ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Yana isa cikin garden ɗin ya hango ta sai zubar da hawaye take.
Da sauri ya ƙarasa inda take ya nemi guri ya zauna, ita kuwa ta haɗa kai da gwiwa sai sharɓar kuka take, bata san yazo gurin ba sai da ya kira sunan ta.
“Suhaila, lafiya kika zo nan kina kuka haka? Me ya faru wa ya taɓa mun ke?
Ɗagowa tayi tana kallon shi da jiƙaƙƙun idanun ta, bata ce mai komai ba ta tashi zata bar gurin,kamo hanun ta yayi ya dawo da ita, be wani tsaya ɓata lokaci ba ya rungume ta tsam a jikin shi yana jin zuciyar shi kamar zata faɗo ƙasa don baya son ganin hawayen ta ko kaɗan.
Ƙamshin turaren shi da kuma yanayin da take ciki yasa tayi lamo a jikin shi tana cigaba da kuka kamar ranta zai fita, a hankalin ya fara shafa bayan ta yana lallashin ta, cikin minute kaɗan ta fara sauke ajiyar zuciya.
Sun kai kusan 10 minute sannan ta fara ƙoƙarin barin jikin shi da hankalin ta ya dawo jikin ta.
Ba musu ya sake ta, ɗan kallon shi tayi, shi kuwa kasa jurewa yayi, ya sa hannun shi duka biyu yana tallabo kumatun ta, haɗe da share mata ragowar hawayen dake saman kuncin ta. A hankali cikin whisper yace”I love you”.
Matso da fuskar shi ya fara yi kusa da tata, ganin yana ƙoƙarin kissing nata yasa tayi saurin barin jikin shi gaba ɗaya tana juya mai baya.
Ɗan lumshe ido yayi yana tunanin me yake shirin aikatawa.
“Am sorry”. Ya furta yana kallon bayan ta.
“Am sorry too” ta faɗa tana barin gurin cikin sauri, haɗe da dana sanin fitowa da tayi, me yake shirin faruwa da ita? Me ta aikata yanzu. Istigifari ta fara maimaitawa a cikin zuciyar ta, wani baƙin ciki yana kama ta, ya zama dole tayi avoiding nashi idan ba haka ba wani abun zai iya faruwa, don mutum ya kan aikata abunda be sani ba ga wanda yake so, kuma yakan iya bashi dama saboda soyyayar dake tsakanin su.
_To ƴan mata, sai muna kiyayewa fa, kar ki bari saurayi ya ɗauke ki ku fita yawan shaƙatawa ya kai ki gurin da daga ke sai shi, to wallahi na ukun ku shaiɗan ne, kuma komai zai iya faruwa tunda ku ba sahabbai bane, kuma ba duwatso ba, zaki iya bashi damar ya rungume ki, ko kuma yayi kissing naki koda wani abun bayan haka be faru ba, saboda soyyayar da take tsakanin ku, ke a ganin ki ai yana son ki kuma kema kina son shi, idan Suhaila ta iya controlling kanta tofa ba lallai ke ki iya ba… Tom take note please, don’t allow him get close to you oooo ƴar uwa, because idan wani abun ya faru you will regret it ko da kuwa auren ki zai yi_..
Cikin sauri ta ƙarasa cikin gidan, inda shi kuma ya rufe fuskar shi da tafin hannun shi yana faɗin”Oh nooo shikenan zata ƙara ƙin yarda da ni, me na aikata?”
Tana shiga cikin gida ta wuce ɗakin Kausar, Kausar kuwa da ta biyo bayan Suhaila bayan ta bar Zainab a ciki, tana zuwa ta gansu ya rungume ta sum sum ta koma cikin gida ba tare da ta bari wani a cikin su ya ganta ba.
Tana shiga Kausar tace; ” Masha Allah, irin wannan love haka”.
Saurin kallon ta Suhaila tayi tana zaro ido alamar mamaki tace; ” Dama kin gan mu, ya subahanallahi, wallahi ban san yadda hakan ta faru ba kar kiyi tunanin wani abun please”.
Dariya Kaysar tayi tana kallon Suhailan haɗe da nuna ta da hannu”Ohhhh ji idon ta, wato har kin ji tsoro, oooo ta ya Jibril, Allah ya barku tare”.
Pillows Suhaila ta ɗakko ta fara bin ta da shi tana dukan ta amma duk da haka bata bar faɗin ta ya Jibril ba, ganin zata jigata yasa ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi.
“Hhhh! ya isa haka Kausar nayi giving up amma babu abunda yake tsakani na da ɗan uwan ki”.
“Uhmmm, story, story”.
Ta buɗe baki zata ƙara magana Hajiya Kulthum ta turo ƙofar ɗakin.
Kausar ce tayi saurin dira daga kan gadon tana faɗin “Hajiya kinji abunda yake faruwa kuw…..
Bata ƙarasa ba Hajiya Kulthum ta ɗaga mata hannu tana mata nuni da ƙofa.
