ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Wani wawan kallo ta jefe shi da shi na baka da hankali, ita abun ma mamaki yake bata, ta san dai iya shekarun shi bazai wuce 27years ba, amma yazo yana cewa wai ita yake so kuma wai auren ta zai yi, which is ta san is a big lie akwai abunda yake so kawai, wanda tasan tana gaya mai abunda yake damun ta ko kallon inda take ma bazai ƙara yi ba, da gudu zai arce, don be mata kama da wanda zai karɓi ƙaddara ba, bama shi kaɗai ba, acikin maza sai an tona da yawa kafin a samu mai karɓar matsalar ta hannu biyu-biyu.
Gyaran murya tayi kafin tace”Ba wulaƙanci nake maka ba Abubakar, abunda kaima kan ka kasan bazai yiwu bane kake faɗa, kana nufin har sai na kusan shekara 30 sannan zamu yi aure umm, kasan sanda zaka samu aiki idan ka fito daga service? See, let be realistic muyi magana akan abunda muke ganin zai iya faruwa, i can’t waste my time akan relationship ɗin da bazan iya building ba, so for this small explanation nasan ka gane abunda nake nufi i don’t need to explain, your are a psychologist, and i too kuma kaima kasan abunda nayi sensing so mu bar maganar a nan please. Thank you very much i really appreciate yadda ka nuna mun soyyayar ka wanda i don’t think akwai ta a cikin zuciyar ka, sai anjima na barka lafiya”.
Nan ta tashi ta bawa hijabin ta iska ta barshi da sakakken baki a gurin.
“Ohhhh my…….. This girl is something”. Ya faɗa yana shafa ƙeyar shi.
“Ohhhh she is also a psychologist which means tayi sensing i just wanna chill up with her, ohhh she is very sharp ooo my….. Amma fa gaskiya nayi missing wannan black beauty babe ɗin, ahhhhh dama so nayi na mata wayo amma ina, ita ko ƴar farar fatan nan da mata suke bina akanta bata gani ba, matsalar ustazan nan kenan, or may be she is the real ustaziya shiyasa tace mun i should go to hell, any way akwai wainda suka fita”.
Nan dai ya gama surutun shi kafin ya bar gurin.
*******
“Aikin banza kawai, ai dama na faɗa miki Abubakar ba son gaskiya yake mun ba, samarin shaho ne kawai wallahi, yau kam dana nuna mai i am a real psychologist be isa yayi fooling ɗina ba tuni ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, sai raba ido yake yi kamar an jijjiga ɓera a buta, haba mana ke ki duba mana ki gani yaro da shi zai auri wacce ya girma da shekara biyu kacal ai kema kin san da sake, shiyasa wallahi gwara ka dinga natsuwa, bawai don ka ɗan kwana biyu a gida ba ka je ka auri wanda bazai ga darajar ka ba sam, don kawai mutane kar su ce ka daɗe a gida, shiyasa wallahi nake nutsuwa, kuma nasan lokaci ne yana yi zanyi auren”.
“Ummm ni kam am speechless wallahi, shege mai kai kamar nawa, ashe duk yaudara ce, amma ni kuma wallahi da muke magana da shi i was trying to read his mind, to read what is going on inside him amma yaƙi bani dama sam, ya ninke ni a baibai, amma kinga yanzu da yake sharp shooter ce har kin hasko mana shi”.
“Ummm abeggi let drop maganar nan nashi da bashi da amfani muyi abunda yake gaban mu”.
“Kin san Ammi tayi pressuring Abbu ta karɓi 80k a gurin shi wai harda photo calendar za ayi da kuma memo”.ni fa kin san ba ko ina nake son hoto na ya fiya yawo ba wallahi haba mana, kuma nasan idan zan mutu baza ta bari nayi da niqab ba”.
“Kai gaskiya kin shiga uku Suhaila mijin ki ma ya huta ba sai yana killace ki ba kema kanki killace kanki kike yi, saura kuma ranar convocation ki zo mana da niqab”.
“Ai kin san baƙaramun aiki na bane zan aikata “.
“Aaa wannan kuma ai bazan damu ba, saboda ina da Ammi a gefe zata taka miki birki”…..
