HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Bazan taɓa iya dena sha ba, har sai kwanaciyar hankali ta same ni, har sai na samu wanda zai iya kula da ni, har sai na samu wanda zai ɗauke mun duk wata matsala ta, Kausar har sai na kasance cikin ku, kuma cikin farin ciki, babu tsangwama kuma babu ƙiyayya”.

Shiru tayi tana kallon yayan nata hankalin ta yana daɗa tashi sosai.

Tashi tayi zata tafi yayi saurin riƙe hannun ta yace; “Please kar ki sanar da Ummi halin da nake ciki ba na so hankalin ta ya tashi”.

Gyaɗa mai kai tayi ba tare da ta ƙara magana ba ta fita daga ɗakin nashi.

Runtse ido yayi ya koma ya kwanta yanajin zuciyar shi babu daɗi sam saboda yasan Kausar ɗin tayi fushi ne.

Ɗaki ta koma direct tana shiga ta hango Suhaila a jikin window tayi shiru kamar ba ita ba, daga gani itama a cikin damuwa take.

Juyowa Suhaila tayi jin motsin Kausar ɗin nan suka haɗa ido.

Suhaila kuwa mayar da hankalin ta tayi kan Kausar ɗin ganin hawaye duk ya jiƙa mata fuska, da sauri ta ƙarasa tana riƙe mata hannu haɗe da jero mata tambayayo.

“Me ya faru? Me ya same ki? Wani abun ne ya samu Ummi? Tana ina?”

Ta ƙarashe maganar a mugun tsorace ga kuma tashin hankali kwance a kan fuskar ta.

Rungume ta Kausar tayi tana fasa kuka, yayin da Suhaila ta kasa furta ko a sai janta da tayi suka zauna a bed bench ɗin gurin tana lallashin ta.

Cikin sanyin murya Suhaila tace ; “Me ya faru? Kin ƙi kiyi magana sai kuka kike yi”.

Kamar an tsikare ta tace; “Me mukayiwa Daddy? Me yasa baya son ya Ahmad? Me ya Ahmad yayi mai? Yaushe zai yafe mai? Sai yaushe zai gane cewa duk abunda aka ce ya faru be faru ba? Sai yaushe zai ajiye wannan ƙiyayyar ya haɗa kan ƴaƴan shi? Ya Ahmad yana can a kwance rai a hannun Allah, ya Ahmad ya zama kamar wani ɗan shaye-shaye, sai ya sha magani yake iya controlling internal behavior ɗin shi, sai yasha maganin yake iya controlling angern shi, ya Ahmad…..”

Bata ƙarasa faɗan abunda yake bakin ta ba ta ƙara saka kuka tana ƙanƙame Suhaila, ba Suhaila ba har ni sai da naji tausayin shi.

A hankali Suhaila tayi ta shafa bayan ta ba tare da tace ƙala ba har bacci ya ɗauke ta.

Gyara mata kwanciya tayi tana goge mata ragowar hawayen fuskar ta, ta ja mata blanket ta tsaya tana kallon innocent face ɗin ta.

Tafi 10 minute a haka, sai ƙarar wayar ta ne ya katse mata tunanin da ta lula, wato idan baka mutu ba ka ga da yawa, yau taga matsalar da ta murje tata.

Cikin nutsuwa ta ƙarasa gurin inda taga sunan Abban ta yana yawo akan wayar mamaki ne ya cika ta don tasan baya kira tunda ƙuɗin da za a charge mutum yawa gare su messege ɗaya ma sai a ɗauka kusan 16 naira.

Sai da wayar ta katse sannan ta kira shi, da sallamar shi ya answer wayar,inda ta amsa mai tana jin gaban ta na faɗuwa, ta san muryar shi sare indan yana cikin ƙunci ko farinciki.

Bata ƙarasa jin sallamar tashi ba tsabar tashin hankali tace; “Abbu na me ya faru? Me ya same ka?”

Ɗan shiru yayi yanajin zuciyar na mishi zafi sosai. Sai da ta ƙara nanata tambayar idon ta ya ciko da ƙwalla sannan yace ; “Inajin zaman aure tsakani na da Ammin ku yazo ƙarshe zan sawaƙe mata kawai kowa ma ya huta”.

Ji tayi gaban ta ya bada wani dam daram kamar bom ya tashi.

Cikin kuka tace; “Abba na don Allah kayi haƙuri, koma menene zan kira ta muyi magana, me ya faru ma Abba da har yasa zaka yanke wannan hukuncin?”

“Ko dai ma me ya faru na faɗa miki don na gaji wallahi ta takurawa rayuwa ta, ta hanani sakat ta tsane ni bata son gani na kusa da ita”.

Ta buɗe baki za tayi magana kenan taji kuɗin sun ƙare nan ta shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa.

