ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Dawowa suka yi cikin ɗakin suna fitowa ta ƙara kallon shi nan suka ƙara haɗa ido, harara ta galla mai tana jin kamar taje ta shaƙe shi, shi kanshi he is not comfortable.
“Kausar i need something da zan rufe kaina, ina kaya na suke?”.
“An shanya, bari na duba ko sun bushe”.
Kallon su yayi ya cire mofular wuyan shi, sannan ya zame coat ɗin da take saman kayan shi ya miƙawa Kausar yace; “Bata wanan ta fara amfani da shi, akwai sanyi da yawa, sannan kuma ki tambaye ta me zata ci”.
Karɓa tayi ta ɗaura mata mofular a kanta sannan ta saka mata coat ɗin.
Bata tashi jin yunwar ba ma sai da taji ya ambaci abinci.
Tambayar ta Kausar tayi ta girgiza mata kai tana faɗin”Bazan iya cin komai ba fa”.
Kallon shi Kausar tayi alamar kaji abunda tace ai.
“Haba dai ki sake tambayar ta, akwai abinci kala-kala fa, ko akawo mata snacks?”
Girgiza kai ta ƙara yi alamar aa.
“Haba dai har snacks ɗin kamar su pizza, samosa, spring roll, shot cake, meat roll, meatpie, stir-fry chicken, glazed doughnut duk babu wanda zata ci a ciki?”
Ɗan kallon Kausar tayi tace”Glazed dought ma ya isa”.
Murmushi yayi yana kallon su inda Ummi itama ta saki baki tana kallon abunda suke yi, idan banda Jibril ya rigashi ai da taji daɗin haɗin da tayi niyar yiwa ɗan nata abun ƙaunar ta.
“Ɓangaren drinks fa?”ya tambaya yana kallon fuskar Kausar, itama saura kaɗan ta kwashe da dariya sai kuma ta dake wai bazai mata magana da kanshi ba sai ya dinga wani gocewa.
Girgiza kai tayi alamar aa.
Kallon ta yayi ta gefan ido yace;” Haba mana Kausar akwai drinks kala-kala wanne take so milk ko juice?”
Bata san sanda bakin ta ya furta Milk ba.
Dariya yayi yana wa Kausar nuni da hannu alamun tazo su tafi tare, sallama sukayiwa Ummi sannan suka fice abun su, bayan sun fita Hajiya take sake tambayar ta ya jikin nata da sauƙi ta amsa mata tana sunkuyar da kanta.
Riƙo hannun ta Ummi tayi tasa shi cikin nata tana shafawa a hankalin kafin ta fara magana “Kiyi haƙuri kinji ko, su Jibril suna dawowa in sha Allahu za mu tafi gaba ɗaya, don Allah ki kwantar da hankalin ki zaki koma gida, nafison ki koma yadda muka taho da ke ba na so wani abu ya same ki sam, saboda ke amana ce a guri na kuma ban ɗakko ki don ki bauta mun a matsayin me aiki, sai don wani buri na da nake so kuma Allah be yi ba, amm duk da haka tunda kun fahimci juna da Jibril muna zuwa sai ayi zancen auren ku indai har kin yarda, kafin mu dawo za ayi magana komai da komai, a ɗaura auren ma sai mu dawo tare”.
Sunkuyar da kai Suhaila tayi ba tare da tace komai ba, su Ahmad da suka dawo daga siyo glazed doughnut duk abunda Ummi ta faɗa a kunnen su, haka kawai yaji maganar wata iri, haka kawai yaji wani haushi ya kama shi, ko na meye oho mai, haɗa ido suka yi da Kausar ta ɗaka kafaɗa tana buɗe ƙofar, a tare suka shiga inda Ummi ta zuba musu ido tana kallon yanayin su, Ahmad ta zurawa ido tana jin son shi yana ƙara shiga jikin ta, ba ruwan shi, komai nashi cikin nutsuwa yake yin shi, ga ladabi da biyayya duk abunda tace shi yake yi, yana son ƴan uwan shi, baya taɓa nuna banbanci tsakanin shi da Jibril kamar yadda itama ko yaushe take ƙoƙarin haɗa kan yaran nata, bata son su zamto kanso a ware yake saboda ba uwa ɗaya suke ba, amma shi Abbun su har yanzu ya kasa ganewa tunda Hajiya Rabi’a (kishiyar Ummi) Allah ya mata rasuwa yake ganin kamar shikenan sun shiga uku sun lalace, yake ganin kamar Ummin baza ta yi abunda ya dace ba, shi ko tunanin amanar da ta bashi baya yi koda yaushe cikin ƙunci yake, baya son ta baya son ƴaƴan ta, duk zaman lafiyan da sukayi da ƴar uwar zaman ta da so da ƙaunar da suka nunawa junan su be sa ya fuskanci Ummin ba, ko da yaushe ba ta da burin da ya wuce taga ta farantawa Aisha da Jibril ta haɗe kansu da Ahmad da Kausar amma ina ya kasa fahimta gani yake kamar itace sanadi, gani yake kamar saboda ita Rabi’a ta rasu ya kasa ganewa ya kuma kasa yin haƙuri, bayan kafin ta mutu saida tace mai kar ya sake ya raba musu kan ƴaƴan su da rashin fahimtar su amma ina, ya kasa ganewa, sai da ta nuna mai koda yaushe dangin shi basu da buri da ya wuce suga sun haɗa su faɗa saboda yadda suka zauna lafiya kamar ba kishiyoyi ba, amma ina daga ƙarshe bayan Rabia ta rasu sai da suka san yadda suka yi suka haɗa ta da Dadday kasancewar kowa yasan irin son da yake mata da kuma ƴaƴan ta, ita kuwa Ummi har yanzu yana zaune da ita a bisa sharaɗin hajiyan sa ne da tun kafin ta mutu ta sanar da shi indai ya rabu da Kulthum baza ta taɓa yafe mai ba.
