HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Addu’ar bacci tayi ta shafawa Kausar don tasan bata yi ba.

Kausar kuwa idon ta biyu, tana jin sanda Suhaila ta shafa mata addu’ar, nan da nan taji sonta ya ƙara shiga zuciyar ta, da Hajiya ce kusan kullum sai tazo ta tuna mata yin addu’ar bacci amma tun da Suhaila tazo ta dena shiguwa, nan ta fara tunanin anya Hajiya ba da wani abu ta kawo Suhaila gidan ba kuwa. Haka dai ta gama tunanin ta har bacci ya ɗauke ta.

Kwance yake akan madaidaicin gadon nashi inda ya ƙurawa guri ɗaya ido , yayi nisa a tunani yaji wayar shi ta fara ƙara wanda inajin wannan shine karo na kusan ashirin..

 

Ɗan tashi yayi yana buga wani uban tsaki haɗe da janyo wayar, ganin sunan Zainab yasa ranshi ya ƙara ɓacci matuƙa, nan da nan yaji zuciyar shi ta hau sama,wani jiri ne yaji yana shirin kama shi ga sarawar da kanshi yake yi.

Wayar ya ɗauka ya kara a kunne yana faɗin”Damn you Zainab!will you ever stop calling my nunber? Kin dame ni, kin ishi rayuwa ta,don Allah ki rabu da ni, na faɗa miki, and this is the last warning next time idan kika ƙara kira na sai nazo har gida na ɓata miki rai wallahi, ni nace kizo England saboda ni? , inada business da ke ne? I hate you, i hate you, ke wacce irin mara zuciya ce kin kasa fahimta, all the memories da kike da su akai na ki manta da su, that will never ever happen, kin fahimta ai, mayya kawai mara hankali, just stay away from me Stay away from me!!!”

 

Cillar da wayar yayi ba tare da ya bari yaji me zata faɗa ba.

Zainab muwa ji tayi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu cikin kuka tace”Wayyo Allah na, Umma duk ke kika ja mun da kin barni da ya Ahmad ya aure ni tuni amma don wani abu naki can kika ɓata mana komai namu”.

Shi kuwa Ahmad tashi yayi, nan da nan yaji kan shi ya fara sarawa, baya son hayaniya,

Drawer ya buɗe ya ɗakko wani ɗan ƙaramin tin, kallon abun nayi sai naga kamar ina ganin shi a films kamar irin giyar nan da masu kuɗi suke sha na wane da wancan wanda ko cup ɗaya baya ci.

Hanun shi ya tsaya yana kallo, wani ɓacin rai yaji ya saukar mishi buɗe tin ɗin yayi, sai dai be kai shi bakin shi ba, ya cillata ta daki bango, nan da nan alcohol ɗin dake ciki ya fara zubewa a ƙasa, yasan ba abunda zai sha yaji sauƙi a halin da yake ciki sai depression pills ɗin shi, drawer ya buɗe, yana ɗakko su ya ɓall yasha, bayan kamar 10 minutes yaji hankalin shi ya fara kwanciya.

Sai da ya ɗan samu nutsuwa sannan ya fita cikin daren yana zabga uban gudu kuma bayan bashi da inda zai je, haka yayi tafiyar kusan one hour yana gudu a dawowa kuma ya shiga bus ta dawo dashi gida da ƙyar ya samu bacci ya ɗauke shi…

*****

Washegari da safe da haka Zainab ta tashi idon yayi ƙananu, round ɗin idon kuma yayi baƙi, da safe kowa sai kallon ta yake alamar tasha kuka.

Shi kuwa Jibril Allah Allah yake ya gama breakfast yaje ɗakin Kausar ya samu Suhaila, kasancewar bata breakfast tare da su tunda yawanci Dadday yana nan.

Kallon shi Hajiya Kulthum tayi tana hango farin cikin da yake tattare da shi.

“Uhmmm, Daddyn yara me ka bawa Jibril ne? Naga yau da farin ciki ya tashi sosai”.

Kausar ce tayi dariya tace; ” Ai dole ku ganshi cikin farin ciki tunda yayi budurwa”.

Daddy ne yayi saurin ɗagowa yace; ” Budurwa kuma? Amma dai ba a garin nan ba ko?”

Shiru gurin yayi babu wanda ya tanka mai, don shi Jibril be ma san me zai ce masa ba, Kausar ya gallawa harara yace ; “Ƙarya take Daddy ni babu wata budurwa da nayi”.

Kausar kam bata sake magana ba har ta gama cin abincin ta.

Tana miƙewa shima Jibril ya miƙe, Daddy ne yace; “Kar kayi nisa fa, kafin ka wuce gurin aiki zaka ajiye ni a company don yau bana jin yin driving, da to ya amsa mai yana bin bayan Kausar.

