ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Dariya yayi mata yana ɗora stick ɗin shi a ƙasa ya ƙarasa inda take. Hannun ta ya kama suka tafi a tare suna yi suna canza position, wayar ta Suhaila ta ciro a cikin aljihu ta ɗauke su huto ta baya, da suka juyo ma ta ɗauke su.
A tare suka iso su uku,bayan sun sakko Kausar ta taho da gudu tana faɗin” Ƴar ƙauye kawai”.
Dariya Suhaila tayi tace ; “Ai ku manya ne shiyasa, ni kuwa ai sai nayi rashin lafiya, akwai sanyi sosai fa”.
“Haka ne zaki saba”. Kausar ta faɗa tana cire takalmin ƙafar ta”.
Bayan sun fita daga gurin suka biya wani restaurants aka kawo musu shayi me mugun zafi, don sun ɗebo sanyi, ita kuwa Suhaila tana tsaye Ahmad ya ƙaraso inda take yace; “Baki sha shayin ba sosai me za a kawo miki? kallon shi tayi tace; ” Grapes”.
Yatsina fuska yayi yana matsawa a kusa da ita yana faɗin”No, no, ki faɗi wani abun dai amma ba wannan ba”.
Dariya tayi sosai sannan tace ; “Okay ice cream”.
“Babu a nan amma bari mu fita sai na siya miki a hanya, da sanyi fa amma”.
Gyaɗa mai ka tayi.
Nan suka kama hanya suka nufi wani gurin wasa.
Costa roll su Zainba suka ce za su hau, ita kuwa tace baza ta haushi ba, saboda akwai lokacin da suka je roxy a kano har sai da ta kusa fitsari a wando tsabar tsoro da fargaba, ga wannan ma yafi na roxy ɗin.
Hawa suka yi suka fara ridding inda Suhaila ta tsaya a gefe tana jin yadda mutane suke ihu daga can sama.
Dariya tayi tana tuna lokacin da suka yi da Farida har sai da tayi fitsari a wando ranar kuwa ba wanda bata kira ba, Allah ne annabi ne, daga baya ma tace idan basu kashe ba duk Allah ya tsine musu. ????????
Tana cikin murmushin nan taga an miƙo mata abu.
Zama yayi a kusa da ita yana faɗin”Wannan dariyar fa?”.
Karɓar ice-cream ɗin tayi tana buɗe shi kafin tace; ” Na tuna sister na ne da muka hau wani irin shi a kano har sai da tayi fitsari a wando, daga baya tace idan basu kashe ba Allah ya tsine musu”.
Dariya yayi shima yana faɗin”Itama Kausar lokacin da take 15 years muna zuwa nan, hawan ta na farko sai da ta kusa suma, amma yanzu kinga ta iya sosai da sosai”.
“Dama haka ne ai, practice makes perfect, gashi yanzu harda video take yi”.
Suna cikin hirar su abun ya zagayo su Kausar suka sakko, a lokacin kuwa Zainab ji take kamar ta shaƙe wuyan Suhaila, hannun shi ta riƙe tana cewa wai su hau water splash, be mata musu ba suka tafi a tare su huɗu dama Suhaila tana so ta hau shi, mutum biyu-biyu ake hawa a gurin zaman amma sai da kujerun kusan a haɗe suke wani ɗan ƙarfe ne kawai ya raba su.
Ahmad da Zainab suka zauna a waje ɗaya sai Suhaila da Kausar, sai dai ɗan ƙarfen da ya raba su ita Suhailan a kusa da Ahmad take,amma ba gurin su ɗaya ba suna dai jere ne.
Kunna abun aka yi ya fara tafiya inda abun da farko zaka ji kamar babu Wahala, amma da akayi nisa ya fara zuba gudu gashi daga sama yake yin ƙasa yabi ta cikin ruwa. Da gudu ya gangaro yayi ƙasa inda Suhaila ta runtse idanun ta, sai jin ruwa tayi a jikin ta saboda yadda ya taho da gudu har sai da ruwa ya fallatsa. Ita da Kausar kuwa riƙe hannu suka yi inda daga ɗayan ɓangaren bata san hannu ko waye ba ta kama ta riƙe shi gam,shima riƙe hannun ta yayi.
Har sai da abun ya tsaya, cire hannun ta tayi a cikin na Kausar suna shirin sauka inda shi kuma yaƙi sakin hannun nata, ɗan juyowa tayi jin hannun ta cikin na mutum suka yi four eyes, saurin sakin hannun nata yayi yana sauka daga gurin ita ma sauka tayi.
