HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

 

Kwance yake akan kujerar shaƙatawa a cikin garden, inda iskar sanyi take kaɗawa ga dare yayi sosai don wajen 10:00pm ne, sanye yake cikin riga da wando sai wata ƙatuwar jacket da yasa ga wata uwar mofula da yaɗe ta a wuyan shi, hanun shi ma cikin safa suke masu ɗumin gaske, ƙafafun shi ma cikin takalmi suke, ya yaƙi sanyi ta ko ina.

A hankali yake sipping tea ɗin da yake gefan shi yana kallon sama.

Haske ne ya kawo dai-dai windown ɗakin Kausar, kamar an ce ya kalli gurin ya hango dream catcher ɗin da ba zai taɓa mantawa da shi ba, zabura yayi yana zama haɗe da ƙurawa wajen ido yana ƙara kallon abun, bai fita daga ruɗin da ya shiga ba yaga ta buɗe labulen ɗakin a hankali, sanye take cikin kayan baccin ta pink in Color ta ɗora rigar sanyi akai, sai ɗan ƙaramin mayafin da tayi rolling kanta zuwa wuyan ta da shi, ɗan shafa dream catchern tayi tana sakin murmushi wanda har sai da one side dimple ɗin ta ya lotsa fararen haƙoranta suka bayyana.

Jibril kuwa ƙamewa yayi a gurin yana kallon ikon Allah haɗe da murza idanun shi yana daɗa tabbatar da SUHAILA ya gani, kuma a gidan su, gidan nasu ma a ɗakin ƙanwar shi, ɗan marin kan shi yayi yana so ya tabbatar da ba mafar ki yake ba…..

*****

_*Tofa ga Suhailan ga Jibril, ko me zai faru? oho*_……

_*Ma’asalama, Faɗma Ahmad*_✍????
[7/1, 9:13 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*Page 3️⃣8️⃣to3️⃣9️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

*Addu’a Yayin da Aka ji Tsawa*

Abdallah bn Zubair ya kasance idan ya ji tsawa sai ya daina magana, ya ce;

سُبْحَانَ الَّذِي يُسَبِّحُ الرَّعْدُ بِحَمْدِهِ، وَالْمَلاَئِكَةُ مِنْ خِيفَتِهِ.

Subhanal-lathee yusabbihur-ra’adu bihamdih, walmala-ikatu min kheefatih.
Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa ta ke wa tasbihi da godiyarsa, Mala’iku ma suna yi saboda tsoronsa.

*_Get to know each other_*

 

Kamar an tsikare shi yayi saurin tashi yana ƙara zuba mata idanuwan shi, ita kuwa Suhaila sai murmushi take ƙara saki ba tare da ta san da Allah yayi hallitar shi a gurin ba.

Cikin sauri har da su tuntuɓe ya bar garden ɗin, ya nufi hanyar shiga cikin gidan, yana zuwa ya tura ƙofar palon, Zainab dake zaune a palo tayi saurin juyowa tana kallon shi.

“Ya Jibrin ina zaka je haka kake zabga wannan uban saurin?”

Ko kallon inda take be yi ba ya fara hawa stairs, ganin bi ɗaya-ɗaya zai ɓata mai lokaci yasa ya fara haɗa biyu-biyu don ya ƙarasa zuwa ɗakin Kausar ɗin, yana zuwa be wani damu ba ya buɗe ƙofar ɗakin, yadda ya barta haka ya same ta, don inuwar ta kawai yake hangowa ta cikin labulen.

Idon sa ne ya kai kan bed bench ɗin da yake gurin nan ya ga box ɗin da ya bata, lumshe ido yayi yana sauke nannauyan ajiyar zuciya don yanzu ya ƙara tabbatar da itace.

Kausar da take kwance idon ta a lumshe kamar me bacci amma ba baccin take ba.

Saurin buɗe idon tayi tana kallon shi from head to toe kafin tace; ” Ya Jibril me kake yi a nan kuma?”

Itama be kulata ba yayi saurin ƙarasawa jikin windown, a dai-dai lokacin kuma SUHAILA na shirin juyowa jin Kausar tayi magana,sai dai kash kafin takai ga buɗe labulen har ya rigata buɗewa, hannun ta yayi saurin janyowa tana barin jikin windown, ita kuwa SUHAILA saurin zaro idanu tayi ganin ƙatoton namiji a ɗakin su don har tsoro ya bata.

Saurin fizge hannun ta tayi tana shirin yin magana, amma kafin takai ga buɗe bakin ta ya janyo ta ya rungume ta tsam a jikin shi, wani shock ne ya kama SUHAILA haɗe da fargaba, ɗan shiru tayi tana tunanin me ke shirin faruwa da ita, meye haka? Wannan kuma waye shi da har zai zo ya rungume ta haka?

