HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Guri guda ta samu ta tsaya tana jiran shi ya shigo.

Kausar kuwa gurin Ummi taje ta saka mata kuka tana faɗin baza ta yanka cake ba tunda Ahmad be zo ba.

Lallashin ta tayi tace; “Haba mana kiyi haƙuri zai zo Kausar, kin san dai indai har ya miki alƙawari babu abunda zai hana shi zuwa”.

Guge hawayen tayi tana gyaɗa kai.

Tana kusa da Ummin ta hasken gurin ya ɗauke gaba ɗaya. Babu abunda kake gani sai duhu, wuta ce ta kawo dai-dai inda wani yake turo cake zuwa cikin gurin, kowa tsayawa yayi yana kallon shi don cake ɗin ya rufe fuskar shi gaba ɗaya.

Yana ƙarasowa ya tsaya, ɗan hannun shi yasa yana zame farin ƙyallen da yake jikin shi, hoton Kausar da Ahmad ya zana ne ya bayyana, daga gefe kuma ga wani cake me shegen kyaun gaske, kusan hawa huɗu, an rubata happy birthday my little princess@ 25…..

Wani ƙayataccen murmushi Kasausar ta saki don ta san idan ba ya Ahmad ɗin ta babu me shirya mata wannan abun.

Ɗan fitowa yayi, nan take kuma aka saki wani music me shegen daɗi na happy birthday, ware mata hannu yayi, a lokaci guda kuma wutar gurin ta dawo.

Sanye yake cikin black suit sai rigar ciki fara yayi kyau sosai, Zainab ce ta saki wani ƙayataccen murmushi, ganin iri ɗaya suka saka dama ta san be wuce ya saka black suit ba don yana son su.

Da gudu Kausar taje ta rungume shi tana sakin kukan farin ciki, nan da nan gurin ya ɗau tafi, ɗan ɗago ta yayi yana faɗin “Happy birthday my princess, an girma ko”.

Ɗan tunɓuro baki tayi tace; “Thank you ya Ahmad”.

“You are welcome my princess”.

Nan fa guri ya ƙara kacemawa inda Zainab taje ta wani ƙaƙame shi tana saƙala hannun ta cikin nashi.

Shi kuwa yana cikin farin ciki ko kula ta be yi ba.

Jibril ne yaje gurin Ahmad, Ahmad na ganin shi kuwa ya rungume shi tsam a jikin yana faɗin “I miss bro”.

“I miss you too, welcome home big bro” Jibril ya faɗa yana sakin wani murmushi.

Ahmad yaji daɗin ganin familyn shi sosai, dama ace ya dawo kenen su cigaba daga inda suka tsaya.

Cake aka yanka, inda Kausar ta bawa ya Ahmad a baki shima ya bata, sannan Ummi, shi kuwa Jibril ja gefe yayi sai da Ahmad ya janyo shi yana faɗin”Ya kake yin gefe ne, lakuto cream yayi yana shafa mai a fuska, dariya Jibril yayi yana yanko cake me girman gaske ya cusa mai a baki.

Haɗa Ido yayi da Suhaila da take gefe, yana mata nuni da ta zo amma ta girgiza kai tana maƙe kafaɗa, Kausar ce itama ta gano ta tana ƙwalla mata kira.

“Besty!!!!!”ta faɗa tana yafito mata hannu, har ta ɗaga ƙafa zata isa gurin da mutane suka yi cincirindo ana ta karbar gift, Alhaji Umar me shadda ya shigo yana faɗin.

” Am sorry my little daughter i am late”.

Ɗan tunɓora baki tayi tana rungume daddyn nata.

Rungume ta shima yayi, amma sai dai me ji tayi ya wani fincike ta a jikin shi.

Alhaji Umar na kalla naga idon shi ya kaɗa yayi ja, duk jiyoyin jikin shi sun tashi, yayin da jikin shi ya soma kirma saboda tsabar jaraba.

Ahmad ya nuna da hannu yana faɗin”Uban me ya kawo ka gida na! ? Me kazo yi la’ananne ɗan iskan gari?”

Ƙaraswa yayi yana kwashe shi da mari, wani punch ya ƙara kai mai, da gudu Zainab ta ƙarasa tana faɗin” Daddy please stop it, ka rabu da shi don Allah”.

Jefar da ita gefe yayi, yana ɗaukan wani gift dake gurin ya kwaɗa mai a kan shi, shi kuwa Ahmad ko motsawa be yi ba sai durƙusawa da yayi, Daddyn nasu na ta dukan shi.

Jibril yayi wani shu’umin murmushi sannan ya fara sallamar mutanen da suke gurin, Suhaila kam tun kafin ya ganta ta fice a gurin tana tsayawa a jikin ƙofar palon. Haɗe da durƙusawa tana sakin kuka, so suma suna da family issue kenan.

Kausar ce taje ta tare Ahmad inda dukan ƙarshe ya sauka a jikin ta.

