ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama mai yaye tsanani, mai dadi, mai ni’ima, mai amfani ba mai cutarwa ba, da gagugawa ba da jinkiri ba.
اَللَّهُمَّ أغِثْنَا، اَللَّهُمَّ أغِثْنَا، اَللَّهُمَّ أغِثْنَا.
Allahumma aghithna, allahumma aghithna, allahumma aghithna.
Ya Allah! Ka yi mana agaji (da rowan sama) Ya Allah! Ka yi mana agaji. Ya Allah! Ka yi mana gaji.
اَللَّهُمَّ اسْقِ عِبَادَكَ وَبَهَائِمَكَ، وَانْشُرْ رَحْمَتَكَ وَأَحْيِي بَلَدَكَ المَيِّتِ.
Allahummas-ki ‘ibadak, wabaha-imak, wanshur rahmatak, wa-ahyi baladakal-mayyit.
Ya Allah! Ka shayar da bayinka, da dabbobinka; kuma ka yada rahamarka, Ka rayar da kekasasshiyar kasarka.
*_The sorrowful birthday…_*????
Da gudu ta ƙarasa kusa da shi tana shafa fuskar shi zuwa jikin shi, yayin da take kukan farin ciki, shi kuwa tsayawa yayi yana kallon ikon Allah rungume shi tayi tsam a jikin ta tana jin wani farin ciki mara misaltuwa.
A hankali ta furta “I really miss you baby na, nayi missing ɗin ka sosai ya Ahmad, ka azabtar da ni ka hana ni ganin ka, ka hanani jin muryar ka, wallahi gidan nan kamar prison yake idan babu kai”.
Ɗan ɗagota yayi a hankali yana kallon fuskar ta nan da nan abubuwan da suka faru a baya suka fara dawo mai, kafaɗar ta ya dafa yana cire ta daga jikin gaba ɗaya ya Maidata gefe.
Kallon shi tayi idon ta duk sun ciko da ƙwalla tace; “Please ya Ahmad na roƙe ka da manta da abunda ya faru a baya wallahi ba lefi na bane lefin Umma ne don Allah”.
Ta ƙarashe maganar tana riƙe hannun shi guda ɗaya.
Murmushi yayi yana cire hannun ta cikin nashi yace; “Zainab stay away from me don Allah, idan da kin san yadda na tsanake yanzu wallahi da ko kusa da ni baza ki zo ba, na riga da na gama da babin ki, meye ban miki ba Zainab wani irin so ne ban nuna miki, amma daga baya aka haɗa baki da ke aka ci mun mutunci, to a baya ma da baki kai kin kawo ba kinyi wannan makirincin ballantana yanzu da kika zama cikkakiyar budurwa”.
“Wallahi ya Ahmad ba haka bane, duk da a lokacin ban san so ba amma wallahi gudun kar na rasa ka yasa nayi hakan don ka yafe mun, don girman Allah ya Ahmad wallahi idan ka guje ni mutuwa zanyi”.
Matsar da ita gefe yayi yace; “If you like go to hell, non of my business”.
Fita yayi ya barta a gurin tana sakin kuka mai cin zuciya, ta rasa yadda za tayiwa Ahmad wani irin abu ne be gani ba,anya kuwa zai yarda da ita, duk wainnan abubuwan da suke faruwa be yi giving up ba ballantana kuma maganganun ta, share hawayen ta tayi tace; “Wallahi ko kana so ku baka so sai ka aure ni ya Ahmad, nice matar ka”.
Ahmad yana fita daga gurin ya wuce mota ya ɗakko abubuwan da ya siyo, ta ƙofar baya ya shiga cikin gidan ta inda ba wanda zai gan shi a hankali ya wuce stairs yana shiga ɗakin Ummin shi.
Ummi kuwa tana gaban dressing mirror ta gama kwalliya tana saka ɗan kunne taji shiguwar shi, a hankali ya salallaɓo ya rungume ta ta baya.
Saurin firgita tayi don bata zata shi bane, amma tana kallon cikin modobi taga ɗan nata da ya shekara kusan biyar ba ta ganshi ba.
Ajiye ɗayan ɗan kunnen da bata riga ta sa shi ba tayi.
Yunƙuri tayi tana tashi daga kan kujerar, bata wani ɓata lokaci ba ta rungume shi tana fasa kuka me cin zuciya, shima kukan yasa yana rungume ta tsam a jikin shi.
Sun kai kusan 10 minutes suna kuka, sai shi ne ya samu ya bar jikin ta yana share mata hawayen ta, a hankali yace; “Ummi na kukan ya isa haka ba gashi na zo ba, nine dai Ahmad ba wani ba”.
Ɗan dukan shi tayi tace; “Nayi fushi da kai, nayi fushi da kai”.
