HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Suna haka sai ga ƴan matan gidan sun sakko, Kausar da Suhaila ne a gaba sai hajiya Zainab daga bayan su, sai wani cin magani take. Duk ta gaji da zaman gidan saboda baƙin cikin da ake ƙulla mata, musamman Ahmad da ta fuskanci wani abun ma da gayya yake mata.

Guri suka samu suka zauna inda Suhaila ta tashi ta fara zubawa kowa abinci, Ahmad ne na ƙarshe bayan ta gama zuba mai ya kalle ta yace ; “Haba sai kace wani ɗan tsako, Zainab ki faɗa mata wannan yayi mun kaɗan”.

Kwashewa suka yi da dariya, inda itama Suhaila tayi dariya cikin zuciyar ta tace ; ” Bari na nuna maka nima na iya tsokana”.

Kallon Zainab ɗin tayi tana faɗin” Ki faɗa mishi ya fara cinyewa dai, kar a cika mishi yayi mana asarar abinci”Ta ƙarashe maganar tana zuba mai juice a kofi.

Ɗagowa yayi ya kalle ta inda Ummi itama ta kalle ta tana mamakin dama Suhailan zata iya magana irin haka.

Zainab kuwa ji tayi kamar ta shaƙe ta, “Wato har ta samu gurin da za ta iya wasa da abun ƙaunar ta, na san me zanyi, sai kin san baki da hankali”.

Fork ta ɗauka ta fara cin doyar ta inda ta fara tunanin wani mataki zata ɗauka akan Suhailan.

Kausar kuwa cewa tayi”Good my aunty, haka nake so ki fara nuna mai true color ɗin ki.

Murmushi tayi ta samu guri ta zauna inda shi kuma har yanzu be dena mamakin amsar da ta mayar mai ba.

A hankali cikin nutsuwa kowa yake cin abini shi, inda a dai-dai wannan lokacin wayar Kausar ta fara ƙara, kallon wanda yake kiran tayi nan taga Jibril ne, miƙawa Suhaila tayi tana faɗin”Ungo, duk yabi ya dameni tun jiya yake kira, gaskiya kizo ki samo waya don bazan iya da wannan lamarin naku ba, don ni za’a takurawa”.

Harar ta Suhaila tayi tana ƙin karɓar wayar wai ita tanajin Kunya.

Ganin kunya take ji yasa Ummi tace; “Karɓi mana”. Karɓa tayi ta tashi a gurin, inda Ahmad yaji wani abu ya tsarga Mishi a cikin zuciyar shi wanda besan menene ba.

Kitchen ta shige tana ɗaukar wayar”Hello Hanoon (kind one)”.

“Baby”Ya faɗa yana relaxing a kujerar office ɗin da yake zaune jin muryar ta sayau babu wani damuwa ko alamar tayi rashin lafiya.

” Baby are okay?”da fatan kin warke babu wani abunda yake damun ki yanzu ko?”

“Hanoon am okay, am fine babu abunda yake damu na, daman sanyin garin ku ne, kuma yanzu Alhamdullilah komai yayi dai-dai naji sauƙi sanyin ma babu”.

“Haka nake son ji, kiyi haƙuri ko, nayiwa Daddy maganar mu jiya da daddare yace indai kinyi mun kuma ke na zaɓa a matsayin matar aure yana dawowa za ayi maganar bikin mu”.

“Allah ya kaimu da rai da lafiya, ka kula da kanka please, bari na koma cikin gida anjima zamu yi waya”.

“Kema ki kula da kanki, Allah ya kaimu to. Wai ina wayar ki ne?”

“Ta samu matsala ne, amma zan samu wata soon”.

“Zanyiwa Kausar magana sai a kawo miki sabo, just take care, bye love you”.

“Love you too, bye”.

Kashe wayar tayi inda tana juyowa zata bar kitchen ɗin suka yi ido huɗu da Ahmad ga plates a hannun shi wanda hakan yake nufin da ya gama cin abincin shi.

Gaban ta ne taji ya faɗi ganin irin kallon da yake mata, sunkayar da kanta tayi tana ƙoƙarin fita a kitchen ɗin.

Har ta kai bakin ƙofa, taji yace”Hanoona, thanks da girkin da kikayi mana, yayi daɗi sosai”.

Kallon shi tayi tana mamakin kalmar da ya faɗa, “Yasan ma’anar ta kenan ko dai kawai zolayar tashi ce”.

“You are welcome”. Ta faɗa tana barin kitchen ɗin gaba ɗaya.

Ajiye plates ɗin yayi ya wanke hannun shi, ya kuskure bakin shi yabi ta ƙofar kitchen ya koma part ɗin shi ranshi babu daɗi sam.

