ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Just stay away from me ya Ahmad bazan ƙara bari ka ƙwace mun wani abu da nake son mallaka ba”.
Ɗan shiru Ahmad yayi, nan Jibril yayi gaba ya barshi a gurin, ruwan da yake hannun shi ya buɗe yana watsawa kan shi, sannan yabi bayan Jibril ɗin da gudu, yana isa gurin shi yace; “In sha Allah nayi maka alƙawarin indai nine bazan ƙara mallakar abunda kake so ba”.
“Better”. Ya faɗa yana barin shi a gurin.
Jibril ya riga shi shiga gida yana zuwa yayi wanka sannan ya shiga cikin gida don karyawa.
Shi kuwa Ahmad wanka yayi shima sannan ya ɗakko wani file yana dubawa, yana zaune Kausar ta shigo da breakfast ɗin shi a hannun ta.
“Good morning big bro”.
“Morning lil sis”.
“Ga break fast na kawo maka”.
“Thanks, ya Ummi na ta tashi, ina fatan dai lafiya lau ko?”
“Yes lafiya lau, yanzu Dadday da ya Jibril za su fita sai ka shigo cikin gida”.
“Okay” Ya faɗa yana sipping tea ɗin da ta ajiye mai babu alamar damuwa ko ɗaya a fuskar shi.
Fita tayi a ɗakin ta barshi saboda yace mata yana aiki. Jibril kuwa sai da ya shiga ya ga Suhaila sannan ya suka wuce shi da Daddy.
Baya wani ɗan lokaci Ahmad ya shigo cikin gida.
Zainba da saurin ta taje ta Tare shi, hannu ya ɗaga mata yana wucewa cikin palon inda ya tarar da Ummi da Suhaila da Kausar suna zaune suna hira ya shigo cikin palon.
Direct gurin Ummi yaje yana kwantar da kan shi a kafaɗar ta, sannan ya gaishe ta, cike da farin ciki da mamakin wai yau Ahmad ne a gida har ya shigo gaishe ta, ta amsa mai gaisuwar tana jin daɗi mara misaltuwa.
Ɗan leƙo Suhaila yayi yana kallon ta alamun zai yi neman tsokana yace; “Aa Ummi baƙuwa muka yi ne? Ban santa ba”.
Ɗan kallon shi Suhaila tayi suka haɗa ido, ya kashe mata ido ɗaya.
Cikin zuciyar ta tace; “Ahhh, wannan yafi Jibril neman magana ma”.
Kafin Ummi ta kai ga bada amsa, Zainab tayi caraf tace; ” Ba wata bace sai me dafa abinci ya Ahmad”.
Ɗan jinjina kai yayi ba tare da yace komai ba.
Kasaur kuwa galla mata hara tayi tana faɗin”Karya ne, new friend ɗina kenan, kar ka ƙara yin wanta tambayar kuma”. Ta faɗa, dukkan su dariya suka yi har da Ummi.
“A to kin san Hali na da tambaya kuwa, amma kin ƙwaci kanki tunda kinyi kashedi”.
Kausar ya kalla yace; “Am ku shirya mu fita yawo ko, am off today”.
Wani ihu Kausar ta saka tana komawa kusa da shi haɗe da rungume shi, ɗan yatsuna fusa Zainab tayi tana harar Suhaila saboda wani haushin ta take ƙara ji don kashe idon da yayiwa Suhaila ɗazu a kan idon ta ne.
Nigeria…
Ammi ce zaune a palo tana karyawa, sai Farida dake tsaye daga gani tayi shirin makaranta ne, kuɗin hannun ta na kalla naga 500.
Ammi ce fa kalli Abbu tana faɗin”Haba mana za su makara, ka ƙara mata kuɗin motar nan, ya za ayi ace ɗari biyar mutum yayi kuɗin mota sannan yaci har da abinci a ciki, gaskiya ka ƙara mata”.
“Asiya abunda Allah ya hore mun kenan, kuma yarinyar nan tace kuɗin zai ishe ta to meye matsalar ki ne?”
“Ni ko nake da matsala tunda ni na haife ta ba wani yayi mun naƙudar ta ba”.
Girgiza kai yayi ba tare da yace komai ba.
Farida ce ta juya fuuuu tana ƙoƙarin barin palon, Ammin ta ƙara dakatar da ita.
Juyowa tayi tana faɗin”Ammi ki barni please zai ishe ni mana, me zan ci a school ɗin? kuma lokacin lectures ɗin mu ƙara matsowa yake yi”.
Bata ƙara bari taji wata kalma daga bakin ta ba ta fice abun ta, tana buga ƙofar gidan da ƙarfi.
Shima Abbu wucewa gurin aiki yayi suka barta tana ta zuba bala’i ita kaɗai.
Su Ammi kenan, baza a canza hali ba.
London….
