HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Mubarak, yau kaida Farida kun cinye credit ɗin ko magana da Abbu ba muyi ba”.

Ɗan cire wayar yayi a kunnen shi yace; “Just 3 minutes shine muka cinye kuɗin?”.

“Uwaka, an faɗa maka kiran Nigeria da nan ɗaya ne”.

Abba ne ya ƙwace wayar yace ; “Mama na karki damu, kinji ko ai naji muryar ki, munyi magana wani lokacin ki kula da kanki kin ji ko”.

To ta amsa mai da shi tana kashe wayar.

Ganin tana ƴan canji yasa ta kira Surayya.

Da sauri Surayya ta ɗaga tana faɗin”Mutanen London, how far ne? ”

” Wallahi fine oooo, dama cewa nayi bari na kira ki naji murya….

Bata ƙarasa faɗan abunda zata faɗa ba taji an warce wayar a hanun ta.

Kausar bata ɓata lokaci ba tace; “Haba mana, ina can ina ta neman ki za a siyi kaya amma kina nan kina making calls, oya tashi muje, mayan ki ma yana can yana neman ki”.

Dariya Suhaila tayi tana miƙewa”Amma wallahi kin raina ni Kausar har da kunne na kika haɗa fa”.

“Allah ko, ai gwara haka ma. Kallon ta Kausar tayi tace ; ” Gaskiya ban gane wannan wankan naki ba, ai kin kusa fina kyau, anya nima ba wankan abayar nan zan yi ba”.

“Da ko kinfi kyau”.

Shiga cikin gidan suka yi Kausar ta bata list ɗin abunda zata siyo mata, driver ne ya ɗauke ta ya kai ta wani ƙatoton mall.

Shiga tayi ta fara siyan abubuwan da take buƙata, su balloons ne crown ne, sweet, short cakes, da manya manya drinks non alcoholic da dai sauran kayan ƙwalamashe.

 

Wata haɗaɗɗiyar motace one door tayi parking a bakin mall ɗin, sai da ya ɗau ƴan mintuna yana tunanin me zai siya mata yasa ta farin ciki sosai.

A hankali ya buɗe murfin motar, ƙafar shi ce guda ɗaya ta fara fitowa sannan ya fito da ɗayar kafin gangar jikin ta fito baki ɗaya.

Sanya yake cikin wando me shegen kyaun gaske blue in color sai farar riga me dogon hannu sai kuma falmaran da ya ɗora akan farar rigar itama blue, wuyan shi ya naɗe da white mofula, hannun shi kuma wani agogo ne me shegen kyau daga gani ma ba wai normal agogo bane, ƙafafun shi kuma cikin wani baƙin cover shoe suke me shegen kyau, fuskar shi na kalla, naga ya bar wani saje haɗe da gemu wanda yayi mugun yi mai kyau gashi yasha gyara har wani kwanciya yayi, sai dai kanshi kuma babu gashi sai ɗan kaɗan da ya fara fitowa, shima kuma ba gashi bane alamar yayi aski ne kan ya fara yin baƙi alamar wani gashin yana shirin fitowa.

A hankali ya fara takawa zuwa cikin mall ɗin yayin da duk inda ya wuce sai ya bar ƙamshin turaren shi, hannun shi cikin aljihunan wandon shi ya shige cikin mall ɗin.

Dube-dube ya fara yi amma ya rasa me zai ɗaukar mata.
Suhaila kuwa da ta gama siyyayar ta tana ƙoƙarin zuwa wajen biyan kuɗi tazo ta wuce shi a gurin wasu teddies sai tunanin me zai ɗaukar mata yake.

Tana wucewa shi kuma yana juyowa ɗan kallon ta yayi sosai, cikin sauri ya ƙarasa yana shiga gaban ta, haɗe da cewa”Assslama alaikum, muslim sister ko? Kuma kamar Nigerian? ”

Ɗan kallon shi tayi from head to toe yayi kyau sosai, shiru tayi bata ce komai ba.

Cire glasses ɗin da yake idon shi yayi yana ƙara kallon ta, har ta sauke idon ta tayi saurin maidasu tana ƙare mai kallo sai taga yayi mata kama da wanda Kausar take kiran shi da ya Ahmad.

Ɗaga mata gira yayi yace; “Uhmmm kin sanni ne?”

Girgiza mai kai tayi tana faɗin”Zan iya tafiya sauri nake yi ?”

“Am sorry please, naga kamar kin siyi birthday things ne, sister na za tayi birthday yau kuma, na rasa me zan bata can you help me please?”

