HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Cikin zuciyar ta take faɗin”May be situation ɗin nan yasa shi shan giyar dama mutanen garin nan ya aka ƙare”.

Ƙatse mata tunani yayi, da ya daki wani dogon wooden ladder(tsani) irin wanda ake hawa a ɗakko abubuwa na cikin gida.

Ga kaya a kan shi, nan ya fara tahowa shi kuwa be ma san ya bar position ɗin shi ba.

Da gudu Suhaila ta taho tana hankaɗa shi gefe inda ta faɗi ƙasa shima yayi nashi gurin.

Ɗan buɗe ido yayi yana ganin ta sama sama amma ba sosai ba.

Kallon ta yake amma baya ganin ta da kyau, wani luuu ya fara yi da idon sa, nan da nan ta motsa kusa da shi tana tambayar is he okay.

Ganin be bata amsa ba yasa tayi saurin tashi don kiran wani daga cikin gida.

Saurin riƙo hannun ta yayi yace; “Who are you?”

“It does not matter”. Ta faɗa tana ƙara ƙoƙarin tashi, yayi mata nuni da hannun shi yace”My pills, suna nan ki ɗakko mun”. Ya mata nuni da aljihun shi.
Zura hannu tayi tana ɗakko wani magani a roba,ciro guda ɗaya tayi, ɗan kalle kalle ta fara yi ko zata ga ruwa.

Karɓar maganin yayi a hannun ta yana sawa a baki.
Kallon shi ta tsaya yi, kusan five minutes sannan ya tashi ya kwanta akan kujera yace ; “kar ki kira kowa i wll be fine now tun da na sha magan….. Be ƙarasa faɗan abunda zai faɗa ba bacci ya ɗauke shi.

Ta kai kusan 10 minutes tana kallon shi, kafin ta fita daga gurin ta koma cikin gida, duk abun duniya ya ishe ta.

Tana shiga ɗaki ta tarar da Kausar tayi bacci, sallah tayi sannan ta cire kayan jikin ta tana saka na bacci kafin ta kwanta.

2:30am.

Sai can dare Ahmad ya tashi da wata irin yunwa ga wani irin ƙishin ruwa da yake ji. A hankali ya tashi ya fara neman hanyar da zata kaishi cikin gida, ta baya ya yabi ya shiga direct ta ƙofar kitchen.

Suhaila kuwa da ta kasa bacci saboda abubuwan da suka faru ɗazu suna ta juyawa mata.

Hakane yasa ta sakko ƙasa don cin inibi ko zata ji dai-dai, tana zaune daga dining tana cin abunta taji motsi ana buɗe ƙofar kitchen ta baya, ta tsora ta sosai har ta kasa motsi, shi kuwa yana shigowa ya buɗe fridge ya sha ruwa sosai sannan ya buɗe warmers ya lodo abinci dama baya wasa da cikin shi, nan ya kamo hanya zai ƙaraso dining, shi kuwa direct ya shigo abun shi, ita kuwa ƙamewa tayi, ta wani yi pause ga inibin dake bakin ta da be ƙarasa shiga ba.

Yana shigowa ya hango ta, abunda ya fara gani shine inbin dake bakin ta, da gudu ya ƙaraso yana ajiye abincin hannun shi.

Ita kuwa tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, yana zuwa ba wani tsoro ko tunani ya kamo kanta yana saka hannun shi a bakin fa ya ƙwaƙulo inibin yana faɗin “Poison”..

Kallon shi tayi da mamaki, shima ya tsaya yana kallon ta yana Zaro idanu ba tare da ya saki kanta ta ba…..

Ni kuma a dai-dai gurin na tsaya nace na gaji da ɗakko rahoton nan till further notice kuma…

*****

_*How far ne? am serious ooo, till further notice, tunda ba a wani comment sai thanks da wata sticker????*_

_*Ma’asalama, Faɗma Ahmad*_
[7/12, 7:28 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*Page4️⃣4️⃣to4️⃣5️⃣*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

 

w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.

 

*Daga Addu’o’in neman tsayar da ruwan sama*

اَللَّهُمَّ حَوالَيْنَا وَلاَ عَلَيْنَا، اَللَّهُمَّ عَلَى اْلآكَامِ وَالظِّرَابِ، وَبُطُونِ اْلأَوْدِيَةَ، وَمَنَابِتِ الشَّجَرِ.

Allahumma hawalayna wala ‘alayna, allahumma ‘alal-akami wazzirab, wabutoonil-awdiyah, wamanabitish-shajar.

