ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Wani farin ciki ne ya ziyarce ta tace; “yaushe zaka zo nan Hilton tau? don Allah kazo na roƙe ka”.
Murmushi yayi yace; “Ummi, zan zo amma sai birthday ɗin Kausar kafin nan abubuwa sunyi sauƙi, aiki ya ragu mun”.
“Allah ya kaimu toh”. Ta faɗa cikin farin ciki mara misaltuwa.
Cikin jin daɗi Hajiya tayi bacci.
Kausar da SUHAILA kuwa sai da suka shirya kayan su tsaf a drawer sannan suka fara tunanin kwanciya bacci.
Ita kuwa Zainab sai da tayi waya da maman ta tana mayar mata yadda aka yi, sannan ta kira Ahmad shi kuma yaƙi ɗaga wayar ta, haka ta kwanta cikin baƙin ciki da ƙunar rai.
Washegari da safe sai da SUHAILA ta ɗan makara sallah saboda yanayin garin ba iri ɗaya bane, lokaci ya ɗan canza.
Tashin Kausar tayi suka yi sallah, sannan suka sauka ƙasa don haɗa breakfast.
Bayan an gama breakfast kowa ya kama gaban shi, Hajiya ta kira Jibril tana tambayar shi yaushe zai dawo daga Nigeria, nan yake sanar da ita zuwa Next 2 weeks kafin nan ya gama ganin patient ɗin shi.
Fatan alkhairi tayi mai tana kewar yaran nata.
_*Ba yawa banji daɗi bane kwana biyu*_
*_Asslama alaikum_*
*_Faɗma Ahmad_*✍????
[6/29, 8:49 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page3️⃣6️⃣to3️⃣7️⃣
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.
*Addu’ar Da Wanda Ya yi Mafarki mara kyau zaiyi.*
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a’uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
– Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
– Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
– Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
– Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.
Idan ya so, ya iya tashi ya yi sallah.
*_The library_*
Bayan su Kausar sun dawo ɗaki take tambayar Suhaila a ina ta tsaya a karatun ta me kuma ta karanta, nan Suhaila take sanar da ita ai degree ne da ita a psychology, Kausar ce ta zaro idano tace; “Wow ni kuma nayi specializing a clinical psychology, kai amma naji daɗi wallahi”.
Ita ma Suhaila cikin farin ciki da mamaki tace; “Masha Allah, kice kina aiki da yara a asibiti kenan?”.
“Ba ma da yara ba har da manya, ai gaskiya ke ma kawai kiyi specializing a nan plss”.
Ɗan dariya Suhaila tayi tace; “A’a bazan yi ba haka ma ya ishe ni, a ina zan kammala tau?”.
Dafa kafaɗar ta Kausar tayi tace; “Ke dai kawai idan zaki yi wallahi ina da hanya kar ki damu”.
Murmushi Suhaila ta ƙara yi tace; “Ki bar wannan maganar zamu cigaba amma ba yanzu ba, ina kike cewa zaki kai ni ɗazu?”.
” Yauwa kin tuna min, zo mu je ki gani tunda ke psychologist ce sai kin fi jin daɗin ganin gurin”.
Fitowa suka yi a tare cikin kayan sanyi suka nufi gurin, a dai-dai wannan ginin mai shegen kyau suka ci birki inda Kausar ta danna wasu numbers sannan ƙofar ta buɗe, suna shiga gurin wani ƙamshi me daɗin gaske ya bugi hancin Suhaila, lumshe ido tayi tana ƙara shaƙar ƙamshin, dai-dai lokacin da ta buɗe idon ta suka ƙaraso cikin gurin.
Wani ƙatoton hoto ne yake kallo su wanda da ka ganshi ka san zana shi aka yi, kuma hoton sai yayi mata kama da wanda Kausar tace mata shi ne ya Ahmad, kallon gurin ta cigaba da yi tana ganin zanuka kalala wasu flowers ne, wasu kuma Kausar ce aka zana kai har da na Hajiya kulthum ma, ɗan gaba suka ƙara yi sai ga zanen Familyn su ya fito reras sai dai mutum huɗu kaɗai ta sani sauran mutum biyun bata san su ba, ɗayan namijin ne ma ta tsaya tana kallon shi sai taga kamar ta taɓa ganin shi a wani gurin. Tafiya kaɗan suka yi suka wuce gurin zanukan, wata ƙofa Kausar ta buɗe sai gasu a wani library mai shegen kyaun gaske, littafai ne a jere a jere, shelf kuwa sun kai kusan guda talatin kuma ko wani shelf zai iya ɗaukan kusan littafi 30, gurin ya tafi da Suhaila sosai da sosai.
