ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Saurin riƙe hannun ta Suhaila tayi tana girgiza mata kai.
Cikin nutsuwa da sanyin murya tace; “Aiki na ne dafa abinci don haka barta zanyi”.
Ganin Kausar taƙi sakin fuska yasa Suhaila tace; “Come on, ba sai ki koya ba kema”.
Murmushi Kausar tayi suka wuce zuwa Kitchen.
Suna shiga suka tarar da Hajiya tana haɗa coffee, saurin kama mata Suhaila tayi tace; “Haba Ummi da kin bari nayi ai, me yasa baki kira ni ba?”.
Girgiza mata kai Hajiya tayi tace; “Bafa don dafa abinci na taho dake ba, sanda nake so zan ce ku zo muyi girki, sanda nake so kuma zan yi girki na da kaina kamar yadda na saba”.
Kallon ta Suhaila tayi tana mamakin abunda ta faɗa.
“Kar kiyi mamaki”. Hajiya ta faɗa tana cigaba da aikin ta.
Shiru suka yi dukkan su suna kallon ta.
Katse musu shirun tayi tana faɗin; “Uhmm tau yanzu me kuka shigo yi Kausar? Me za a dafa mana?”.
Har Kausar ta buɗe baki za tayi magana Suhaila tayi saurin cewa; “Ummi cake za muyi red velvet”.
Juye coffee ɗin tayi daga cikin coffee maker ɗin tace; “Masha Allah, ina wancan uwar son jikin? ita banda ita za kuyi?”.
Taɓe baki Kasaur tayi tace; “Wallahi ta sha zaman ta *Ummi* bamu da buƙatar ta a nan”.
Har ta juya zata fita ta ɗan dakata jin Kausar ta kira ta da Ummi, wani farin ciki taji ya ziyarce ta, daga jiya zuwa yau har ta kama jin Suhaila na faɗa, “Allah sarki Ahmad bayan kai babu wanda yake ce mun Ummi yau gashi Kausar ta faɗa”.
Ita kuwa Kausar cigaba da sabgar ta tayi don bata ma san ta faɗa ba, ita kuwa Hajiya har sai da kwalla ta cika mata ido.
Tana fita waje ta kira Ahmad ta sanar da shi yau Kausar ta kira ta da ummi, shi ma yaji daɗi sosai, nan yake tambayar ta ko me yasa ta kira ta da hakan, don ya san an koya mata an koya mata amma ta kasa koya.
Nan take sanar da shi zancen Suhailan.
“Allah sarki Ummi Allah ya mata albarka”.
Amin ta amsa masa da shi tana kashe wayar.
Bayan sun gama cake ɗin aka kai wa Zainab nata, su kuma suka saka nasu a fridge don ba yanzu za su ci ba.
Hajiya ce ta kira su, nan ta basu kuɗi tace da Kausar suje mall a siyawa Suhaila sabon sim card wanda zata kira ƴan uwanta, sannan kuma su siyo abunda babu a gida.
Driver ne ya kaisu nan suka siyo sim card ɗin sannan suka yi siyyaya ciki kuwa harda kayan cake su nuzzles ne, spatula, turn table, su cake pan da sauran abubuwa wai za a fara koyawa Kausar cake, har da wiping cream suka siyo wanda za su decorating wanda suka yi ɗazu.
Suhaila kuwa ba abunda take tunowa na sha’anin gidan su, domin kuwa idan tace bata manta ba to tayi ƙarya saboda yadda aka karɓe ta a gidan kuma babu wulaƙanci, ga yadda Kausar take mu’amala da ita kamar yayar ta, cikin farin ciki da annashuwa suka koma gida.
Nan suka buɗe fridge suna jera kayan da suka siyo, Suhaila ce tayi ido biyu da inibi, masoyin ta abun ƙaunar ta, ai bata san sanda ta miƙa hannu ta ciro shi ba, nan da nan ta cire guda ɗaya ta jefa a bakin ta tana wani lumshe ido.
Kausar kuwa yatsina fuska tayi tana kallon ta kamar wacce take cin kashi.
Bayan Suhaila ta buɗe idon ta taga irin kallon da Kausar ke mata, girgiza kai tayi tana buɗe hannu alamar me ya faru, nuni tayi mata da inibin tana daɗa yatsina fuska.
“Baki so ne?”. Suhaila ta faɗa tana ƙara jefa wani a bakin ta.
“Ya Ahmad baya so, idan yaci har amai yake yi, tun ina yarinya da yaga na ɗauka zan ci idan ana cin fruit sai ya buge hannu na yace poison, shikenan nima na daina ci”.
Dariya SUHAILA tayi har da su riƙe ciki tace; “Wannan ne poison ɗin, kai har naji ina son ganin shi wallahi, wai poison, very funny wallahi”.
