama yaran gidan nan kowa da hajiya yake kira na?”.
Dariya Suhaila tayi tace; “To Ummi Insha Allah na daina kiran ki da Hajiya daga yau”.
Hajiya Kulthum taji daɗi sosai jin SUHAILA ta kira ta da Ummi.
Nan suka nufi kitchen don shirya dinner, Irish potato suka soya aka yanka plantain, aka soya ƙwai aka haɗa tea, sai natural orange juice.
Shirya komai aka yi a dining, suna shirin zama sai ga Alhaji Umar mai shadda ya shigo, da gudu Zainab taje ta rungume shi tana faɗin; “Oyoyo Daddy”.
Cikin fara’a da jin daɗin ganin ƴar ƙanwar tashi yace; “Oyoyo my daughter amma naji daɗin ganin ki sosai da sosai, ya momyn ki da daddyn ki, hope they are all fine ko?”.
” Yes daddy duk suna gaishe ku”.
Kausar ce ta ɗan tashi ba yabo ba fallasa ta mai *bose* inji ƴan Turkish da faɗe wato kiss guda biyu a kumatu, tace; “You are welcome daddy”.
“Welcome my daughter, ya biki?”.
“Alhamdullilah”. Ta faɗa a taƙaice, hajiya ce tayi saurin tashi tace; “Sannu da zuwa Abban yara”.
Abunda Ummi bata yarda dashi ba turancin ƙarya a gidan ta don babu wanda take yarda ya mata magana da turanci a gida, sai dai idan sun fita shiyasa har yanzu suna jin hausar su sosai da sosai.
SUHAILA kuwa tana gefe tayi tsuro da ido kamar an jijjaga ɓera a buta.
Ɗan kallon ta yayi yace; “Wannan fa daga ina?”.
Hajiya ce tayi saurin cewa; “Muje kaci abinci anjima munyi magana”.
Ganin haka yasa Kausar ta kama hannun Suhaila suka koma ɗaki don ita ma ba son cin abinci tare da daddyn nata take ba.
Hira suka ɗan taɓa sannan daga baya Kausar ɗin ta sauko ƙasa ta ɗibar musu abincin, lokacin kuma ba kowa a dinning ɗin.
*****
“New cook fa kika ce Kulthum, duk cook ɗin garin nan sai kin ɗauko wata daga Nigeria iye, saboda kuɗi sun miki yawa har ki mata visa da passport ku taho tare da ita, lallai ma, kuɗin da nake bar miki ne yasa har kike ganin arharsu haka kina kyauta!”.
“Ba abunda kake tunani bane Alhaji, akwai abunda yasa na ɗauko ta, don haka ka kyautata mun zato plss”.
“Koma menene dai ya kamata ki sanar da ni kafin ki aikata shi”.
Tashi tayi tsaye tana shirin barin ɗakin tace; “Kayi haƙuri nayi kuskure”.
Bata ƙara magana ba ta fice a ɗakin nashi, ɗakin ta ta nufa tana shiga ta zauna a bakin gado, nan da nan naga ƙwalla ta cika mata ido.
Hoton da yake gefan bedside ɗin ta ta ɗauko tana kallon shi.
Wayar ta ta janyo tayi dialing numbern Ahmad.
Bugu biyu ya ɗau wayar, abunda ya fara cin karo da shi shi ne kukan Ummin tashi.
Lumshe ido yayi yana jin kukan nata har cikin ranshi.
A hankali ya furta; “Ummi na”.
Sai da ta ɗan daidaita muryar ta sannan tace; “Ahmad ya kamata kazo in ganka don Allah don Allah, ba don ni ba”.
Shiru yayi yana jin yadda Ummin nashi take roƙon shi tana kuka duk don yazo gida.
Sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske yayi sannan yace; “Ki gayawa mijin ki zan zo gida na ganki, ya san da zuwa na don kar na zo yasa ayi mun korar kare”.
“Yaushe zaka zo London toh?”.
“Yau na shigo Switzerland akwai wani case da muke dashi ne”.