Faɗuwa tayi, nan da nan Ahmad ya ɗago yana kallon ta, saurin tashi yayi yace; “Enough! Am here because of her and am leaving now, so stop this madness please”. ya faɗa ƙwalla na taruwa a idon shi.

“Get him out of my house now!”.

“Ba sai an fita da ni ba zan fita da kai na”.

“Better” Alhaji Umar ya faɗa,”Ka isa kazo gida na babu izini na”.

Kausar ce tayi saurin ɗakowa tana kallon Jibril alamar tambaya, cikin zuciyar tace”Me yasa ya Jibril yace mun Daddy ya yarda bayan ba haka bane”.

Barin jikin Ahmad tayi da yake riƙe da ita, ta ƙarasa kusa da Jibril, tana zuwa ta ɗauke shi da mari.

“How dare you!, me yasa zaka mun ƙarya? Me yasa ya Jibril, why!?

Riƙe kuncin shi yayi bece komai ba sai dariya da yayi mata, Daddy ne ya ƙaraso gurin itama ya ɗauke ta da mari.

Cikin kuka Ummi tace; ” Ya isa!dukkan ku ya ishe ku haka na faɗa muku! Meye hakan kuke yi? Me kuke so ku mayar da gidan nan ne? Gidan ƙiyayya?”

Zainab ce ta ƙarasa kusa da Ahmad tace ; “Ka yarda muyi aure, ka san muna yin aure komai zai dawo dai-dai, duk abubuwan nan za su dena faruwa, don Allah ya Ahmad kayi saving family ɗin nan ka aure ni”.

“Never! Indai Sai na aure ki to wallahi baza a taɓa dawowa dai-dai ba na riga da na gama dake Zainab”.

“Then leave my house” Alhaji Umar ya faɗa”.

“Am leaving, now”.

Hanyar waje ya fara nufa, Kausar ce ta miƙe tace; “Am leaving too, indai har ya Ahmad ta tafi we are going together”.

“Go to hell dukkan ku, ban damu ba, ku tafi ina da Jibril da Aisha ai, ku tafi”.

Ummi ce tace; “Indai har za su tafi sai dai mu tafi tare tunda ka riga da ka raba mana kan yaran mu, wai Umar me yake damun ka ne han, me yake damun ka?.

Da sauri Suhaila ta bar gurin tana wucewa library don baza ta iya ƙarasa jin wainnan abubuwan ba, ashe ita nata nafula ne ma.

Alhaji Umar ne yace”Jibril, next week zamu tafi Germany, kai kuma kar ka bari na sake ganin fuskar ka har na tafi, sannan kuma kafin na dawo kun gama good time ɗin ku don bazan yi kaffarar zama da kai waje ɗaya da nace bazan ƙara yi ba inda baka yi abunda nace ba”.

Fuuu ya bar gurin yana wucewa ɗakin shi, Jibril ma part ɗin su ya wuce, ita kuma Zainab ta matso kusa da shi ganin kan shi yana ɗan jini, hannu ya ɗaga mata, nan tayi baya bata ma ƙaraso ba..

Ummi bata ƙara magana ba itama ta wuce ɗaki, Kausar ce ta rungume Ahmad tana rarrashin shi, kama hannun ta yayi ya kaita ɗaki yace” kiyi sallah ki kwanta”.

“Am off” ta faɗa kanta tsaye”.

Kwantar da ita yayi yana ja mata blanket yace; “Kiyi Bacci yanzu, anjima idan kin tashi kin yi wanka ki canza kaya ko”.

Gyaɗa mai kai tayi tace; “Kan ka, kayi treating nashi please”.

Murmushi yayi mata yace”I will dear”.

Fita yayi a ɗakin, be ci burki a ko ina ba sai ɗakin shi, an gyara mai shi ba kamar yadda yazo ba.

Depression ɗin shi ne yaji yana so ya tashi, ya rasa me zai yi.

Ɗan gwangwanin shi ya ɗakko ya kaɗa shi yaga abunda yake ciki ba shi da yawa.

Danna pin yayi ya shige cikin library, Suhaila tana zaune bayan wani Shelf sai kuka take yi taji shigowar mutum, ɗan leƙowa tayi tana kallon shi, cikin ranta tace dama bayan wannan gurin akwai ƙofa.
Wucewa yayi yana jin zuciyar shi na mai zafi, ɗakin zanunkan shi ya shige, inda yake bi yana kallon hotanan ɗaya bayan ɗaya, duk wanda yaga da Zainab a jiki sai yayi wurgi da shi, haka yayiwa gurin kacaca, daga ƙarshe ya ɗaga alcohol ɗin dake hannun shi ya shanye, yana cilli da abun, dama ba wani yawan arzƙi gare ta ba, a dai-dai lokacin Suhaila ta leƙo.

Zaro idanu tayi tace; “Ohhh no, giya yake sha, wani hawaye ne ya wanke mata fuska, wannan mutumin yana shan giya, innallilahi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button