ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Yau ta kama Daddy da Jibril za su tafi Germany inda aƙalla za suyi kusan wata biyu zuwa uku don wani business ne ya taso musu gashi dole ya tafi da Jibril kuma dama aikin shi na asibiti kusan part time job ne, saboda yana ganin patients ma a Nigeria.
Inda Daddy ya sanar da Ahmad da kuma Ummi ranar da yaji zai dawo to ya bar mishi gidan shi.
Jibril ne Zaune a garden cikin sea green suit tayi mai kyau sosai gashin nan yaji gyara ga wani takalmi me shegen kyau a ƙafar shi.
Suhaila ce daga gefan shi tayi tsit gaba ɗaya ba ta son tafiyar da zai yi, inda shi kuma sai lallaɓata yake yana bata haƙuri.
Gaban ta ya koma saboda ta juya mai baya, ya fuskance ta yana marairaice fuska yace; “Don Allah kiyi haƙuri, na miki alƙawarin muna dawowa za ayi maganar auren mu, so dom haka ki dena damuwa. Ni zan tafi yanzu, kar Daddy yazo yana jira na, zan yi mai maganar ki a can nasan bani da matsala da shi sannan Hajiya ma baza ta bamu matsala ba, I love you Suhaila, ki kular mun da kanki please”.
Ɗagowa tayi ta kalle shi duk idon ta ya ciko da ƙwalla tace; “I love you too, take care of yourself and be safe”.
“In sha Allah, ki yafe mun da abunda zanyi yanzu can’t hold me self”.
Kafin tayi magana ya bata peck a baki yana saurin miƙewa, haɗe barin gurin.
Lumshe ido tayi tana jin gaban ta na faɗuwa.
Wato duk inda kakai ga addini indai kana irin garuruwan nan kana tare da irin su, sai a hankali dole wata rana sai kayi abunda ba dai-dai ba.
Kuma su basu ɗauke shi a bakin komai ba, wai ai ina sonka kina so na ne, wai suma sun ɗau al’adar turawa, peck, kiss, hug, holding hands wai duk cikin relationship ne, duk cikin love ne. Kai Allah ka rabamu da iyaye masu son zuciya su ɗaukeka su kaika irin nan gurin a sunan aikatau. Allah yasa mu dace.
Yana fitowa ya shige part ɗin su ya janyo jakar shi ya fito da ita daga ɗakin shi, yana fitowa Ahmad ma ya fito daga ɗakin shi, kasancewar ɗakunan su suna facing na juna.
Ɗan tsayawa Jibril yayi yana kallon Ahmad yace; “Yauwa zanyi tafiya, zan baka guri for sometimes, kafin na dawo, and am warning you stay aware from my woman, i love her so much, kar ka sake kayi attempting yi mata halin bunsurancin da ka saba, duk na san ita ba haka take ba za ta taka maka burki don baka isa ba”.
Tuni ran Ahmad ya ɓaci nan da nan zuciyar shi ta tafasa, ciwon shi ya sauka, juyo da Jibril yayi ya naushe shi a fuska ya daɗa ɗago ya ƙara naushin shi, tuni hancin shi ya fashe jini ya fara zuba.
Har ya ɗaga hannun zai ƙara dukan shi, sai kuma ya dunƙule hannun ya daki bango da shi har sai da hannuwan shi suka yi ƙara.
Cikin ɓacin rai yana zubar da hawayen da bashi da control a kan su, dole sai sun zuba yace; “I will stay away from her basai ka zo kana mun ihu a ka ba, kana kira na da bunsuru ba, kasan abunda ya faru ne? Ko kana nan? da zaka dinga ƙarar da abunda baka sani ba”.
Shiru yayi ya durƙushe a gurin yana sakin kuka mai ƙarfin gaske, ya rasa yadda zai yi, ya rasa ina zai saka kanshi, ya rasa me zai ce mai zai yi mutane su fahimce shi.
Jibril ya tashi yana goge jinin hancin yace ; “Bazan taɓa fahimta ba, kuma abunda kayi akace kayi”.
Ya ƙarashe maganar yana wucewa cikin ɗaki don wanke fuskar shi, jinin ya wanke ya fito ya saka tissue ya toshe ƙofar da jinin yake fita ya turo akwatin shi ya fito.
Yana fitowa ya tarar da su a compound sun rako Daddy ƙarasawa yayi yana sunkuyar da kai.
Daddy ne ya kalle shi yace; “Kai me ya faru da kai naga kamar hancin ka ya fashe ga fuskar ka tayi wata iri?”