Ɗan murmushi tayi tana daɗa tabbatar da shine. Gyaɗa mai kai tayi tace”Me tafi so? ”

” Ummm tau before na san, tana son teddies, Chocolate, boga, pizza, glaze doughnuts, sai mai kuma, uhmm perfumes, abayas and na manta gaskiya”.

Dariya tayi tana girgirza kai jin duk abunda Kausar take so ya lissafa, a cikin zuciyar ra tace”And tsokana ba”.

“To yanzu dai baza mu sai mata teddy ba, tunda yanzu may be ta dena amfani da su”.

“Kuma fa haka ne kin kawo idea me kyau”.

Gurin turare suka nufa shi kuma ya karɓi kayan yana tura mata gashi ya cika ta da surutu, ɗan kallon shi tayi cikin zuciyar tace”Kai wannan har yafi Jibril surutu ma, duk halin su ɗaya daga gani shima zai yi tsokana”.

Suna zuwa gurin perfumes ta ɗakko wanda taji Kausar tace tana son siya, ɓangaren abayas suka je ta zaɓar mata me shegen kyau dama ɗazu taji tace ko itama tayi wankan abayar ne.

Chocolate har sai da tace mai ya isa haka.

Suna gamawa ta karɓi kayan ta tace; “Asha birthday lafiya, bye”.

Kafin yayi magana har ta bar gurin kallon bayan ta yayi a hankali yace; “Thank you, ai ko godiya kin tsaya na miki”.

Kafin ya zagayo har ta ƙarasa gurin payment bata daɗe ba ta bar gurin.
Tana isa aka fara decorating gurin inda Kausar take cikin annashuwa, saboda yau zata ga yayan ta.

Bata daɗe da isa ba motar Ahmad tayi horn, buɗe mai aka yi ya shiga.

Ya kusa 20 minutes a cikin motar ya kasa fitowa, wani nannauyan numfashi ya sauke yana fitowa daga cikin motar kallon gidan ya fara yi a hankali, yana jin daɗi sosai wai yau shine a gidan su.

A hankali ya fara takawa gaban shi na mugun faɗuwa.

Dai dai ƙofar libraryn shi ya tsaya. Password ɗin ya danna, nan yaga ƙofar ta buɗe, ɗan murmushi yayi yace; yace for all these years baki canza ba Kausar”.

Shiga gurin yayi yana kallon komai tsaftsaf ƙarasawa yayi cikin libraryn shima komai cikin nutsuwar shi yake.

Wani abu ne ya faɗo mai saurin kiran Kausar yayi yace ta tura mai picture nata yanzu.

Ɗaukan kan ta tayi ta tura mai, gurin zanen shi ya dawo ko zai samu pens ɗin sa na zane, yana dubawa kuwa yaga akwai.

Rigar da yake ɗaurawa idan zai yi zane ya ɗora nan ya fara zana hoton da ta tura mai, cikin 3 hours ya kammala.
Kowa yaga mota a parking space amma an rasa ta waye, Zainab ce ta tambayi me gadi ko yasan wanda ya shigo, nuni yayi mata da libraryn yace mata ya ganshi dai ya shiga cikin gurin nan.

 

Ta san dai Jibril ba ya shiga to ko ya Ahmad ne yazo.

Da gudu taje gurin amma ta tsaya cak don baza ta iya tuna password nashi ba ko za a kashe ta.

Tunawa tayi da ɗakin shi, ai kuwa da gudu tayi part ɗin su tana tura ƙofar ɗakin shi, komai na ɗakin a rufe yake da farin ƙyalle, jikin wani shelf ɗin littafan shi taje ta danna wani pin nan wooden door ɗin ta buɗe. Shiga libraryn tayi ta buɗe ƙofar da zata sada ta da gurin zanen shi, tana buɗewa kuwa ta hango shi yana ƙara goge zanen don ya fito da kyau.

 

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar ta, tace; “Ya Ahmad!!”…….

*****

*_Ni Fatima ina son ganin Abunda zai faru a bithday ɗin nan_*..

_*Ma’asalam, Faɗma Ahmad*_✍????
[7/9, 7:32 AM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*Page4️⃣2️⃣to4️⃣3️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

 

*Daga Cikin Addu’o’in rokon Ruwa*

اَللَّهُمَّ اسْقِنَا غَيْثاً مُغِيثاً مَرِيئاً مُرِيعاً، نَافِعاً غَيْرَ ضَارٍ، عَاجِلاً غَيْرَ آجِل.
Allahummas-qina ghaythan mugheethan maree-an muree’an, nafi’an, ghayra dar, ‘ajilan ghayra ajil.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button