Wainnan tunanukan ne suke ta yawo a ranta, yadda ta banzatar da ɗanta akan ƴaƴan ƴar uwar zaman tata, yadda ta nuna su ba komai bane, duk abunda Jibril yake so shi take yi bata taɓa yi mai baƙin ciki, ko wasu abubuwan da yake yi sai dai kawai ta kawar da kanta tayi kamar bata gani ba don a zauna lafiya, kuma ta san harda sa hannun Daddyn nasu saboda shi yake nuna mai yafi son shi akan Ahmad ɗin, yar Jibril ma Aisha wadda daga ita sai Jibril bata son abunda Daddyn nasu yake yi sam tafiso taga kan su ɗaya kamar yadda Umman su take so.
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubar mata, da sauri ta tashi ta fita daga ɗakin inda Ahmad ya sun kiyar da kanshi ƙasa saboda yasan kukan me take yi, kujerar da ta tashi ya janyo ya zauna a kai yana buɗe abunda suka shigo dashi hankalin shi na kan Ummin nashi amma so yake ya bata lokaci ta ɗan huta kafin sai yaje ya rarrashe ta.
Hilarious face ɗin ya saka yana miƙawa Kausar box ɗin glazed doughnut da suka shigo da shi yana faɗin”Ki bata ta ci sannan kuma ga milk ɗin ta ni kuma zan sha juice ɗina”. Ya faɗa yana kallon Suhaila ta gefan idon shi, karɓa tayi ta fara ci a hankali inda ita kuma Kausar gaba ɗaya hankalin ta na kan Ummin ta, tashi tayi ta fita da sauri tana neman ta.
Ɗakin shiru yayi kamar ruwa ya cinye inda babu abunda kake ji sai ƙarar warmern ɗakin kallon ta yayi yace; “Cogartulations, nayi farinciki da naji kece zaki auri ɗan uwa na, fata na Allah yasa ki iya kula da shi”.
Ɗan kallon shi tayi tana jin gabanta yana faɗuwa saurin sauke idon ta tayi saboda kwarjinin da yayi mata.
Cikin zuciyar ta ta amsa da Amin, inda ta cigaba da taunar doughnut ɗin ba tare da tace komai ba, sai da akayi kamar 10 seconds sanan tace; “Thanks”.
Kallon ta yayi yace; “For what mrs Jibril?”
Ɗan murmushi tayi tana mamakin addesh huwa hanoon.
“For helping me earlier”. Ta faɗa tana kallon cikin idon shi, shima kallon ta yake yi yana jin wani abu da be taɓa ji ba a rayuwar shi.
A lokaci ɗaya suka ɗauke idanun su daga cikin na juna, a dai-dai wannan lokacin kuma nurse ta shigo ta duba ta inda take faɗa mai she is fine ko yanzu za su iya tafiya gida.
Bayan nurse ɗin ta fita ta kalle shi tace; “Me ya sa Ummi take kuka ɗazu?”
Yayi mamakin tambayar sosai hakan ne yasa ya ɗan yi shiru.
“Allah yasa dai ba ganowa tayi kasha wine ba, don naga tana kallon ka ta fara kuka”.
Saurin ɗora hannun shi yayi a bakin shi yana faɗin “Shshitt, kar ki ƙara faɗan haka ba wanda yasan wannan sirrin nawa sai ke kuma a hope ko Kausar baza ki sanar da ita ba”.
Gyaɗa mai kai tayi tana faɗin”To ka dena idan ba haka ba wata rana zata gane”.
*****
A ɓangaren Kausar kuwa a veranda ta hango Ummi da sauri ta ƙarasa tana rungume ta, itama rungume ta tayi, duƙushewa suka yi suna sakin kuka a tare sai da suka yi me isar su ba wanda ya iya lallashin wani sai daga ƙarshe Kausar ta share mata hawaye tana faɗin”Haba Ummi na, wani zubin kina daɗewa baki shiga damuwa ba amma duk sanda kika tuna bakya iya daurewa”.