HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

” Ummm Ammi duk yadda kika tsara dai dai ne, sai kin dawo bari na shiga ciki”.

*****

“Hello oum Walid, kika ce baza ki zo ba?

” Suhaila, au wai yanzu sai da Ammi ta faɗa miki, ni ai da na barshi a suprise ne sai dai kawai ki ganni a garin kano”.

“Amma naji daɗi sosai wallahi, ai na zaci da gaske kike baza ki zo ba”.

“Haba dai Suhaila ina kano ina kaduna da zan ƙi zuwa”.

“To gaskiya a taho mun da prince and princess ɗina kar ma uncle Muhammad yace baza su zo ba, don nasan yanzu sai yace baya so suyi missing school”.

“Karki damu harda shi ma za a mu zo, shi zai kawo mu”.

“Yauwa haka nake so?

” Ya gidan kuwa?amma dai Ammi bata kawo wani matsala ba ko?.

Sai da Suhaila ta leƙa tsakar gida ta window ta tabbatar da Ammi ta fita kafin tace “Hmm kema kin san sai tayi bajintar nan, don 80k ta karɓa a gurin Abba wallahi wai har da su photo calender da kuma memo za tayi”.

“Kai Ammi trouble maker kenan, ai babu yawa ma sosai, kar ki damu komai zai yi dai dai, ke dai kawai naki ido babu ruwan ki da shiga sabgar ta tau, ayi a gama lafiya kawai shine magana”.

“Hmm ai har na fara mata magana ta hau kaina da masifa tun daga nan ban ƙara magana ba”.

“Hmm to ke dama wa ya kaiki ummm, shishigi ko kuma azarɓaɓi?

“Hmm sai dai kin zo kawai, ki gaidar mun da Nihla”.

“Okay zata ji in sha Allah, Assalama alaikum”.

“Wa alaikum salam”.

*******

Monday….. 8:00am

“Kai Suhaila gaskiya kin fiya nawa wallahi tun yaushe nake gidan nan? wallahi zanyi tafiya ta, inaji so kike kar mu shiga cikin convocation arena ɗin nan ko!?

” Sorry besty gani nan fitowa”.

Aunty fatima ce ta ce ” Ummm kya ga da yawa sai kuma ta fito kiga babu wata kwalliyar arziƙi”.

Bata gama rufe bakin ta ba kuwa Suhailan ta fito kamar anjefo ta.

Sanye take cikin wata gold atamfa wacce ta fita sosai, kalar ta sky blue sai kuma touches light purple sai gold ɗin atamfar da ya ƙara mata haske sosai, fuskarta kuma babu wani make Up. Kwalli ne ta saka shi sai kuma powder da ta shafa, sai ɗan lipstick wanda kalar shi ta fito kaɗan akan leɓan nata light purple, sai tayi ɗaurin Zahra buhari wanda ake sa mai kwali, ta yafa mayafin ta tundaga kanta har zuwa gwiwar ta, tayi kyau sosai babu ƙarya, hannun ta kuma ta ɗaura wani agogo me shegen kyau wanda nake tunanin zai iya kaiwa 5k.

Dukkan mutanen da suke palon kallon ta suke kamar wacce suka fara gani yau.

“Uhmm bana faɗa miki ba, sai ta fito kiga babu wata kwalliyar arziƙi”.

Taɓe baki Fatima tayi kafin ta ce”Amma fa kuma duk da haka kinyi kyau babu lefi”.

Ammi ce tayi caraf tace “Ina fa wani kyau, ta wani dankama wani ɗauri, ga wani uban lulluɓi da ta ɗora a kai kamar wata matar liman,Allah dai ya shirye ki”.

“Ke yanzu don Allah Surayya bata burge ki ba? duk da tayi lulluɓin ta a ka, amma ai dai tafi ki kyan gani, Allah ya shirya dai, sai ki wuce ku tafi kin barta tana ta jiran ki kamar wata baiwar ki”.

Sum sum Suhaila tazo zata wuce sai ji su kayi Ammi ta buga salati kamar wanda wani Abu ya faru.

“Ohhh ni Asiya, yanzu ɗan ƙunshin da kika yi, yau na rana ɗaya baza ki bar ƙafar a buɗe ba, sai da kika saka wannan safar taki ta gado. To wallahi sai kin cire safar nan kinji ma na rantse, ko ke kika kawo ustazanci duniya”.

“Kai Ammi don Allah ki barni na tafi a haka mana. wallahi a haka ma nayi ƙoƙari, don Allah”.

“Okay ya zama dole nayi azumi uku kenan, inaji baki ji rantsuwar da nayi ba ko? “.

Zata ƙara magana kenan Surayya da take sanye cikin irin atamfar ta da komai nasu iri ɗaya sai dai yanayin kwalliyar ne kawai ya banbanta, ta ƙifta mata ido, alamar tayi shiru kar ta ƙara magana.