Riƙe mata hannu yayi yana kallon ta, ɗan kallon hannun tayi sannan ta ƙara kallon shi tace” What? What again? Ya Jibril you should stop disturbing me fa, kace baka da budurwa yanzu kuma me kazo yi? Oya let go off my hands please”.

“Haba Kausar please now, i promise idan kika mun abunda nake so zan yi miki komai duk abunda kike buƙata”.

Ɗan shiru tayi tana kallon shi tace; “Duk abunda nake buƙata fa?”

“Yess now”.

“Okay, okay inajin ka”.

“Please, kinga yanzu zamu fita da Daddy ko”.

“Uhmmm” ta amsa tana jiran taji me zai ƙara faɗa.

“I want to have a words with Suhaila, please anjima ki haɗa mana gurin da za mu haɗu, i mean, gurin ya zamana kamar we are going for a date”.

“Ohh, a date” ta faɗa tana mai wani irin kallo.

Bata bari taji me zaice ba, ta ƙara gaba.

Kallon ta ya yi tana tafiya yace; “Kausar please”.

Bata juyo ba tace mai”Just remember your promise, because there will be a day da zan tambaye ka ooooo just remember”.

Murmushi ya saki yace; “Yess i will”.

Juyowa yayi ya nufi down stairs, yana zuwa suka wuce da Dadday ya ajiye shi a company shi kuma ya wuce asibitin da yake aiki.

A ɓangaren Ahmad kuwa da mugun ciwon kai ya tashi, da ƙyar ya samu ya tafi gurin da suke da case ɗin su, haka dai ranar kowa ya ganshi haka-haka sai a hankali.

Nigeria….

Kwana biyu Surayya taji Suhaila shiru babu ita ba labarin ta hakan ne yasa yau ta shiryo tazo gida don sanin lafiya me ya faru, tana zuwa Ammi take sanar da Surayyan ai Suhaila bata nan tana London kuma wai aiki ta tafi, abun yayiwa Surayya ciwo, da ilimin ta da komai a ɗauke ta akaita dafa abinci can wata ƙasa ba tare da an san wani hali zata shiga ba, ita ba jahila ba ballantana ace, kai kwaɗayi ma be yi ba a rayuwa, haka dai ta gama mitar ta, haka nan ta koma gida tana don jiran Suhailan, don ta san zata kira ta yanzun ma wa yasan a yadda take, may be tana cikin halin rayuwa shiyasa bata samu ta kira ta ba.

London, England….

Da misalin 9:00pm Kausar tace da Suhaila tazo ta rakata library akwai wani littafi da take so za ta yi amfani da shi.

Har Suhaila ta tashi za su fita da kayan baccin da ta saka, Kausar ta ciro mata blue black abaya da ta sha farin stones.

Ɗan kallon ta tayi tace; “For what” tana ɗan girgiza mata kai.

“For nothing” Kausar ta faɗa tana jefa mata rigar.

Ɗauka tayi ta saka suka fito, sai da suka zo dai-dai library taga Kausar ta canza hanya bata kawo komai ba, ta bita suka shiga cikin wani guri, suna buɗe ƙofa suka ga gurin dumɗin babu haske ko kaɗan, ita dai Suhaila bata farga ba sai ji tayi kamar an buɗe ƙofa an fita tana shirin tsala ihu wani haske me shegen kyau ya kawo.

Kallon gurin tayi taga yadda ya haɗu, flowers ko ina, ɗan juyowa tayi tana ƙara kallon gurin da kyau, wani rubutu ta hango a dai-dai wani gurin zaman mutum biyu wanda ya ƙawatu da jajayen furanni, ga wani ƙyalli da yake fita daga ƙasan table ɗin. Plate ne guda biyu a kan gurin sai cups ma guda biyu sai spoon, folk, da kuma table knife.

Rubutun ta ƙarewa kallo tana son ganin me aka rubuta *” I like you Suhaila will you be my friend*?

Ji tayi kawai ta saki dariya, saboda jin abun tayi kamar wani wasan yara, wai like, ba ma love ba.

Tana tsaye wata ƙofa ta buɗe, nan jibril ya shigo cikin gurin, sanye yake cikin black suit rigar ciki kuma fara, yayi kyau sosai ga wani ƙamshin shi da ya daki hancin ta, lumshe ido tayi, kamar an tsikare ta tayi sauri ta buɗe idon tace; “No sheɗan ne kar ki biye mishi”.

Ɗan tsayawa tayi tana kallon shi idan tace be mata kyau ba ta zabga ƙarya, idan tace be tafi da zuciyar ta ba ta yaudari kanta, idan tace ba taji komai a kanshi ba ta cuci zuciyar ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button