A hanya Suhaila sai tunanin kalmar Ahmad take a ranta inda take tunanin me yasa yake mata irin wannan kallon, meye dalilin shi nayi hakan don yaji tana waya da Jibril. Bata kawo komai a ranta ta ba ta cigaba da sabgar gabanta.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har na tsahon sati guda, inda Suhaila ko da wasa bata nemi ƴan gidan su ba, kuma hakan ba wani damun ta yayi ba, saboda tasan zuwa yanzu komai ya wakana, to me zataji idan ba ɓacin rai ba gwara kawai ta haƙura har sai ta koma inyaso duk abunda taje ta tarar ta fuskance shi a lokacin, amma ina sam zuciyar ta ƙi bata haɗin kai musamman ma idan ta tuna irin damuwar da Abbunta zai shiga.

Ita da Jibril ko da yaushe a manne suke a wayar Kausar saboda har yanzu ba a kawo mata wata ba.

Inda ita da Ahmad suke sake sannin junan su, kuma suka fara sabawa na ɗan wannan lokacin da guard ɗin ta baya nan.

Ita kuwa Zainab har yanzu tunanin irin haɗin da za tayiwa Suhaila take, so take ta haɗa mata tugun da yafi ƙarfin ta.

Ni kuwa nace kar dai kije garin neman gira a rasa ido.

Kausar kuwa ko da yaushe tana hanyar zuwa gurin aikin ta, yayin da shaƙuwar da take tsakanin ta da yayan ta, ta ninku akan ta baya, Ummi kuwa ji take kamar wannan karan za ayi batakashi don baza ta iya rabuwa da shi ba a karo na biyu wanda sai da ya ɗibi shekaru kafin ta sashi a idon ta.

Zaune take a garden ita kaɗai, inda babu abunda kake ji sai kukan tsuntsayen gurin, ga iska me daɗi da take kaɗa ko wanni fire da yake cikin gurin. Sanye take cikin doguwar riga abaya, ash inda tayi rolling da mayafin abayar daga sama kuma ta ɗora rigar sanyin ƙulu dark ash,hankalin ta gaba ɗaya yana a kan rubutun da take yi, inda idean rubutun nata a lokacin ne yake sakko mata shiyasa ta nutsu ta kuma mayar da hankalin ta gaba ɗaya akan abunda take rubutuwa.

A hankali ya shigo cikin garden ɗin yana kallon yadda take komai cikin nutsuwa, da yadda ta bawa rubutun hankalin ta gaba ɗaya.

Zuwa yayi ya zauna kusa da ita, bata ankara ba sai jin ƙamshin turaren shi tayi.

Saurin ɗagowa tayi suka yi four eyes da shi, inda ya sakar mata murmushin shu me kashe mata jiki. Littafin tayi saurin rufewa tana ajiye shi a gefe haɗe da zuba mai lulu eýes ɗin ta.

Cikin yanayin rashin gaskiya tace; “Yau baka je Washington bane?”

“Eh banje ba saboda bani da aiki, ko da yake bazance bani da shi ba, wani case ne nake da shi me rikitarwa wallahi, ina da tabbacin abunda ya faru amma kasancewar bani da sheda ko ɗaya yasa jiki na yake sanyi, i dont know what to do, ni da ragowar team ɗina kuma koda manyan mu sunsan hakan ne idan bamu kawo musu hujja ba a banza wallahi”.

“Hhhh”, ya sauke long sigh yana kallon ta kafin yace; “Bama wannan ba, wai me kike rubutuwa ne? wanda sai kin samu guri shiru kike rubutuwa? haka ranar na ganki a library kika ɓoye, is it a deary or what?”

“Ba diary bane”. ta bashi amsa kai tsaye babu wani tsoro a tattare da ita.

“Ohhh ai nazaci shine, ince ba abunda zai ja miki sai ɓacin rai saboda duk sanda wani ya ɗauka ya duba wanda baki so hakan ba sai kinji kamar ki faɗa rijiya”.

Dariya tayi tana faɗin”You are funny”.

Ɗan shiru ne ya ratsa gurin kafin yace; “Baza ki kira shi ba?”

“Who?” ta faɗa tana kallon shi.

“Your Dad mana, he must be worried about you, just forget and call him, and i asure you ba abunda ya faru tsakanin su”.

Wayar shi ya ciro a aljihu ya miƙa mata yace; “Just call, ki dena punishing kanki”.

Cikin sanyi jiki ta karɓi wayar ta danna numbern Abbun nata, yana office ɗin shi a makaranta yana ganin kiran numbern waje, ai da sauri ya ɗauka don yasan bazai wuce Suhailan tashi ba.

“Mama na” Ya faɗa hankalin shi a mugun tashe.

“Abbu na”.

“Wallahi ban saki Ammin ki ba, tana nan a gida muna tare da ita, kar ki ƙara fushi da ni irin haka kinji ko bazan taɓa yin abunda bakya so ba, ke uwa ta ce kuma Abunda uwata tace shi zanyi”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button