Ƙara rungume ta yayi yana share hawayen fuskar shi yace; “Na san Ummi na baza ta taɓa fushi da ni ba, kiyi haƙuri ki yafe ni, nayi hakan ne saboda kwanciyar hankalin ki da kowa ma Ummi na”.
“Kalle ka fa, ji yadda ka koma, ka wani girma duk ka canza ka zama kamar americans ɗin nan”.
“Aaaa Ummi na, a hakan ai nayi ƙoƙarin yin dressing me kyau fa”.
Dariya tayi tace; “Ji har hausan ka duk ya canza ya koma na gwari”.
Dariya yayi sosai yana kama hannun ta”Ummi na nayi missing ɗin ki sosai wallahi”.
“Nima nayi kewar ka ɗana. Amma ba da wuri zaka koma ba ko?”
Dari yayi yana ɗakko ɗayan ɗan kunnen da ta ajiye, ya kama kunnen ta zai saka mata yace; “Har kin manta taurin kan mijin ki kenan”.
Smacking kanshi tayi tace; “Gidan ku Ahmad, wato miji na ko?”
Auchhh ya faɗa yana sosa gurin”Ummi na da zafi fa, mijin ki mana”.
Zaunar da shi tayi a bakin gado itama ta zauna tana kama hannun shi tace; “Duk abunda zai faru sai dai ya faru kam wannan karan amma baza ka sake yin nesa da ni ba haka, saboda ban san abunda kake aikawata ba a can ba, wannan spoiled country ɗin ace a can kake zaune, kuma ma wani new yolk”.
“Ummi na, am fine am good baki gani bane”.
“Na gani mana amma nasan wani irin ɗabi’a ka koyo mana a can, nan ma ana fama ballantana kuma can”.
Ɗan lumshe ido yayi yana rungume ta haɗe ta tunanin idan Ummin shi tasan halin da ya shiga a garin bai san yadda za tayi ba.
“Ba komai Ummi na”. Ya faɗa yana ɗakko abubuwan da ya shigo da su, kayan ya fara buɗewa yace; “Time ya tafi fa, ki kaiwa Kausar wannan ta sashi, amma kar ki ce mata na riga da nazo saboda akwai surprise da na tanadar mata.kafin ki dawo zan fara haɗa gift ɗin”.
Ummi karɓan rigar tayi tana shiga ɗakin su Kausar inda ta tarar da Jibril sai zuba yake musu, kallon shi tayi tana girgiza kai tace; “To na mata na mata sai ka bamu guri ko, kai ko kunya baka ji, oya fita ka bamu guri”.
Dariya yayi yana sosa ƙeya yace; ” Da giraman kujerar Ummi na tafi”.
Dungure mai kayi tayi cikin wasa tace; “Allah yasa kuma na ƙara ganin ƙafar ka, mara ta ido kawai”.
Da gudu ya fita yana dariya.
Rigar ta miƙawa Kausar, karɓa tayi tana buɗewa wani tsalle tayi tana ƙara duba rigar”Kai Ummi, wannan fa? Masha Allah gaskiya ta haɗu iya haɗuwa”.
Kallon Suhaila tayi tana mata gwalo haɗe da dariya”Sai na fita kyau, sai na fita kyau”.
“Uhmm” kawai Suhaila tace, cikin zuciyar ta kuwa cewa tayi; “Baki san ma ni na zaɓo rigar ba”.
Dariya Ummi tayi tana faɗin”Rabu da ita duk da haka baza ta kamo ki kyau ba”.
” Na sani Ummi, sai ta san sirrin rigar ma tukunna”.
Kallon ta Ummi tayi tana juya maganar a ranta “Sirrin rigar kuma”.
Basarwa tayi tana faɗin” Kuyi ku shirya, kunga yanzu fa har 8:30 kuma bana so mutane suyi dare sosai a gidan nan.
To suka amsa mata da shi inda Kausar ta saka rigar tana zama a gaban dressing mirror don tsantsara kwalliya.
Wata red abaya me shegen kyau Suhaila ta ɗakko ta saka tayi rolling da white veil, tayi kyau sosai kuma bata shafa komai a fuskar ta ba sai natura beauty ɗin ta.
Kafin su sakko har an haɗa gurin an kawo cake kusan kala bakwai an jire su a gurin.
Wani ƙato aka shigo da shi daga baya sai dai a rufe yake, a gefe guda aka ajiye shi.
Cikin 30 minutes kowa ya hallar a gurin inda Jibril yasa red suit sai farar riga daga ciki yayi kyau sosai su kayi matching da Suhaila.
Tun da aka sakko ake gaisawa da mutane ana ɗan shan drinks sama-sama, inda Kausar take ta trying number Ahmad amma yaƙi shiga.
Zainab na hango taci wata black and white riga ta haɗu iya haɗuwa kai baka ce ita bace ta saka wani uban takalmi me Tudun gaske tayiwa gashin ta wani style me kyaun gaske ta ɗan sa wani net akanta inda duk rabin gashin ana ganin sa.