Kallon ta ta tsaya yi da mamaki don kafin Ummin nasu tayi behaving haka ana daɗewa.
Fita Kausar tayi a ɗakin.
Hannun Suhaila ta kama suka zauna a bakin gado, kallon ta tayi tace”Kar ki mun ƙarya kuma karki ɓoye mun komai, me ya faru tsakanin da Jibril jiya da daddare? ”
Suhaila kuwa ji tayi gaban ta ya faɗi, kar dai ace Ummi taga duk abunda ya faru jiya.
Shiru tayi tana ɗan sunkuyar da kanta.
” Hajiya ba komai”.
“Ƙarya ne, har yace miki i love you”.
Ɗan lumshe idon ta Suhaila tayi tana buɗe su a hankali.
_”Ya Allah”_ta furta can ƙasan maƙoshin ta.
Numfashi ta sauke sannan ta fara faɗawa Ummi duk abunda yake tsakanin su, nan da nan taji zuciyar ta ta karaya, amma duk da haka ai shima ɗan ta ne babu komai.
Cikin sanyi jiki tace; “Amma dai kema kina son shi ko?”
Sunkuyar da kai Suhaila tayi tana wasa da yatsun ta, alamun kunya.
“Ba komai, abunda nake so nace miki shine kuma nasan kin sani amma tunatar da ke zan yi, kar ki sake ki bawa ko wani namiji damar taɓa ki ko ya ya ne, kinji ko?”
Gyaɗa kai Suhaila tayi ita kuma Ummi ta bar ɗakin.
Hankalin Ummi ya tashi matuƙa gashi ba yadda ta iya, babu komai duk ɗaya ne, haka ta koma ɗaki zuciyar ta tana mata ciwo, sosai.
****
Bayan sallar magrib Jibril ya shigo ɗakin Kausar don bata haƙuri.
Ganin shi yasa Kausar tayi saurin barin ɗakin. Tana fita ya ɗan matsa kusa da ita yace; “Kiyi haƙuri please ba da son rai na hakan ta faru ba”.
Ɗan murmushi tayi har sai da fafaren haƙoran ta suka bayyana, “Ba komai, ya wuce”.
Dariya yayi yana jin daɗi a cikin zuciyar shi, hira suka ɗan taɓa.
Bayan ya Fito daga ɗakin Kausar ta tsare shi a hanyar sauka ƙasa tace; ” Uhmmm yau ranar biyan bashi ce”.
“Wani bashi kenan Kausar?”
“Na alƙawarin da ka mun mana.
Nannaɗe hanun shi yayi a ƙirjin shi, yana ɗan jingina da bango yace; “Ohhh, ohhh na tuna tabbas, inajin ki me kike da buƙata?”
“Ya Ahmad zai zo birthday ɗi na”.
Ɗan zaro ido yayi yana kallon ta yace; “Shi ya Ahmad ɗin ne yace miki zai zo da kan shi”.
Gyaɗa mai kai tayi ta cigaba da magana, “So, abunda nake so shine, kayi convincing Daddy idan yazo please kar ya kore shi, baifi yayi sati ɗaya ba ya tafi”.
Ɗan kallon ta yayi yana shafa gemun shi sannan yace; “Kai Kausar, amma dai kin san da ƙyar idan zan iya cika miki wannan alƙawarin ko, idan Dadday be yarda ba ya kike so nayi kuma, gashi kin sa na miki alƙawari ummm?”
“Haba ya Jibril wallahi sai dai idan ba kayi mai magana ba, amma nasan indai kaine zai yadda, ni kuma zan sanar da ya Ahmad yayi avoiding haɗuwa da shi ko da yaushe”.
Ɗan sauke ajiyar zuciya yayi yace; “To shikenan zanyi trying muji mai zai ce”.
Rungune shi tana faɗin” yaya na, amma naji daɗi sosai wallahi”.
Da saurin ta ta bar jikin stairs ɗin tana shigewa ɗaki.
Shi kuwa Jibril har kishi yake da Ahmad shima yana jin dama ace Kausar da Ummi suna mai irin son da sukewa ya Ahmad, ba matsala nima Daddy yafi so na akan kowa.
Bayan wata biyar.
Abubuwa sun faru da yawa, inda Suhaila da Jibril shaƙuwa ta shiga tsakanin su me ƙarfin gaske, don soyyayar su suke yi sosai, da ya dawo daga gurin aiki to yana tare da ita, ita kuwa Kausar kullum cikin tsokanar su take.
Suhaila na hango zaune a cikin garden ta sha wata abaya me shegen kyau army green inda ta saka hijab half sunna light green me irin kwalliyar nan a jikin shi.
Waya ce a kunnen ta naji tana faɗin”Oya Mubarak bawa Abbu wayar “.
” Aaaa ya Suhaila please mana ki bari mu ƙarasa gaisawa yaushe rabo na da ke?”