HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Shhhhh” ta faɗa tana rufe mata baki”Ya isa haka bana son maganar ma, ya wuce tashi ki koma ciki kinji ko”.

Suna tashi suka hango shi a tsaye yana kallon su, da sauri ya ƙaraso ya haɗa su gaba ɗaya ya rungume su tsam a jikin shi yana shanye ƙwallar da take son zubo mai.

Rabasu yayi da jikin shi ya gogewa Ummin shi hawayen da har yanzu be dena zuba ba yana girgiza mata kai.

Goge hawayen tayi tace”Shine kuka baro ƴar mutani ita kaɗai a ciki, ka koma gida dare yayi ka ga yanzu to 1″.

“Ummi na dama zuwa nayi na sanar muku kozo mu tafi gida don Suhaila ma tana mota”.

“Mu tafi to”. ta faɗa tana riƙo hannun su gaba ɗayan su.

Tundaga nesa Suhaila ta hango su, sun burge ta sosai, shigowa su kayi ya tayar da motar inda Ummi take ƙara tambayar ƙarfin jikin ta.

Tundaga nan ba wanda ya ƙara magana har suka isa gida kowa da abunda yake tunani.

Ahmad be shiga gida ba ya wuce part ɗin shi don yayi wanka, su kuma suka shige cikin gida, banɗaki Suhaila ta shiga tayi alwala sannan tazo ta kabbara sallah, bayan ta idar da isha’i ta ɗora da nafula duk da jikin nata har yanzu da ɗan saura amma haka ta cigaba da ibada tana kai kukan ta zuwa ga mahallicin sammai da ƙasasai don shi kaɗai ne zata iya kaiwa kukan ta, bata yi bacci ba har 3:30.

A ɓangaren Jibril kuwa da ƙyar ya samu yayi bacci saboda damuwar da ya shiga.

Ahmad kuwa yana zuwa part ɗin shi ya shiga toilet ya haɗa ruwa masu ɗumin gaske a bathtube saboda ya ɗebo sanyi, sai da ya gasa jikin shi sosai sannan ya ɗauraye jikin shi a shower ya fito ya saka kayan bacci sannan yaja blanket ɗin shi me shegen ɗumin gaske, bacci yayi awan gaba da shi.

Da misalin ƙarfe biyar na asuba, kwance yake yana bacci yayin da saman goshin shi sai gumi yake fitarwa duk sanyin da akeyi daga gani mafarki yake yi. Da sauri ya tashi ya buɗe idon shi yana sauke wani numfashi sai kace wanda yayi gudu, a dai-dai lokacin kuma agogon shi ya buga, saurin sa hannun shi yayi yana kashe alarm ɗin, lumshe idon shi yayi ya buɗe yana faɗin”What is the meaning of this, why Suhaila now?”

Tashi yayi ya shiga banɗaki yana tunanin abun a ranshi me yasa yau a mafarkin shi yaga fuskar Suhailan yana saduwa da ita, ko don event ɗin da suka faru a tsakanin su ne jiya.

All what he knows yana yin irin mafarkin nan kusan ko da yaushe which is normal ga ko wani ɗa namiji wani zubin ma harda matan, amma me yasa yau zai ga fuskar Suhailan.

Girza kai yayi yace ; “Shaa, koma dai miye ne zaka iya irin wanan mafarkin, but ganin fuskar ta yana da nasaba da abunda ya faru jiya”.

Da wannan tunanin yayi alwala ya fito ya tayar da sallah ba tare da ya ƙara sa wani tunanin a ranshi ba….

*******

_*Ma’asalam… I luv you all my people, face book readers, whatapp reader’s, wattpad reader’s heart you guys thanks for ur comment*_

_*Faɗma Ahmad*_
[7/25, 3:30 PM] Aunty Sumie: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page5️⃣3️⃣to5️⃣4️⃣*

 

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*Addu’a ga wanda ya gabatar maka wani abu daga Dukiyarsa:*

بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي أَهْلِكَ وَمَاِلكَ.

Barakal lahu laka fi ahlika wa malika.
Allah Ya yi maka albarka a cikin iyalinka da dukiyarka.