“Innallilahi wainnailaihi raji’un” ta fara maimaitawa a cikin zuciyar ta.

“Ni Suhaila ina na kawo kaina? Na shiga uku na”.

Gaba ɗaya ƙarfin ta tattaro tana ture shi amma ina yaƙi barin ta tabar jikin shi.

Wani irin yunƙuri tayi tana ture shi daga jikin ta, babu shiri sai jin shi yayi a jikin dressing mirror, gaba ɗaya kayan da suke kai kuwa sai da suka samu masauki a ƙasa.

Cikin ɗaga murya duk ƙwalla ta taru a idon ta tace; ” Kana da hankali kuwa!? Kasan me kake shirin aikawata? Kai wanane kuma me ya kawo ka nan?ka sanni ne? Meye haɗi na da kai?”

Kasaur ce tayi saurin dirowa daga gado tana riƙe Suhaila da jikin ta ya fara rawa babu shiri.

Kausar ce ta kalle shi tace; “Ya Jibril, me ke faruwa ne? Me ya faru? Ka santa ne?”

 

Dai-dai ta kanshi yayi yana miƙewa da kyau yace; ” Am really sorry….. I mean am sorry i don’t mean it…. it just happen”.

Kallon shi ta cigaba da yi tana ƙara zaro idanun, “Wace irin rayuwa ce wannan? anya yana da cikakken hankali kuwa?

“Ya Jibril kamar ya? akwai wani abu mana, ka santa ne? Ko ka taɓa ganin ta a wani gurin ne?

Dai-dai ta kan shi ya ƙara yi yace; ” Suhaila am doctor Jibril, do you remember? The letter, the dream catcher and the watch”.

Saurin ɗagowa tayi ta kalle shi tace; “Really!?

” Yess am sorry, don Allah, is just that na daɗe ina neman ki, a koda yaushe tunanin ki nake, but then ban san ta yarda zan sake ganin ki ba, ko wannan zuwan da nayi saboda na ganki na daɗe ban dawo ba, ashe kina nan gidan mu”.

Suhaila shiru tayi bata ce komai ba.

Kausar ce tace; ” Come on, stop this drama”. Ta ƙarasa maganr tana kama hannun shi ta buɗe ƙofa tace; ” My head is aching me, gobe da safe ayi wannan maganar, bye good night”.

Ta rufe ƙofar ta tana komawa cikin ɗakin tace ; “Sorry Suhaila sai kin mai uzuri kinji ko, don’t mind him.Kawai bacci na shirin ɗauke ni yazo ya tayar mun da hankali”.

“By the way, a ina kika san shi? Naji yana cewa doctor Jibril ne, kin taɓa haɗuwa da shi a Nigeria ne?”

Duk abunda ya faru Suhaila ta sanarwa da Kausar na haɗuwar su da Jibril.

“So kice love birds ne ku, lallai, congratulations to”.

Ɗan dukanta SUHAILA tayi tace; ” Ni kam ba wani, ba son shi nake ba”.

“Uhmm did i ask your opinion mrs? Kar dai ki faɗi abunda zaki zo kina dana sani nan gaba”.

Dariya Suhaila tayi tana ƙara dukan Kausar.

Jibril kuwa bayan Kausar ta fitar da shi jingina yayi a jikin ƙofar yanajin wani farin ciki mara misaltuwa, yau gashi ga SUHAILA kuma wai a gidan su, unbelievable,ta ya hakan ta faru.

Sanin ko zai mutu Kausar baza ta ƙara buɗe ƙofar ba yasa ya wuce zuwa part ɗin su.

Kayan jikin shi ya cire ya shige toilet yana sakarwa kan shi ruwa me ɗumin gaske, har wani tiriri2 ne yake fita daga jikin shi.

Bayan ya fito ya saka kayan baccin shi yana shigewa cikin bargo, nan da nan bacci me daɗin gaske yayi awan gaba da shi.

Itama SUHAILA a nata ɓangaren taji daɗin ganin Jibril ɗin gashi kyakkyawa, duk wani abunda mace take so akwai shi a jikin shi don ma ba fari bane, hango ta tayi sanda ya rungume ta yadda ya ɗora kanta a ƙirjin shi.

Saurin kawar da tunanin tayi tana faɗin”A’uzubillahi, me yake shirin faruwa dani ne? Ya Allah ka tsare ni daga irin wannan rayuwar, ka ƙara sa mun tsoron ka a cikin zuciya ta, dumin ina tsoron irin wannan rayuwar, oh ni Suhaila wa ya kaini yarda nazo irin wannan garin? Ya Allah ka tsare mun imani na, ya Allah kada ka barni na aikata abunda zan zo ina da nasani a garin nan, ya Allah ka fitar dani”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button