Fita tayi ta rasa inda zata sa kanta dama Kausar ce ke musu recharging don bata ma san ya ake yi a nan ba gashi tayi bacci kuma baza ta iya tashin ta ba.

Dai-dai jikin windon Ahmad ta zube tana kuka kamar ranta zai fita, yana kwance idon shi a lumshi ya jiyo shashsheƙar kukan ta.

Saurin tashi yayi yana leƙowa ta window, a durƙushe ya hangota sai kuka take kamar ranta zai fita, da sauri ya fito daga ɗakin sai da yazo dai-dai ƙofar fitowa daga part ɗin nasu sai kuma ya tuna rashin mutuncin da Jibril yayi mai a kan ta ɗazun da ko cikakken awa 3 uku ba ayi ba, jikin shi a sanyaye ya koma cikin ɗakin yana tsayawa a jikin window haɗe da ƙare mata kallo yana jin kukan nata yana ratsa ko wacce gaɓa ta jikin shi.

Tafi 15 minuets a gurin inda shima yana nan a inda yake be motsa ba, sai da ta gaji don kanta sannan ta miƙe, ji tayi kamar ana kallon ta tayi saurin juyowa tana kallon gurin amma kafin ta kai ga ga juyowa har ya matsa.

Share hawayen ta tayi ta koma cikin gida tana dana sannin zuwa London ɗin.

Kitchen ta shiga ta wanke fuskar ta a sink ɗin wanke-wanke. Tana gamawa ta buɗe fridge ta sha ruwa me mugun sanyi ta ɗakko inibi tana turuwa huɗu-haɗu, uku-uku a bakin ta, wani kukan ne ya ƙara zuwan mata ba tare da ta shirya ba, zubewa ta ƙarayi a gurin tana cigaba da kukan ta, a dai-dai lokacin kuma Ummi ta shigo kitchen ɗin, da sauri ta ƙarasa tana rungume ta a jikin ta hankali ta a mugun tashe ta fara tambayar ta me ke damun ta.

“Suhaila me ya faru kike kuka haka? Ko wani abu aka yi miki?”.

Suhaila kuwa dama kaɗan take jira ta shige jikin Ummi tana ƙara sakin kuka, cikin muryar ta da ta fara dishewa tace; “Ummi gida nake so na tafi, don Allah ki kaini gida”.

Mamaki ne ya kamata sosai jin abunda Suhaila take tambayar ta, bata ce mata komai ba tayi ta shafa bayan ta tana lallashin ta, a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya alamar taci kukan ta har ta ƙoshu sai ka ce wata ƙaramar yarinya.

Kamata tayi ta kai ta palo ta zaunar da ita sannan ta dawo ta ɗaukar mata lemo me sanyi sosai ta zuba mata a cup ta kai mata, karɓa tayi ta sha kaɗan sannan ta mayar da cup ɗin ta ajiye, kallon Ummi tayi tace; “Kiyi haƙuri, amma ina so naje gida saboda abubuwa suna faruwa sosai kuma ya kamata ace ina can don na kula da komai”.

Murmushi Ummi tayi tana shafa kanta tace; “Ba komai, ni na ɗauke ki kamar ƴa ta ne kuma duk abunda kike so shi za ayi, amma ki ɗan bani lokaci kaɗan in Allah ya yarda zaki je gida nan ba daɗewa ba, akwai wani bikin ƴar wan baban su Kausar da za ayi, idan muka je sai ki je gida”.

Wani farin ciki ne ya ziyarce ta bata san lokacin da ta rungume Ummi ba tana mata godiya.

Ahmad da yake kallon su tun a kitchen yayi sallama yana shigowa cikin palon, zama yayi a kojera yana gaishe da Ummin nashi da mamaki take kallon shi ganin yadda fuskar shi ta faɗa ya rame sosai, ganin kallon da take mai yasa ya shigo da magana yana faɗin”Ummi na a bani abinci wallahi muguwar yunwa nake ji”.

Murmushi tayi tana mai nuni da dining, ba musu kuwa ya tashi ya nufi wajen yana zuba abinci, be wani tsaya ɓata lokaci ba ya fara ɗurawa cikin shi.

Suhaila kuwa sum-sum ta koma ɗaki, tana shiga ta tarar har Kausar ta tashi daga bacci ta dafe kanta alamar ciwo yake mata, da sauri Suhaila ta ƙarasa tana temaka mata ta shiga banɗaki don yin wanka bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin riga da wando tayi parking kanta ta ɗakko rigar sanyi ta ɗora a kai sannan ta sauka ƙasa.

Gurin Ummin nasu ta ƙarasa tana zama a kusa da ita ta kwantar da kanta a kan cinyar ta, tana hango shi daga can sai aikin danna waya yake daga gani wani aikin me mahimmanci yake yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button