*Dedicated to Golden pen writer’s association*

 

_*Phone call*_????

Bayan ya idar da sallah ya janyo ƙur’anin shi ya fara karantawa a hankali cikin muryar me zaƙin gaske, bayan ya gama kuma ya fara karanto azkar subih, jin shi yayi wasai saboda rabon da ya zauna ya bada hankalin shi haka ya nutsu har ya manta, wato home sweet home, duk inda ka bar gida shima ya barka.

Suhaila kuwa a dai-dai lokacin da ta saba tashi ta buɗe idanun ta, shiga tayi banɗaki da zummar yin alwala sai kuma taga period hakan yasa tayi wanka ta saka pad, sannan ta dawo ɗakin don tashin Kausar tayi sallah, yanzun kam idan da sabo har ta saba, alwala ta ɗoro tazu ta kabbara sallah inda suhaila ita kuma ta fara karƙaɗe gadon.

Bayan ta gama ta wuce zuwa kitchen don bata so taje ta tarar da Ummi tana haɗa breakfast, doya ta ɗakko ta fere, bayan ta gama slicing nashi ta ɗora shi a wuta don ya dahu, kafin doyar ta dahu ta fasa ƙwai ta kaɗa shi ba tare da tasa mai komai ba hakan ne zai sa ya kama doyar sosai, sai albasa da ta yanka saboda ƙarni, bayan doyar tayi kamar rabin dahu ta ɓoɗe ta barbaɗa maggi know a ciki ta mayar ta kulle, doyar na ƙarasa dahuwa ta sauke ya tsane a sifter, kafin ya ƙarasa tsanewa ta yanka Tomato da pepper da dai sauran vegetable da take buƙata a sauce ɗin da za tayi, soya doyar tayi, bayan ta gama tayi sauce ɗin ta yanka hanta ƙanana ta saka a ciki, tuni gidan ya ɗau ƙamshi inda kowa yake baza hanci, bayan ta gama sauce ɗin ta ɗora tea ta saka duk wani kayan ƙanshi, cinnamon, cloves black paper, na’a-na’a da kuma lemon grass, wayyo Allah na wannan spicy tea zai haɗu kamar a bani nasha amma babu dama.

Daga gefe kuma ta kunna coffe maker tayi ta haɗa coffe ko akwai wanda ze buƙata.

Bayan ta gama ta ɗakko pure oranges masu kyaun gaske ta kunna juicer ta matse su sannan ta samu plate ta jera fruit game buƙatar ci.

Jera komai tayi a dining, ta ɗakkowa kowa plate ta ajiye shi a mazaunin su.

Tana cikin haka Ummi ta sakko, kallon ta ta tsaya yi ganin ta jera dining ga wani ƙamshi me daɗi da yake tashi.

“Ohhh ni Ummkulthum! yanzu Suhaila har kinyi warkewar da kika yi wannan aikin?”

Murmushi tayi tace; “A haba Ummi naji sauƙi babu abunda yake damu na wallahi, dama cewa nayi bari yau na rigaki sakkowa saboda karkizo ki kama hidima da safennan alhalin akwai me yin hakan a gidan”.

“Allah ya miki albarka”. Hajiya ta faɗa tana faɗaɗa murmushin ta.

Ɗan sunkayar da kanta Suhaila tayi tace; “Amin”. tana ƙara gyara yanayin zaman cups da spoons da suke kan dining.

“Bari na na kira Kausar”. Ta faɗa tana ɗaukan hanyar sama.

“Okay bari na kira Ahmad na sanar da shi breakfast is ready”.

Daga bayan ta taji muryar shi yana faɗin”Gani nan Ummi na, wannan ƙamshin abincin ai ya hana ni sukuni, dole na taso dama ciki na kiran ciroma yake”.

Ya faɗa yana zama akan dining ɗin haɗe da fara janyo warmers zai fara buɗewa.

Ummi ce tayi saurin buge hannun shi tace ; ” Malam dakata, ba yanzu ba tukun sai kowa ya sakko uban ƴan ci, mara kawaici akan abinci”.

Sosa ƙeya yayi yace; “To me za a tsaya jira fisabillilahi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button