ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Shafa kanta Ummi take a hankali kafin ta fara tambayar ta cikin nutsuwa don yau taga rashin walwala a fuskokin yaran nata.
Kamar daga sama Kausar tace; “Ummi don Allah kisa baki yaya Ahmad ya auri Zainab komai ya wuce, gidan nan ya dawo dai-dai, idan ba haka ba wallahi akwai matsala babba da zata kunno kai wacce sai ta fi abunda aka fuskanta a baya”.
Da mamaki Ummin take kallon ta jin abunda take faɗa bayan a baya itace kan gaba wajen zuga Ahmad ɗin ma.
“Me yasa kausar” Ta tambaye ta tana kallon fuskar ta.
“Kawai Ummi, ya kamata komai ya wuce”.
Saurin ɗagowa tayi ta kalli Ahmad ɗin taga su yake kallo yana jira yaji me za ta ƙara faɗa, wani long sigh ya sauke yana ƙara gyara zaman shi a jikin kujerar.
Suhaila kuwa tana ɗaki duk hankalin ta yayi gidan nasu, sai bayan sallar la’asar sannan ta iya tamabayar Kausar yadda za ta saka credit, recharging tayi musu through bank, bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta danna kiran numbern Abbun nata sai dai kashh numbern a kashe take, tunanin kiran Ammin nasu tayi sai kuma ta fasa, don tasan idan ta kira yau sai ta ƙare mata tanadi tass tukunna, tace ya bugo ya faɗawa uwar shi.
Tana ƙoƙarin ajiye wayar sai ga kiran Fatima ya shigo wayar tata bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta ɗau wayar tana karawa a kunnen ta nan da nan kuma hawaye ya suka cika mata ido kaɗan take jira kawai ta fashe.
Fatima ce tace ; “Kin ji abunda Abbu yake faɗa ko?”
Jikin ta har wani rawa-rawa yake tsabar firigici da tsoro.
Kukan da take riƙewa ne ya kufce mata, bata san lokacin ta da fara zazzaga mata bala’i ba”Haba ya Fatima meye amfanin ki a Nigerian ne? shikenan yanzu baza ki iya dakatar da Abbu ba, baza ki bashi haƙuri ba kan kar ya saki Ammi, sai dai kawai ki zauna ki naɗe hannu kina kallon su, kamata yayi ace kin tafi ƙafa da ƙafa ki nunawa Ammi abunda take yi be kamata ba fa, haba mana, sai yaushe ne zata girma? wallahi ko ni yanzu bazan yi abun da take yi ba, to wallahi na gaji, na gaji ya Fatima wallahi ki sanar da Abbu idan na barsu na barsu har abada, zan shiga duniya kawai nayi abunda nake so, tunda bani da mafaɗi iyayen mu suna raye amma basu da amfani a rayuwar mu sam, komai duk abunda yake faruwa rabi duk saboda nine, to zan basu guri su sha iska”.ɗut ta kashe wayar ta jefar da ita sai da tayi fatata ta koma pieces wanda ko moruwa baza tayi ba.
Fatima kuwa daga can ɓangaran baki kawai ta saki tana jin yadda ƙanwar tata take zazzaga bala’i kamar ba ita ba, abun ma har mamaki ya bata dama ance me hanƙuri be iya fushi ba.
Kausar ma da take gefan ta sakin baki tayi tana kallon ta, dama ta iya masifa haka? to me hakan yake nufi? kenan itama tana da issues da family ɗin ta.
A wannan karan kuwa Kausar ce ta koma lallashin Suhaila inda ita kuma take kuka baji ba gani, gaba ɗaya duniyar ta mata zafi, ta gaji da komai, ita idan banda kar tayi saɓo da ta nemi mutuwa da wannan rayuwar baƙin cikin da take ciki, tunda ta taso ko da yaushe a cikin baƙin ciki take, ta tsani kanta ta tsani komai nata, farko Ammin ta bata son ta, na biyu kuma anyi raping ɗin ta, na uku tayi shekara da shekaru ba tayi aure ba, na huɗu tayi auren mijin ya sake ta, na biyar ankawo ta ƙasar waje aikatau, ga iyayen ta sun kasa zaman lafiya ita ina zata saka kanta ne.
Da wainnan tunanukan bacci yayi awan gaba da ita, ba ita ta tashi ba sai bayan sallar magariba, Kausar kuwa sai da ta gayawa Ummi duk abunda taji Suhailan na faɗa a waya, nan taji tausayin ta ya ƙara dasar mata a zuciya ta kuma yi alƙawarin faranta mata ko ta wani hali.
Bayan tayi sallar magrib ta fito palo, tana zuwa ta haɗu da zainab ta ɗebo kayan wanki zata kai laundary a wanke mata.