Basu ƙara tsayawa a wani gurin ba suka wuce gida.
Suna shiga yayi parking a gurin da ake ajiye motoci, suna fara sakkowa Jibril ya fito daga part ɗin su, dama ya dawo tuntuni Hajiya tace mai ai sun fita da Ahmad.
Shi kuwa Ahmad ganin Zainab bata son Suhailan a kusa da shi yasa ya matsa yana whispering a hankali.
“Am sorry madam, it was accidentally”.
Ɗan murmushi tayi tana kallon shi, a dai-dai lokacin Jibril ya ƙaraso kuma yaga abunda ya faru.
Da sauri ya ƙaraso gurin, be yi wani tunani ba saboda tsabar idon shi ya rufe da kishin bala’i ya fincike hannun ta yana jan ta, ta koma side ɗin shi, ita kuwa tsabar mamaki ya hana ta furta kalma ko guda.
Ahmad ya kalla yana nuna shi da hannu yace; “Stay away from Suhaila she is my fiancée, and i love her”.
Shi kuwa Ahmad abun mamaki ma ya bashi dariya kawai yayi yana gyaɗa mai kai.
Inda ya ƙara jan hannun Suhaila suka bar gurin..
*****
_*Manage please*_
*_Faɗma Ahmad_*
[7/14, 6:03 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page4️⃣6️⃣to4️⃣7️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.
*Addu’ar Ganin Jinjirin Wata*
اللهُ أَكْبَرْ، اَللَّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلَيْنَا بِاْلأَمْنِ وَاْلإِيمَانِ، وَالسَّلاَمَةِ وَاْلإِسْلاَمِ، وَالتَّوْفِيقِ لِمَا تُحِبُّ وَتَرْضَى، رَبُّنَا وَرَبُّكَ اللهَ.
Allahu akbar, allahumma ahillahu ‘alayna bil-amni wal-eeman, wassalamati wal-islam, wattawfeeiqi lima tuhibbu watarda, rabbuna warabbukal-lah.
Allah ne Mafi girma. Ya Allah! Ka sanya tsayuwarsa a gare mu ta zamo kwanciyar hankali ce da imani, da Aminci da Musulunci, da kuma gamonkatar da abin da Ka ke so, ya Ubangijinmu, kuma ka ke yarda da shi. Ubangijinmu da Ubangijinka (ya kai wannan jinjirin wata!) shi ne Allah.
_*The confusion*_
*Congratulations, sis Juhee Allah ya kaimu da rai da lafiya yasa da mu za ayi Amin ya rabbi*
Cikin gida ya jata suka shiga ta Kitchen, suna shiga ta fizge hannun ta a cikin nashi.
Ita kuwa Kausar sakin baki tayi tana bin shi da kallo, wai my fiancee ko da yaushe ta zama fianceen nashi oho mai.
Shikuwa Ahmad hanyar part ɗin su yabi ya shige ɗaki yana ɗaga kafaɗa ko a jikin shi.
****
“Suhaila stay way from that spoil some one ɗin nan na faɗa miki ko, idan za su tafi yawan su kar in ƙara ganin kafar ki ta bisu, kin san ina da ina suke zuwa da zaki bisu, han?”
Ɗaga mai hannu tayi tana faɗin”This is the last time da zaka ɗau hannun ka ka taɓa ni, am not your trash bin ko kuma closet naka da duk sanda kaso zaka ɗau hannun ka, ka taɓa ni, and naji kana cewa fiancee ko menene, yaushe na zama fiancee naka umm? Yaushe aka mana engagement ban sani ba? ko kaje gidan mu ka kai kuɗi na ban sani ba? An that someone da kake faɗa ba wani guri ya kai mu ba, sannan kuma banga wani spoil habit a tattare da shi ba”.
Ganin Suhaila tayi fushi sosai yasa ya kwantar da murya.
“Am really sorry Suhaila i don’t mean to hurt you, kiyi haƙuri please amma don Allah ki dena shiga harkar shi, sannan kuma in sha Allahu muna dawowa daga tafiya za ayi magana da Daddyn ki asa mana ranar aure don soon nake so ayi bikin idan ba haka ba za a iya samun matsala wallahi”.
Kallon shi tayi kawai ta juya zata shiga cikin gida, yayi saurin shan gabanta yana daɗa bata haƙuri.
“Don Allah kiyi haƙuri my Suhaila”.
Murmushi tayi sannan tace ta haƙura.