Daɗa taɓe baki Kausar tayi tace; “Ni dai ki daina ci idan ba haka ba, zan yi amai yanzun nan”.
White rober ɗin da suka cire kaya SUHAILA ta sa a ciki tace; “Ni kuwa kinga favorite ɗina ne, kamar na mutu idan na daɗe ban ci shi ba, kuma ko a hanya ko hannun waye indai na gani sai nace ya tsammini”.
“Wata rana zaki ci na ƴan yankan kai”. Kausar ta faɗa tana cigaba da jera kayan a fridge.
“Never”.
SUHAILA ta faɗa tana ɗan ƙara buɗe robar ta ciro wani ta saka a bakin ta.
Ɗaki suka koma nan SUHAILA ta ɗauko wayar ta ta saka sim ɗin a ciki.
Ya Fatima ta fara kira, a ɓangaren Fatima kuwa tana ganin kiran Sabuwar number. Kamar ta waje yasa tayi saurin ɗauka ta kara a kunnen ta don Farida ta sanar da ita abunda yake faruwa.
“Ya Fatima”, ta faɗa cikin sanyin murya.
Kuka Fatima ta fashe da shi tace; “kina ina yanzu? are you okay? Are you safe?”.
“Ya Fatima am okay, am safe kar ki damu, ina su Nihla da Walid? da kuma ya Mujahid, da fatan duk suna lafiya ko?”.
“lafiya lau suke, ya abubuwa? Abunda Ammi tayi kenan daman? shi yasa ta takura ki dawo gida?”. Kallon Kausar SUHAILA tayi tace; “rah hakiki ba’aden, bye intibih ala halek mani la wahade”.(Zamu yi magana anjima, bye ki kula da kanki bani kaɗai bace)”. Bata bari tayi magana ba tayi saurin kashe wayar.
Abbun ta ta kira suka gaisa shi ma ta sanar mishi da tana cikin ƙoshin lafiya ba abunda yake damun ta.
Daga ƙarshe kuma ta kira Ammi suka gaisa ba yabo ba fallasa, tana da niyyar tace a bata su Farida kuɗin suka ƙare.
Littafin da ta ɗakko ta buɗe ta fara karantawa, abunda ta fara cin karo da shi shi ne; “introduction, criminology are dedicated to studying, not only the causes of crime but the social impact as well”.
Ta sauko definition :is the scientific study of crime, including it causes, responses by law enforcement, and methods of prevention…”.
Haka dai ta cigaba da karatu tana yi tana jotting abunda ya shige mata duhu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda SUHAILA tana gama duba littafi suke zuwa su ɗauko wani, wani zubin ma idan Kausar ta tafi gurin aiki ita kaɗai take zuwa libraryn kasancewar yanzu ta san password ɗin ƙofar, ita da Kausar kuwa kullum shaƙuwa ce take ƙara shiga tsakanin su yayin da Zainab take kishi da Suhailan ganin ko kulata Kausar bata yi yanzu, a baya duk da basa shiri amma at least ɗaki ɗaya suke zama kuma ko ɗan faɗan ne sunyi amma yanzu sam sai dai ta zauna a ɗaki gashi sahibul ƙalb ɗin nata baya gidan kuma bata san sanda zai zo ba.
Bayan sati uku Jibril ya fara shirye-shiryen dawowa daga Kaduna ganin ba ta yadda zai ga SUHAILA ya jira ya jira amma ko sau ɗaya bai ji ance tazo ba.
A ɓangaren Suhaila kuwa sai da tayi sati biyu a London sannan ta ciro dream catcher ɗin ta ta rataye a jikin windown ɗakin Kausar.
Kausar kuwa daga gurin aiki ta saci hanya ta tafi har Switzerland gurin Ahmad, kuma sai da ta kwana biyu a can.
Bayan ta dawo sai da Alhaji Umar ya mata duka kuma yace she is banned to go out for good 1 month, yasa kuma aka ɗaukar mata excuse a gurin aiki.
Ya kuma sanarwa da hajiya in dai ta ƙara zuwa ganin shi sai ta bishi, kuma ita ma sai ya cire ta daga cikin ƴaƴan shi tunda bata jin magana kamar yadda Ahmad ɗin shi ma baya jin magana.
Haka Kausar ta dawo wata iri inda Suhaila bata ji daɗin abunda ya faru ba.
Jibril kuwa yana dawowa gida ya tarar ana wannan crisis ɗin shi ma baya son abunda daddyn nasu yake yi amma ba yadda za su yi da shi, sai da ya kwana huɗu a gidan amma sam bai haɗu da Suhaila ba, sau biyu yana ganin wulgawar ta tana shiga cikin library amma ya kasa gane wace ce kuma me take yi a libraryn Ahmad. Gashi bai san password ɗin ba, shi dai yana hango ta, da yake side ɗin su a jikin ginin libraryn yake.