Cillawa Suhailan tayi tana bata umarnin kaiwa masu wankin, ko ƙurar da kaso ta Suhaila bata kalla ba tayi ficewar ta abunta.
Ta kitchen tabi don tafi sauƙin zuwa library, sai dai tana fitowa zata wuce ta gurin flowers taji ruwa a fuskar ta zuwa jikin ta wata ajiyar zuciya ta sauke saboda sanyin ruwan, ga garin ya ɗau mugun sanyi don saura ƙaɗan snow ya fara sauka.
Sai da Zainab ta jiƙata tun daga saman ta har ƙasa, sannan ta jefar da tiyon da yake bawa flowers ruwa, ta kuma ƙara watso mata kayan tana faɗin”To ƴar gidan talakawa, matsiyata wainda basu iya cin arzuƙi ba daga kawo ki London sai ki fara ɗaga kai, to ki sani nafi ƙarfin haka a gurin ki wallahi, iyayen ki dai sunyi asara, kuma kwaɗayi shi zai kaisu ya baro su”.
Kwasan kayan Suhaila tayi kamar zata kai inda ta umarce ta tana zuwa ta watsa mata kayan, ta kuma ɗauke ta da mari, sai da ta yarfa mata huɗu kyawawa sannan ta ɗauki tiyon da be dena zubar da ruwa ba ta ɗaga shi a jikin ta har sai da ta jiƙe jagaff sannan ta hankaɗe ta ta wuce abun ta.
Zainab kuwa ji tayi kamar ta bindige Suhaila ga wani mamalolon baƙin ciki da take ji yana taso mata, cike da ɓacin rai ta shige cikin gida tana rawar sanyi.
Suhaila kuwa a haka ta tafi library wani mugun sanyi yana ratsa jikin ta.
Tana zuwa ta danna password ɗin ta shige, yau kam bata kai ga shiga cikin gurin littafan ba ta zube a ɗakin zanen tana sakin kuka, ga shi sai rawar sanyi take.
Ƙanƙame jikin ta tayi tana ƙara dunƙulewa waje ɗaya saboda yadda sanyin yake shiga jikin ta, har cikin ɓargwan ta take jin shi.
Murmushi ta saki tana tuno da Abbun ta, when she was 15 tana son shiga ruwan sama idan anayi, ko daga makaranta aka taso su idan ana ruwa Fatima zata fake amma ita sai ta shiga ruwa, kuma indai ruwa ya taɓa ta sai tayi zazzaɓi me mugun zafi, kuma bashi zai hana ta idan taga ruwa taƙi shiga ba, shi zai kula da ita ya bata magani ya rufa mata bargo, har sai da akayi raping ɗin ta rayuwa ta canza mata sannan ta dena wanka a ruwa.
Ahmad tun bayan la’asar da ya fita be dawo ba sai yanzu, be tsaya a ko ina ba sai libraryn shi, yana shiga ya jiyo sheshsheƙar kukan ta yana tashi lumshe idon shi yayi yana tambayar kanshi wai me yasa take wannan kukan ne, ƙarasa shigowa yayi ya hango ta ta rakuɓe guri guda sai rawar sanyi take, saurin ƙarasowa yayi da shirin yi mata magana, sai kuma ya tsaya yana tuno maganganun da Jibril ya faɗa mishi .
Zama yayi a jefan ta ɗan nesa da ita ya ciro special wine ɗin shi ya buɗe murfin yana kurɓa a hankali.
Jin motsin mutum yasa tayi saurin ɗagowa tana kallon shi, shi kuwa ko a jikin shi ya cigaba da sha.
Ganin tana mai kallon tuhuma yasa yace mata”Kar ki damu, nasan kin san ina sha, saboda ranar da muka a haɗu a nan har kika bani magani kin ganni sanda nasha.
“Me yasa kake sha?” ta tambaya muryar ta na rawa tsabar sanyin da yake ratsata.
“Saboda na rage damuwa ta, kuma bana son shan magani na saboda Kausar bata so”.
“Uhmm saboda hakan ne yasa ai tace bata so kana shan waincan magungunan, kuma ba wani damuwa da zata rage maka sai dai ma ta ƙara maka, we do have the same problem, ni meyasa bana sha? kuma me ya same ni?”
Kallon ta yayi yana mamakin maganganun ta yace; “Yana magani mana, sannan kuma wacce matsala muke da ita?”
“Family issues mana” ta faɗa kanta tsaye ba tare da tayi tunanin wani abu ba, sanna ta ƙara cewa”To nima ka bani nasha sai na rage matsala ta”.
Kafe ta yayi da idon shi me kashewa mutane jiki yace”Do we have the same problem? ”