ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Gyaɗa mai kai tayi tana faɗin” Don Allah ka dena sha, wannan ba abu ne mai kyau ba, baka tunanin yanzu idan Ummin ka ta gano kana sha itama tayi fushi da kai”.
Kallon hannun nashi yayi yana nazarin maganr ta “Kuma fa haka ne idan Ummin shi ta kama shi da wannan ɗabi’ar itama za tayi fushi da shi”. Rufewa yayi ya ajiye yana ƙara zuba mata idanun shi, cikin muryar shi me daɗin sauraro yace; “Kije ki canza kayan jikin ki kar sanyi ya kama ki, tunda wanan ce hanyar da kika zaɓa don calming kanki, you will catch cold and zaki sha wahala”.
Murmushin baƙin ciki tayi shi kuma ya miƙe zai wuce ɗaki yana ƙara juya maganar ta a ran shi.
Da ƙyar ta samu ta miƙe jikin ta yana rawa saboda tsabar sanyi ga wani mugun zazzaɓi da ya rufar mata lokaci guda.
Ta fara tafiya kenan taji kanta ya sara ta fara ganj biyu-biyu tana ganin dishi dishi. Zuciyar tace ta fara tashi inda cikin ta ys hautsine, komawa tayi ta zube a ƙasa tana furta”Wayyo Abbu na, ka temake ni zan mutu”.
Saurin juyowa yayi yana kallon ta ai da sauri ya ƙarasa gurin yana tambayar ta me ke damun ta ba tare da ya taɓa ta ba.
Wani amai ne yazo mata nan ta fara kwara shi babu shiri, tayi shi da yawa bayan ta gama sai kuma taji ɗan sauƙi sauƙi amma fa jikin ta ya mutu sosai don ko tafiya bata jin za ta iya yi, a hankali ta fara sulalewa zuwa ƙasa ta kwanata daɓas kamar wata matacciya, ganin haka yasa yayi saurin ƙarasawa yana bugun fuskar ta haɗe da girgiza ta.
*****
_*Ma’salam, Faɗma Ahmad*_
[7/24, 10:40 AM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*page5️⃣0️⃣to5️⃣1️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*_Glazed_*????
Girgiza ta ya cigaba da yi inda ba abunda take sai kiran sunan Abbun ta idon ta a kulle bata san inda kanta yake ba ma.
Saurin ɗaukan ta yayi ya nufi cikin gida da ita Ummi da Kausar suna zaune a Palo suna kallon tv ya shigo hankalin shi a matuƙar tashe.
Zainab kuwa da take sakkowa daga canza kayan da tafi tuntuni, ƙamewa tayi tana kallon yanda ya ɗakko ta kamar wata baby,wani baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta, inda take ji kamar taje ta shaƙe shi, don me yasa zai ɗau wannan ƙazamar bagidajiyar, komawa tayi cikin ɗakin ta don ta san idan ta tsaya ta cigaba da kallon su zuciyar ta zata iya fashewa. Ni kuwa nace da yafi miki Allah raka taki gona.
Cikin fargaba da tashin hankali Ummi ta taso da saurin ta tana ƙare musu kallo daga shi har Suhailan, da sauri Kausar itama ta ƙarasa gurin tana kallon yadda Suhailan take sauke numfashi da ƙyar, a tare suka jefo masa tambaya”Me ya same ta? ”
” Wallahi ban sani ba, abunda na sani dai na tarar da ita tana kuka a library sannan kuma a jiƙe take, to may be sanyi ne ya kama ta”.
Tashin hankali kwance kan Fuskar Ummi tace ; “Na shiga uku ni Ummukulthum, kar ƴar mutane ta mutu a hannu na, maza muje a kaita asibiti ai bamu ga ta zama ba”.
Da sauri suka hau sama suka saka kayan da zai rufe musu jiki sannan suka fito daga cikin gidan, kafin su kai ga fitowa har ya saka ta a mota.
Suna zuwa suka shige, Kausar ta zauna a gaba while Ummi ta shiga baya tana ɗora kan Suhaila akan cinyar ta tana shafa mata hannun ta da saurin gaske ko zai ɗan yi ɗumi amma ina hannun nata ya ɗau sanyi sosai kamar ƙanƙara.
Basu jima ba suka isa asibitin, suna zuwa aka karɓeta kasancewar inda Kausar take aiki suka je.
