ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Tana shiga ta tarar da Kausar har ta cire kayan jikin ta.
Toilet ta buɗe ta shiga ta ɗora alwala tayi salla.
Bayan ta idar da sallah ta kalli Kausar tace; “Ni kam ina so na tambaye ki wani abu”.
“Uhmm inajin ki”. Kausar ta faɗa tana sauke wayar da take dannawa.
“Don Allah meye tsakanin Ahmad da Jibril? Me yasa suke samun matsaka haka? Ɗazu ce mun yayi wai spoil someone kamar ba ɗan uwan shi ba”.
Wani long sigh Kausar ta sauke kafin tace; “Wannan dogon labari ne sosai, amma zan fison ki san hakan nan gaba”.
“Okay” Suhaila ta faɗa tana buɗe ƙofar ɗakin ta tafi zuwa kitchen.
Tana shiga ta tarar da Ummi tana girki abun ta, saurin ƙarasawa tayi tana faɗin”Haba Ummi da kin bari na dawo nayi ai, meye amfani na to? ”
” A’a ki bar shi kawai sanda nake so zanyi, sau nawa faɗa miki ba don haka na kawo ki gidan nan ba”.
“Haka ne Ummi amma duk haka inajin ba daɗi”.
“To yanzu taya ni yin paper chicken ɗin na”.
To ta amsa mata dashi, tana placing tukunya a wuta haɗe da zuba mai,sannan ta fara aikin ta cikin nutsuwa da ƙwarewa.
Bayan sun kammala suka shirya komai a dining a lokacin ne kuma Kausar ta sakko ƙasa.
Da sauri ta ƙaraso tana buɗe warmers ɗin haɗe da shaƙar ƙamshin abincin tana faɗin “Wow yau za muci abincin Ummi da na Aunty Suhaila”.
Ahmad da yake shigowa shi da Zainab yace; “Kice yau zamu ci delicious”.
Kowa kallon shi yayi, Ummin shi ya kalla yana ɗaga kafaɗa yace; “Yess tsohan hannu da kuma ƙwararren hannu, kinga za aci daɗi kenan”.
Dariya Ummi tayi tana smacking kanshi tace ; “Ɗan nema kawai”.
Kujera ya janyo ya zauna yana buɗe abincin, ba wani ɓata lokaci ya fara zuba abinci ko a gefan takalmin shi.
Ummi ce ta zauna tana faɗin”Ai ka bari ayi serving naka ko”.
“Tabb ina Ummi, in tsaya sanya mijin ki ya dawo ya hana ni cin abinci da ke”.
Dariya duk suka yi, jan kumatun shi Ummi tana faɗin”Maza kaci to”.
Zama su kayi duka, ita kuma Suhaila ta juya zata bar gurin.
Yana kallon duk move nata, yana kai loma baki yace; “Haba miss Suhaila yanzu so kike wannan albarka ta wuce ki”.
Ummi tayi saurin juyowa tace; “Haba mana, zo ki zauna a nan muci yau ai Daddyn su baya nan.
Cikin sanyin jiki tazo ta zauna tana harar shi, inda shi kuma yake kallon wani wajen amma a zahiri yana kallon abun da take yi.
Duk a takure take don abincin ma kawai dai cin shi take yi amma ba a nutse take ba.
Suna cikin haka shi har ya gama cin abinci shi ma, suka ji motar Daddy, da gudu ya tashi yana shigewa kitchen.
Bayan shi Kausar ta kalla tana sakin dariya har da su tuntuɓe, Suhaila ma sai da tayi dariya, Ummi kuwa cewa tayi”Ɗan nema kowa da wanda yake jin tsoro”.
Ɗan leƙowa yayi yana faɗin”Zan kama ki Kausar zaki sani”.
Suhaila ce ta tashi itama tayi hanyar stairs ta koma ɗaki, shi kuwa zama yayi a kitchen yana jin shigowar su.
Wani iri yaji a ranshi jin yadda ake ta kacaniyya sai yaji shima dama ace da shi ake yi.
Ɗan leƙowa yayi yana kallon yadda suke cin abinci cikin natsuwa duk da akwai ƙarancin walwala a fuskar ko wanne daga cikin su.
Zainab ce ta tashi tsam da plate ɗin ta a hannu ta shigo kitchen kamar wacce ta gama cin abincin.
A zaune ta hango shi ya haɗe kai da gwiwa. Plate ɗin ta ajiye tana matsawa kusa da shi tana zuwa ta kamo kanshi tana rungumewa a saman cikin ta, tana faɗin “Ya Ahmad kayi haƙuri ka manta da abubuwan da suka faru don Allah, kazo muyi aure”.
Cire jikin shi yayi a nata yana miƙewa zai bar kitchen ɗin ba tare da yace komai ba.
Shan gabanshi tayi tana daɗa reƙo hannun shi.
Fizgewa yayi ya nuna ta da hannu yace ; “Na ce miki ki dena bi na bana so ko, ko so kike nayi raping naki ne na gaskiya, stay aware from me Zainab me yasa baki ganewa ne, ke wacce irin mayya ce, na tsane ki, na tsane ki, ki fita a rayuwa ta”.