Ya Allah! Ka sanya shi ya zuba a kewayenmu ba a kanmu ba. ya Allah! Ka sanya shi a kan jigayi da duwatsu, da cikin rafuka, da wajen saiwoyin itatuwa.

 

*This page is dedicated to Aunty Sumiee (Sumayya babayo) Allah ya ƙara bar mana ke ina yin ki… ????*

 

_*She is the one….*_

Cire hannun shi yayi a bakin ta yana nuna ta ba tare da ya cire hannun shi a kanta ba yace; “Are you not the one?”

Kallon shi ta cigaba da yi, cikin sanyi murya tace; “Uhmmm your hands, are you planning to kill me”.

Saurin ɗauke hanneyen shi yayi yana faɗin “Ohh, ohhh sorry”.

“Dama kin sanni ne? Kika mun shiru a super market”.

“Uhmmm” ta amsa mai tana ƙara ɗaukan inibi zata sa a bakin ta.

Saurin buge hannun ta yayi, inibin ya faɗi ƙasa.

Idanu ta zaro mai waje tana faɗin”What again, what is the matter, can you please have your food and leave me alone”.

“Baki san wannan abun kamar poison yake ba, ki dena ci please”.

“Ummm don yana maka reacting sai ya zama kowa ma haka yake mai, ni kuma ka ga favorite fruit ɗi na ne ko haushi nake ji idan naci sai inji ni dai-dai, so don haka ba ɗaya bane”.

Zama yayi a kujera yana janyo abincin shi ya fara ci, yana kallon ta yana yatsuna fuska kamar wanda yake kallon kashi.

Sai kusan uku ta tashi zata wuce.

“Ina kuma zaki tafi?” ɗan juyowa tayi tace; “Zan koma ɗaki mana”.

“Thank you for helping me earlier”.

“Don’t mention”.

“Ammm zan iya sanin ki?”

“Yes, why not am just a cook here,that all”.

“A cook?” ya maimata.

“Yess, bye, good night”.

Kafin yayi magana har ta bar gurin, can ƙasan maƙoshin shi yace; “Good night, ita bata tsayawa a ƙarasa magana sai ta wuce”.

Abinci yaci sosai sannan ya koma ɗaki yayi wanka bayan ya fito ya shirya cikin kayan baccin shi masu kyaun gaske.

Be wani daɗe da kwanciya ba alarm ɗin shi ya fara ƙara tashi yayi ya shiga toilet yayi alwala sannan ya fito ya kabbara nafila kafin ayi kiran alfajir.

A ɓangaren Suhaila ma tana shiga ɗaki bacci ya ɗauke ta sai da akayi sallah sannan ta tashi, Bayan ta fito daga toilet ta tashi Kausar da tun da ta kwanta bata farka ba.

Sallah suka yi a tare, Suhaila ta ɗan taɓa karatu, ita kuma Kausar ta koma bacci.

Sai wajen 8:30 sannan suka sakko don shiga kitchen su haɗa abun karyawa.

Suna cikin soya ƙwai Hajiya ta shigo kitchen ɗin.

A ɓangaren Jibril da Ahmad kuwa a hanyar dawowa daga jogging suka haɗu suna dawowa.

Suna gudu suna magana.

Ahmad ne yace ; “Why do you lie to her? Me yasa zaka bari nazo? da ka faɗa mata gaskiya da baza ta faɗa mun ba”.

Jibril kuwa yana nishi yace; “Because they always love you, ita da Hajiya ba ruwan su da ni sun fi sonka da ni, me yasa za su dinga nuna banbanci, so it’s hurt, duk lokacin da naga suna nuna concern a kan ka”.

Ɗan tsayawa Ahmad yayi yana grabbing hannun Jibril hade da cewa”But Daddy loves you more, so i don’t see the differences idan haka ne nima nace sai ya so ni kamar yadda yake son ka mana, ba halin mu ɗaya ba Jibril, you always hide your self from people, idan kuma an fi nuna kulawa a kaina kaji haushi baka da son mutane don haka mutane baza su so ka ba, ya kamata ka gane hakan”.

“Hankaɗa shi yayi yace; ” No, am scared shima Daddy wata rana zai zo yafi sonka a kaina shiyasa nayi abunda nayi jiya”.

“Jibril you don’t have to do all this, duk abunda kake so fa na baka ko lokacin da nake company nake yiwa Dadday zanen atamfa da sauran kayayyaki da ka nuna kana so ba gashi na bar maka ba, amma ka kasa saboda baka da skills ɗin shiyasa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button