HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Cikin sanɗa ya ƙaraso gurin, turaren shi ne ya ƙara dukan hancin ta, nan da nan taji cikin ta ya bada ƙuuu, ita kan ta tasan bata yarda da kanta ba ballantana kuma shi, dole tabar gurin idan ba haka ba idan yace zai yi wani abu bata jin zata iya hana shi, gwara tun yanzu ta samar ma kanta mafita.

Kamar yasan me take tunanin yace; ” Ki samu guri ki zauna, wallahi wallahi ko kusa dake bazan zo ba, kar abunda ya faru jiya yasa ki fara wani tunanin akai na to ba haka nake ba”.

Ɗan shiru tayi tana kallon shi, rantsuwar da yayi itace zata sa ta zauna idan ba haka ba da barin gurin za tayi.

Zama tayi shima ya zauna, ɗan table ɗin da ya ke kusa da su ya buɗe abinci kalala ya bayyana, saurin kallon gurin tayi abunda ta fara cin karo da shi shine inibi.

Har ya buɗe plate zai fara zuba abinci tace; “A’a bazan ci komai ba bana jin yunwa, grapes ɗin can kawai zanci sai kuma ruwa idan na gama sha”.

“Yadda kike so haka za ayi” inibin ya ɗakko ya ɗora mata akan plate ɗin babu wani ɓata lokaci ta fara ci, dama wanda takai ɗakin Kausar duk ta fitar da shi.

A hankali ya fara magana”Tun ranar da na ganki a asibiti, naji kin bani tausayi, daga lokacin da naji mamaki tace you’re divorcee naji na fara sonki a cikin zuciya ta, kuma so na tsakani da Allah, abunda yasa ban faɗa Miki ina son ki a lokacin ba, saboda nasan idan nayi magana a lokacin kamar naso kaina ne shiyasa na bar miki letter, kuma nace ki neme ni amma shiru, ko da yaushe a cikin damuwa nake, Allah Allah nake naga kiran ki amma shiru, dana koma Nigeria na ganki a gurin bikin cousin ɗin ta ji nayi kamar nayi hauka dana nemeki na rasa”.

Cikin zuciyar ta tace; “Ohhh dama shi ya ƙwalla mun kira”.

Katse mata tunani yayi da ya cigaba da magana”So, nace may be ba ke bace, na dawo Kaduna ko zanji ance kinzo amma shiru.Me yasa baki kira ni ba? ”

Da yake ba yarinya bace yasa tace; ” Na kira ba adadi amma bana samun numbern ka kusan kullum sai nayi trying amma bana samun ka, nima kuma na shiga cikin damuwa”.

Kallon yadda take shan inibin yayi yace; “Is it your favorite?” ya ƙarashe maganar yana nuni da inibin hannun ta.

Gyaɗa mai kai tayi tana cigaba da cin abun ta.

“Dama so nake naga kin kira ko baki kira ba, akwai faɗan da muka yi da Kausar, kin san sako da sako, tace na kaita New York Daddy yace baza ta je ba shine ta huce akan waya ta”.

Ɗan dariya tayi tace “Ayya”.

“Me ya kawo ki gidan mu?”

Ya jefo mata tambaya.

“Am here as a cook”. Ta bashi amsa babu wani tsoro.

” A Cook fa, duk kyaun ki, da nutsuwar ki, da kamalar ki, ace as a cook,gaskiya aa kisa a ranki you are here as my wife kinji ko?”

Ɗan dariya tayi tana tashi daga kan kujerar tace; ” Thank you, sai da safe”.

Bin bayan ta yayi yace “Please mana ki tsaya”.

Kafin ya ƙara magana har ta fito waje, “Dare yayi” ta faɗa tana waigen shi.

“To shikena I love you”.

Juyowa tayi tana zaro ido tace”Shhhhhh”. Tana mai nuni what if wani yaji fa.

Hannu ya buɗe yana taɓe baki irin sai me?

Ai kuwa duk abunda ya faru bayan fitowar Suhaila Hajiya Kulthum na tsaye a jikin window tana kallon su………

*****

*_Tofa! Ko ya Hajiya zata ji? Ko mai zata ce oho_*

*_Assalma alaikum, Faɗma Ahmad_*✍????
[7/3, 5:07 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*Page 4️⃣0️⃣to4️⃣1️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

*Addu’a Yayin da Aka ji Tsawa*

Abdallah bn Zubair ya kasance idan ya ji tsawa sai ya daina magana, ya ce;

سُبْحَانَ الَّذِي يُسَبِّحُ الرَّعْدُ بِحَمْدِهِ، وَالْمَلاَئِكَةُ مِنْ خِيفَتِهِ.