Haka nan ta cire safar ta ajiye ta akan kujera, a nan ne kuma na ƙara ganin kyawun ƙunshin nata saboda da hannu kawai nake gani”.

Cikin ɗacin rai tace”Mun tafi sai kun taho.ya Fatima ki taho mun da kayan da na baki ajiya kar ki manta please”.

Umman sheka da take shigowa cikin palon tayi saurin tare Suhaila tace”Gaskiya Asiya bana son abunda kike wa yarinyar nan, bafa haramun take aikatawa ba ina toilet inajin ku duk kun sa ta a gaba. Ke ba alfaharin ki bane ace tana suturce jikin ta a matsayin ta na budurwa ba, to ma wai idan bata kare al’aurarta ba ya kike so tayi iyee?

“Nifa yaya ba haka nake nufi ba, kawai dai yau na rana ɗaya ai ta ɗan yi kwalliya”.

“Hmmm Allah ya shirya ki tau. Kije gurin Mubarka ki karɓi graduation gown ɗin ki ɗazu na bashi ya goge miki kar garin ɗacin rai ki manta da ita. Sai mun ƙaraso.

“To Umma, mun tafi”.

“Allah ya kiyaye hanya ya kuma sa muku albarka”.

“Amin ya Allah”.

******
Makekyan hall ne wanda yake ɗokan ɗalibai sama da ɗari bakwai, a cike yake dam, maƙil babu masaka tsinke babu abunda kake ji sai hayaniyar ɗaliban da suka cika gurin suna taya juna murnar kamalla karatun nasu na degree, yau kam ranar ta ƴan engineering ce da kuma ɓangren education saboda gurin bazai ɗau ɗaliban makarantar ba shiyasa aka raba ranakun, kowa da ranar shi.

Ƴan engineering sune suke sanye da blue tie while ƴan education kuma da green. Gurin kam yanzu ya ɗan yi shiru saboda shugaban makarantar nasu *YAHUZA BELLO* ya fara gabatar da speech.

Ya daɗe yana jawabi kafin baƙin da suka halarci gurin suma suka karɓa, bayan an gama ne kuma ya fara bawa ɗaliban wata letter da take cikin wani gwangwani wanda aka ƙayatashi da logo ɗin makarantar.

Nan dai akayi aka gama wanda taron sai da ya ɗau kusan awa uku.

Nan fa ɗaliban suka fara fitowa, wanda ga wasu nan a waje basu samu damar shiga ba,saboda makarar da suka yi.

A can ƙarshe na hango su Suhaila suna shirin fitowa daga gurin, yanzu kam kwalliyar da akayi ta canza makani saboda gumurzu da aka sha cikin wajen.

Ai mamaki be gama kamani ba sai da na kai ga fitowa daga cikin gurin. Jama’a ne rututu a bakin gurin yadda kasan filin idi, kowa na jiran ɗan uwanshi ya fito daga cikin convocation arena ɗin don su tarbe su.

Nan fa guri ya ƙara ɗinkewa, jama’a suka ƙara cakuɗewa.

“Surayya kin san me za muyi kuwa?

” A’a sai kin faɗa”.

” Mu wuce inda kika yi parking motar mijin ki, ki kai mu department mu karɓo result ɗin mu, don wallahi kin san idan su Ammi suka ganmu zamu sha kwakwa kafin mu samu shiga cikin makaranta, kinga kafin nan an cika department sai mu karɓi result da wahala, zo muje kawai”.

Basu ɓata lokaci ba suka wuce department suna zuwa kuwa suka yi sa’a babu wani layi sosai, nan su kayi signings ɗin da za su yi,su ka karɓi result nasu. Cikin farin ciki suka bar department ɗin.

*****

“Aaa masha Allah, haka ake so, Allah yayi wa wannan karatu naku albarka, Allah ya baku abunda kuke nema sannan ya kawo muku aiki a nan kusa”.

“Amin ya rabbil alamin hajiya mun gode sosai sosai”.

“Aaaa wa yaga su ya Suhaila da ya Surayya da second class upper”.

“Aa yarinya ya son ranki, faɗi ki ƙara faɗa, saura ku”. Cewar Surayya.

“Fadila wallahi ki fita daga ido na tamm, idan na kama ki baza ki ji da daɗi ba”.

“Oyoyo ga ƴata, ga ƴata, Allah yayi miki albarka Suhaila, Allah ya biya miki buƙatu, ashe haka aka yi kun fita da result me kyau, ai tun daga rumfar can Mubarak ya fara sanar da ni”.

“Na gode sosai Umma. Amma ai kin makara baki ƙaraso da wuri ba”.

“Mun tsaya kammala aikin gida ne Suhaila shiyasa, kowa yaji daɗi sosai wallahi Allah ya ƙara hazaƙa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button