“Ba komai haɓo nayi ne, shiyasa ban fito da wuri ba”.
“Ayya sannu” Ummi ta faɗa tana ɗaga fuskar shi tana dubawa, haɗe da ƙara jeramai sannu.
Daddy ne yace; “Ƙarya kake yi”.
Ganin yadda Hajiya ta nuna damuwa yasa yayi insisting cewar haɓon ne.
Hajiya ce tace; “Kasan sanyi ne sai a hankali k?”
“Na sani ko waccen wawan ne ya dake shi”.
Shiru tayi bata ƙara magana ba.
_*Ma’asalam*_
*_Faɗma Ahmad_
[7/21, 8:58 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Page 4️⃣8️⃣to4️⃣9️⃣*
*Wattpad@cynosure3*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶????
w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,
s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶✍,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.
α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶̶????,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶ c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.
*Dedicated to my cynosure, Allah ya biya buƙatu na alkhairi, Amin ya Allah*
66- Daga Addu’o’in neman tsayar da ruwan sama
اَللَّهُمَّ حَوالَيْنَا وَلاَ عَلَيْنَا، اَللَّهُمَّ عَلَى اْلآكَامِ وَالظِّرَابِ، وَبُطُونِ اْلأَوْدِيَةَ، وَمَنَابِتِ الشَّجَرِ.
Allahumma hawalayna wala ‘alayna, allahumma ‘alal-akami wazzirab, wabutoonil-awdiyah, wamanabitish-shajar.
Ya Allah! Ka sanya shi ya zuba a kewayenmu ba a kanmu ba. ya Allah! Ka sanya shi a kan jigayi da duwatsu, da cikin rafuka, da wajen saiwoyin itatuwa.
_*Do we have the same problem?*_
Hajiya Kulthun bata ƙara magana ba, su Daddy suka shiga mota za su wuce, ɗaga musu hannu suka yi inda kowa yake jin daɗin tafiyar tasu.
Cikin gida suka koma, inda Hajiya take tunanin boɗeɗɗen hali irin na mijin nata babu yadda za tayi da shi amma ba ta son abunda yake yi a tsakanin ƴaƴan nashi. Haka tayi ta juya maganar har ta shiga ɗaki tana tunanin abun a ranta.
Kausar kuwa kamar ta san yayan nata yana cikin wani hali bata shiga cikin gida ba ta nufi part ɗin su, tana shiga ta hango shi sai uban nishi yake, be motsa daga inda ya zube ba tun da suka yi faɗa da Jibril.
Da sauri ta ƙarasa gurin tana kiran sunan shi, ɗago shi tayi tana taɓa fuskar shi haɗe da yin waige don neman me tekama mata.
Ta buɗe baki zata fara ihu kenan yayi saurin rufe mata baki yana girgiza mata kai, a hankali ya yunƙura zai tashi ita kuma ta temaka mai suka shiga cikin ɗakin shi, rafkewa yayi a gado yana maida numfashi, kallon ta yayi yana mata nuni da side bed drawer dake gefan ta, kallon gurin tayi don ganin abunda yake nuna mata, robar maganin shi ta gani da sauri ta ƙara gurin ta ɗakko haɗe da ruwa ta bashi ya sha.
Bayan kamar 10 minute ya fara dawowa cikin nutsuwar shi duk wani abun da yake ji yayi ƙasa, wata annashuwa da jin daɗi ya saukar mishi.
Kallon Kausar yayi yana girgiza mata kai ganin tana zubar ta hawaye, saurin tashi zaune yayi cikin nutsuwa, hannun shi ya buɗe mata alamar tazo, babu musu kuwa ta faɗa jikin shi tana sakin wani kuka mai cin zuciya.
Zuciyar shi ce yaji ta mai ba daɗi ganin hawayen ƙanwar tashi abun ƙaunar shi.
Ɗan ɗago ta yayi yana share mata hawayen yace; “Ya isa haka princess ɗi ta,tsada gare ki fa, don Allah ki dena zubar da hawayen nan naki, am fine ba gashi na dawo dai-dai ba”.
“A’a ya Ahmad, ba ka dawo dai-dai ba tun da har sai da ka sha magani, wai da yaushe ka fara shan wainnan pills ɗin?”
“Ummm daɗewa”. Ya faɗa yana jan kumatun ta”.
Riƙe hannun shi tayi tace; “Yaya mubar maganar wasa, ya kamata ka dena sha, idan ba haka ba akwai matsala, duk sanda irin haka ta same ka sai ka sha zaka samu nutsuwa”.