Subhanal-lathee yusabbihur-ra’adu bihamdih, walmala-ikatu min kheefatih.
Tsarki ya tabbata ga wanda tsawa ta ke wa tasbihi da godiyarsa, Mala’iku ma suna yi saboda tsoronsa.

 

*This page is dedicated to Umar Ɗalhat…godiya me yawa..*

Oudeedat.
Aunty sumiee.
Fatima batula.
Harira Aliyu.
Shatu.
Fharidatey.
Umm yusuf.
Teemachutyy.
Maman twins.
Shamsiyya.
Princess Fatima mazudu.

Da duk wani member na goledn pen, ina miƙa gaisuwa ta gare ku Allah ya ƙara haɗa kan mu baki ɗaya.. Heart you guys❤️

_*Get to know each other 2*_

 

Ummi kuwa ji tayi gabanta yayi munmunar faɗuwa jin abunda Jibril ya furta, ga kuma Suhaila da ta gani cikin farin ciki. Kanta ta fara tambaya.

“To a ina ya santa? yau kwanan shi biyar da dawowa a yaushe suka haɗu har suka yi wannan shaƙuwar?”

Sanin bata da wanda zai bata amsa yasa ta maida Windown ta rufe ta kuma cikin ɗakin ta ƙudiri niyyar gobe da safe zata tambayi Suhailan.

Washegari da safe da wuri su Suhaila suka tashi don yanzu Kausar har ta saba da tashi da wuri.

Bayan sunyi sallah Suhaila ta kalli kausar tace; ” munafuka wato ke kika shirya gurin ko? Har da wani kai grapes saboda kin san favorite ɗina ne ko?”

Tintsirewa da dariya Kausar tayi tace; ” Uhummm, alƙawari yayi mun, ni kuma zan iya yin komai don cikar buri na. To how far? Ya yi miki ne yayan nawa?”

Ɗala mata duka Suhaila tayi tace; ” Ban sani ba, dalla malama tashi muje mu kama aiki zaki zo nan ki cika ni da tambayoyi”.

Dariya Kausar tayi, nan suka fito suka nufi kitchen, breakfast suka fara haɗawa inda Alhamdullilah yanzu Kausar ta iya abubuwa da yawa, suna cikin tattara kwanuka Zainab ta shigo cikin gurin tana wani ɗaga kai sama, kallon Suhailan tayi a wulaƙance tace; ” Ke!”.

Suhaila kuwa taji ta Sarai amma taƙi juyowa ta kalle ta.

Matsawa tayi kusa da Suhaila, hannun ta tasa ta juyo da Suhaila ta zabga mata mari a kuncin ta.

Suhaila kuwa jin saukar marin ba tare da ta shirya ba yasa ta dafe kuncin ta, wani baƙin ciki na ratsa zuciyar ta, wai yau ita wannan abar zata mara, ƙanwarta, ko Kausar bata mare ta ba ballantana kuma ita.

Kausar ce ta ajiye plate ɗin da yake hannun ta tayo kan Zainab ɗin tana shirin kwashe ta da mari, amma Suhaila tayi saurin riƙe hannun tana girgiza mata kai, wasu hawayen baƙin ciki ne suka zubo mata, yayin da Kausar take cika tana batsewa.

Zainab ce ta wani yi fari da ido tace; ” Har ni zan miki magana ki wani share ni? Kin ga nayi miki kama da wanda zaki wulaƙan ta? Sakariya wawiya kawai”.

Da gudu Suhaila ta fita daga kitchen ɗin don baza ta iya tsayawa tana cigaba da jin maganganun da take faɗa mata ba.

Ta Ƙofar baya ta fita daga cikin gidan, garden ta nufa direct, guri ta samu ta zauna tana sakin kuka me cin zuciya, ba komai zata jure, duk Ammin ta ce ta ja mata.

A ɓangaren Kausar kuwa harara ta gallawa Zainab kafin tace; “Wannan shine na ƙarshe da zaki ɗaga hannu ki daki Suhaila idan ba haka ba wallahi da kanki zaki tattara kayan ki ki bar gidan nan na faɗa miki”.

Cikin fushi Kausar ta bar kitchen ɗin, itakuwa Zainab ranta fari ƙal.

Jibril da ya fito daga part ɗin su zai shiga cikin gida ya hango ta ta fito ta ƙofar baya daga kitchen, bayan ta yabi ganin tana kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button