Kausar ce ta juyo ta kalle ta ta ce; “Kin ga gurin ko? Yayi miki sosai ko? “.
Gyaɗa kai kawai Suhaila tayi don baza ta iya magana a halin da take ciki ba.
” Ki duba ki gani ko akwai littafin da zai miki, don na san halin mu akwai son bincike da kuma karatu”.
Murmushi Suhaila tayi tana ɗan zagaya gurin yayin da Kausar ta nemi guri ta zauna tana ɗauko wayar ta cikin aljihun rigar sanyin dake jikin ta.
Ita kuwa Suhaila sai duba littafan take tana neman wanda zata ɗauka ta karanta, gaban wani shelf taje ta tsaya taga an rubuta *criminology* littafan gurin ta kalla sai dai basu da yawa don basu fi guda 20 ba, wani littafi ta fara cin karo da shi wai shi *Introduction to criminology by Frank E. Hagan.*
Zaro littafin tayi a hankali tana kallon shi, duk yayi ƙura, ɗan goge shi tayi nan taga an rubuta AHMAD da glitters pen, kallon rubutun ta ƙara yi ta tuna da letter ɗin da jibril ya bata shi ma rubutun da yayi mata shigen irin wannan ne kuma shi ma da glitters pen aka rubuta.
Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙarasawa gurin Kausar tace; “Na samo amma fa na criminology ba na psychology ba”. Dan kallon ta Kausar tayi tace; “Kina sha’awar shi ne?”.
” A’a kawai dai zan duba ne”. Suhaila ta faɗa tana juya littafin.
Cigaba da danna wayar ta Kausar tayi tace; “Na ya Ahmad ne before shi artist ne, duk zanen da kika gani a farkon gurin nan duk shi yayi su, haka kawai daga baya ya koma criminology ba wanda yasan sanda yayi karatun ma sai dai ji muka yi yana aiki da CBI, babu yadda hajiya bata yi da shi ba amma yaƙi jin ta sam”.
Ɗan kallon Suhaila tayi tace; “Karki damu zaki iya dubawa kin ƙara mana ilimi”.
To ta amsa mata da shi nan suka kamo hanya za su fito daga gurin.
Suna hanyar fitowa Suhaila ta bugi wani hoton zane ya faɗi ƙasa nan ta duƙa zata ɗauko shi tana ɗakkowa taga wanda ake kiran shi da ya Ahmad a jikin hotan sai kuma zanen wata budurwa wanda tayi mata kama da Zainab sosai, ya riƙe hanun ta yana kallon ta amma zanen shi ma daga gani ya ɗan daɗe don zainab ɗin bata kai yadda take yanzu ba.
Kausar ce ta juyo jin Suhailan ta tsaya nan taga hotan da take kallo, saurin ƙarasowa gurin tayi tana warce hoton a hannun Suhaila dustbin ɗin dake gurin tasa ƙafar ta ta danna pin ɗin shi yana buɗewa ta jefa hoton ciki tana kama hannun Suhaila suna fita daga gurin.
Suhaila tayi mamakin abunda yasa Kausar ɗin tayi behaving haka, nan ta tuno da maganar Umman sheka. _”Ba ruwan ki da shiga sabgar da ba taki ba”_
Kafaɗa ta ɗaga tana bin Kausar ɗin.
Suna shiga ciki suka tarar da Zainab akan kujera ta hakimce ga remote a hannun ta kai ka ce ita ce ƴar gidan ma.
Wucewa suka zo yi tace; “Ke wa kike da suna Suhaila ne ko mene ne? ina so ki yi min cake, red velvet sannan bana son cream ko kuma wiping cream, normal cake kawai zaki yi”.
Kausar ce ta juyo ta kalle ta tace; “Malama talk to her with respect, kina hauka ne?”.