Shiga akayi da ita likita ta fara duba ta, inda aka cire mata rigar jikin ta aka sa mata sky bluen doguwar rigar marasa lafiya ta asibiti, allurar kashe sanyi akayi mata sannan aka sa mata drip haɗe da yi mata allurar bacci don ciwon da take ji, doctor na fitowa ta faɗa musu ai babu matsala komai ya dai-dai ta sanyi ne ya kama ta kuma dama jikin ta be gama sabawa da yanayin sanyin garin ba tunda wani zunubin har snow yana sauka, hankalin Ummi sai yanzu ya samu damar kwanciya, ana cikin haka Jibril ya kira wayar Kausar saboda yayi ta neman ta Suhaila bata shiga, tana ɗagawa ta mai sannu da hanya ya sanar da ita ai har sun isa ma amma basu daɗe da sauka ba, su Ummi ya tambaye ta ya suke sannan daga baya ya tambaye ta ina Suhailan yayi ta kiran numbern ta baya shiga.
Bata ɓoye mai ba ta sanar da shi ai Suhailan bata da lafiya yanzu haka ma suna asibiti, hankalin shi ne ya tashi sosai inda yake ji kamar yayi tsuntsu yazo inda take, Ummi ta miƙawa wayar suka gaisa sannan ya kashe wayar hankalin shi na sake tashi.
Suhaila bata farka ba sai wajen 11 ta tashi.
A hankali ta fara buɗe idon ta tana bin ɗakin da kallo babu abunda kake ji sai ƙarar warmer dake warming ɗakin.
Ɗan yunƙura tayi zata tashi amma sai taji kanta yayi mugun yi mata nauyi hannun ta ta kalla taga calola na ruwa alamar an saka mata ruwa kasancewar ruwan befi 2hours ba ya ƙare kuma bayan shi ba a saka mata wani ba.
Daɗa yunƙurawa tayi tana daɗa ƙoƙarin tashi cikin ikon Allah kuwa ta tashi zaune tana jingina da jikin ƙarfen gadon.
Ahmad ta tuno lokacin da yayo kanta da gudu, amma bayan nan bata ma san abunda ya ƙara faruwa ba sai yanzun da ta farka ta ganta kwance a ɗakin asibiti.
Bango ta fara kallo tana neman agogo, ai kuwa daga cen jikin wani edge na ɗakin ta hango wani ƙaramin agogo inda ya nuna mata ƙarfe 11 da mintuna biyar.
Ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idon ta ko sallah ma bata yi ba gashi bata jin za ta iya tashi daga inda take.
Tana cikin wannan tunanin aka murɗa luck ɗin ƙofar alamar za a shigo, a tare suka shigo duka su ukun, Kausar kuwa ganin Suhailan ta tashi tayi saurin ƙarasawa tana mata sannu haɗe ta tambayar ta ina ne yake mata ciwo yanzu ko a kira doctor.
Girgiza mata kai tayi alamar babu.
Ummi ce ta riƙo hannun ta tana faɗin”Daughter, ya jikin naki da fatan babu inda yake miki ciwo yanzu ko”.
Gyaɗa mata kai tayi, saboda baza ta iya magana ba wani yawu ne ya tarar mata a baki.
Shi kuwa Ahmad kallon ta kawai yake yi, saboda ko ɗankwali babu akan ta ga gashin kanta baƙi wuluk, idanun ta duk sun faɗa sai suka ƙara fitowa sosai, fuskar ta tayi fayau, sai tafi kyau ma a hakan.
Ɗago ido tayi nan suka yi two eyes da shi saurin sauke idon shi yayi yana matsawa daga jikin ƙofar ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun. Nuni tayi da bakin ta inda Kausar ta gane abunda take nufi temaka mata tayi suka ƙarasa bakin ƙofar banɗakin, suna zuwa ta zubar da yawon da yake bakin ta kallon kanta tayi a mudubin gurin sai yanzu ta fuskanci dalilin da yasa Ahmad yake kallon ta ashe ko ɗankwali babu a kanta uwa uba ma har bra sai da aka cire mata daga ita sai rigar asibitin, wani haushi taji ya kama ta, shiyasa yake kallon ta kamar wani tsohon maye”Mtsswww”. ta ja tsaki tana jin haushin shi a cikin ranta.