Barin kitchen ɗin yayi yayin da ita kuma ta fito da gudu tana hayewa sama, da kallo suka bita, inda Ummi tayi murmushi kawai don ta san ita da Ahmad ne.
Ɗaki ya koma yana jin kan shi yana wani mugun sarawa, kayan shi ya cire ya saka na barci yana kwanciya a kan gado, haɗe da janyo blanket zuwa rabin jikin shi,ganin zai shiga halin ha’ula’i yasa ya tashi ya ɗakko maganin shi ya sha. Komawa yayi ya kwanta be daɗe ba bacci ya ɗauke shi.
*****
Bayan Suhaila ta shiga ɗaki ta ɗakko wayar ta ta kira Surayya don su gaisa. Surayya kuwa na ganin kiranta tayi saurin ɗauka tana karawa a kunnen ta.
“Hello besty na ya kike ya London?”
“Ina lafiya lau Alhamdullilah, ya baby Najwa?”
“Tana lafiya lau wallahi, gata nan sai rigima take, wai baza mu saka pampas ba”.
“Ayya, Allah sarki tana fitsarin kwance ne”?
“Aa, gaskiya ba sosai ba, sai ta kwana biyar ma ba tayi ba indai bawai ruwa tasha da yawa ba”..
“To ki ƙyale ta mana, ta saba ma”.
“Wallahi nima haka nake so amma baban ta ne sai yace a saka don za ta iya yi”.
“Ayya ki gaida shi, sai da safe dama cewa nayi bari na kira mu gaisa”.
“Ai kuwa mon gode sosai ina doctor Jibril? No story a bani na sha mana”.
Dariya Suhaila tayi tace; “Ki bari sai kin saka kati sai ki kira na kora miki jawabi”.
Kashe wayar tayi tana dariya. turawa da Abbun ta message tayi, tana tambayar ko ya yake ya yanayin gidan nasu.
Tana zaune Ummi ta shigo ɗakin. Ɗan tashi tayi ta gyara zaman ta don jin abunda Hajiyan zata faɗa.
Guri Hajiya Kulthum ta samu ta zauna tana fuskatar Suhaila.
A hankali ta fara magana”Dama cewa nayi, kinga yanzu mun shiga wata na kusan 7 kenan, to zancen albashin ki zaki bari sai munje Nigeria a baki ko kuma na baki a nan ko akwai abunda zaki siyawa mutanen gida ki aika musu da shi”.
Ɗan jimm Suhaila tayi sannan tace; “A’a ki barsu a hannun ki zan kira su sai na ji yadda za ayi”.
“Yauwa to hakan yana da kyau, dama cewa nayi bari na tambaye ki”.
“Ayya Ummi ba komai ai da kin kirani ma da nazo”.
“A’a ba komai wallahi, ina Kausar take bata shigo ba?”
“Eh Ummi bata shigo ba”.
“Ayya inaji ta wuce gurin Ahmad ne”.
“Eh may be”. Suhaila ta faɗa tana wasa da ƴan yastun ta.
A ɓangaren Kausar kuwa part ɗin su Ahmad ta nufa, tana zuwa ta shiga ɗakin shi sai dai ta hango shi yana ta bacci abun shi.
Robar maganin shi ta hango a kan bedside tayi saurin ƙarasa tana dubawa, ɗan rubutun da yake jiki ta karanta, saurin ɗagowa tayi tana kallon shi a lokacin ne kuma taji wani mugun tausayin shi ya ƙara shigar mata.
Gyara mai kwanciya tayi tana ja mai bargo da kyau, a hankali ya ɗan buɗe idon yana kallon ta, murmushi yayi mata, itama ta mayar mai taana faɗin”Ka cigaba da baccin ka yanzu xan tafi nima na kwanta dare yayi sosai”.
Gyaɗa mata kai yayi yana lumshe idon shi.
Direct ɗaki ta koma abun duniya duk ya ishe ta. Da sallama ta shiga ɗakin nata inda ta tarar da Suhaila a kwance kamar me bacci amma ba baccin take ba.
Guri ta samu ta zauna nan taji motsin mutum yana ƙoƙarin shigowa ɗakin, kafin tayi magana har ya buɗo ƙofar, tana ganin shi tace; “Ya Jibril tayi bacci ka bari sai da safe”.
Kallon Suhaila yayi kamar me bacci sannan ya mayar da ƙofar ya rufe.
Bayan kwana biyar.. haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Kausar ta shiga damuwa sosai ganin pills ɗin Ahmad da tayi, shi kuwa sai rayuwar yake a gidan su cikin kwanciyar hankali, inda idan yana da aiki zai fita idan kuma basu da shi zai ɗan je yayi abunda zai yi ya dawo, Suhaila da Jibril kuwa sai daɗa shaƙuwa suke inda, Ahmad kuma yana sa ta dariya sosai tana jin daɗin kasancewa da shi a duk sanda suke tare da mutanen gidan saboda ko ba komai zai yi tsokana kuma za aci dariya.