*******
_*Hhhhh drama, drama i don’t have to say it????????????*_
_*we meet tomorrow in sha Allah*_
*_Asslama alaikum_*
*Faɗma Ahmad*✍️
*???????? AL’AMARIN SUHAILA????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
Page3️⃣
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*
*~We are bearer’s of so golden pen????~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*
_Assalama alaikum zaku ga na canza sunan littafin SUHAILAT zuwa AL’AMARIN SUHAILA hakan ya faru ne saboda an rubuta wani littafin a baya me suna SUHAILAT wanda yake mallakin maryam obam shiyasa nace bari na canza saboda kar a samu ruɗani wajen neman littafan ……_
_*The convocation arena*_
“Hmmm kedai bari, ai abun sai addu’a kawai. To yanzu ya ake ciki waye zai mana kayan snacks ɗin ne? Don ni gaskiya bazan samu lokaci ba, kuma kin san Ammi sai tace mu zamu yi tunda kuɗin gurin ta babu makawa a gurin calendar da su memo zai ƙare”.
“A haba kar ki damu mana, Habibi yace zai bayar ayi mun, ke kuwa nasan ko Aunty khadija zata baki snacks a matsayin gudunmawa, ko kuma idan kinje gida sai ki tambayi Ammi muji wa zai yi snacks ɗin, tunda dai na san fried rice babu makawa ita zata yi mana. Kwano huɗu ma ya ishe mu, hajiyan mu kuma tace zata yi mun sinasir da waina kinga ai shikenan mun haɗa komai, drinks kuma tun last week na siyi kaya na”.
“Ummm ni dai kam babu abunda aka siya, sai dai idan na koma gida muji yadda za ayi da Ammi”.
“To ai shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya”.
“Amin, amma fa gurin nan zai cika, don wallahi mu dangi ne da mu kamar tsiya, kuma kowa cewa zai yi zai zo saboda Ammi ta maida abun kamar wani biki”.
“Kai Allah yayi wa Ammi albarka, ai haka ake so, abun taya murna ne Suhaila, sai dai don ke ba sosai kika fiya son shiga mutane ba shiyasa kike ganin kamar tayi gayya”.
“Any way, Allah ya kaimu. Ni kam bari na wuce gida, jibi kizo ki karɓi ɗinkin ki don bazan sake zuwa gidan nan ba ehe”.
“ƴar rainin hankali, Allah ya kaimu da rai da lafiya, ki gaida Ammi”.
“Aha za ta ji, idan Isyaku ya dawo shima kice ina gaida shi don Allah”.
“Tabb ai kam miji na ba sunan shi Isyaku ba, sunan shi Ishaq”.
“Ahaf ana dai jika”.
“Hmmm Allah yasa ki auri me suna Mudi, ko kuma Garba”.
“Ahaf garba ai Abubukar ne, idan Garba ake kiran shi da shi, sai ni kuma na dinga kiran shi da my Abubakari”.
“Uhmmm Abubakar na B. U.K kenan kike nufi? ????
“Aikin kawai, Allah ya sawwaƙa ni kam har ma kin ɓata mun rai kinga tafiya ta”.
“A haba Aunty Suhaila Allah ya huci zuciyar ki bari na zo na raka ki!
” A’a kiyi zaman ki na gode wallahi sai anjima, ba fushi nayi ba, ki gaida Habibin ki!
******
“Yauwa Ammi nace mun gama shirya komai, wa zai yi mana snacks ne?
” Ai kema kin san wanda zai mana snacks, na yiwa hajiya khadija magana tace za tayi in sha Allahu”.
“Okay, drinks fa?
“Anjima idan Mubarak ya dawo daga islamiyya zai je ya siyo mana. Fried rice Kuma ɗazu munyi waya da fatima tace jibi zata shigo kanon, idan tazo tare zamu haɗu da su Umman ki ta sheka duk ayi girkin wannan ba wani abu bane”.
“Ammi da gaske ya fatima zata zo!?
” Eh haka dai tace mun ɗazu”.
“kuma fa munyi waya da ita jiya da daddare tace mun Abban su Nihla yace baza ta zo ba har nake cewa zan kira shi”.
“Aaa to inaji dai so take ta tsokane ki, amma idan ba haka ba ina shi ina hanata zuwa wannan sabgar Suhaila?
“Wayyo daɗi bari na kira ta a waya”.
“To shikenan, bari na shiga gurin maman su Hassan muji yadda za ayi zancen calendar ɗin, tace ƙanin ta ya iya sosai , kinga idan aka yi calender 50 sai ayi memo ma 50, ko da baka samu duka ba ka samu ɗaya ai ba lefi ko?