Da misalin 4:30 su Kausar suka shirya za tafi outing, kallon Suhaila tayi da take riƙe da wani littafi tana karantawa ko alamar shiri ma babu a tattare da ita, matsawa tayi tana fizge littafin tace ; “Uwar karatu, ki tashi ki shirya mana jiran mu yake fa”.
Suhaila ce tayi dariya tana miƙa hannu zata karɓi littafin cikin muryar shagwaɓa2 tace; ” Please ki bani, nifa babu inda zanje”.
Ɗan girgiza kai Kausar tayi kafin ta buɗe drawer tana jefa littafin tace; “Wallahi baki isa ba malama ki tashi ki shirya mu tafi kawai”.
“Ahhhh, uwar neman magana muje to, duk kinbi kin dame ni wallahi”.
“Dan ma anaso a fita da ke yawo, kinga banbancin shi da wanccen ɗan ƙauyen ko?”
Dariya Suhaila tayi sosai tana faɗin “Kuma a haka nake son shi ba”.
“Ina wata soyyaya, come on tashi ki canza kaya mu tafi malama”.
Riga da skirt ta saka english wears komai black, sannan ta kawo pitch coat wanda ya kai mata har kusan gwiwa tayi rolling da light pitch ɗin mayafi, ta saka flat shoe black, kallon Kausar tayi da take danna waya tace; “Miss, zamu iya tafiya?
“Masha Allah”. Kausar tace tana kallon Suhaila sama da ƙasa, ganin zata mata sharhi yasa Suhaila ta kama hannun ta ta buɗe ƙofa suna fitowa daga ɗakin.
A palo suka tarar da Zainab, ta saka wata crazy coat me irin gashin nan a saman wuya, sai kuma hular sanyi dake kanta.
Harara ta gallawa Suhaila tana faɗin”Wai har da wannan abar zamu tafi?”.
Ko kallon inda take Kausar bata yi ba tace;” Idan kinga hakan be miki ba kina iya fasa zuwa”. Ta ƙarashe maganar tana jan hannun Suhaila.
Suna fita suka hango shi ya wani harɗe ƙafa a jikin mota yaci wani sun glasses me shegen kyaun gaske, coffe wando ne a jikin shi, sai white shirt ya ɗora coffe coat a samanta ya naɗe wuyan shi da white mofula, sai hular sanyi baƙa da take kan shi.
Tun da Suhaila ta mai kallo ɗaya ta ɗauke idon ta a kan shi saboda yayi kyau sosai, ita kuwa Zainab ji tayi wani mugun son shi ya ƙara da sar mata a zuciya.
Wayar da yake dannawa Kausar ta fizge, saurin ɗagowa yayi yana kallon ta, nan yayi ido biyu da Suhaila ɗan kallon ta ya tsaya yi don tayi mai kyau sosai, daga gefan shi kuma ya kalli Zainab, ji yayi wani baƙin ciki ya kama shi.
Bayan mota Kausar ta buɗe tana cilla mai mukulin motar Ummi, Zainba ce ta buɗe gaban mota ta shige, ita kuwa Suhaila bayan Kausar ta bi suka zauna a baya..
A wani shago ya faka,Kausar ce ta kalli shi tace ; “Ya Ahmad me kuma za muyi a nan”.
Be bata amsa ba ya shige gurin be wani jima ba ya fito hannun shi riƙe da wata ƴar jaka.
Cillawa Kausar jakar yayi yace; “Ki bawa friend ɗin ki ta saka, ke ma ki saka ɗaya idan mun isa inda zamu je, Zainab kuma already naga ta saka nata”.
Hands gloves ne irin wanda zaka ga bayan su leda cikin su kuma cotton.
A wani ƙatoton guri ya faka motar.
Da gudu Kausar ta duro tana rungume shi.
“Wow ya Ahmad yaushe rabon da nayi ridding abun nan, wow thank you so much”.
Dariya yayi kawai bece komai ba, ita kuwa Zainab dayake tasan yana zuwa gurin sosai ta san nan za su fara zuwa shiyasa ta fito da shirin ta.
Shiga cikin gurin suka yi kowa ya ɗau takalmi da kuma stick, ita kuwa Suhaila sai kallon su take baki a sake.
Kafin tayi magana har sun shige, tuni Kausar ta saka takalmin ta fara yawo a cikin snow ɗin gurin, itama Zainab bayan ta tabi, ita kuwa Suhaila leƙowa tayi tana kallon su, gani tayi mutum ya miƙo mata abu, ɗan kallon shi tayi tana girgiza mai kai.
“Me yasa?”Ya tambaya yana kallon cikin idon ta”.
“saboda ban san yadda ake ridding ba, kuma akwai sanyi sosai har yanzu jiki na be gama sabawa ba”.
“Na koya miki ne?”
“A’a da sanyi sosai”.
Kallon ta ya cigaba da yi ba tare da ya bar gurin ba, sai jin ihun Kausar yayi har taje ta dawo.
“Ya Ahmad zo muyi tare”.