HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Kallon Ahmad tayi idon ta duk ya ciko da ƙwalla, girgiza mata kai yayi yana ɗaga mata kai alamun tayi magana.

“Abbu na, kayi haƙuri, bazan sake ba, ka yafe ni, da fatan kana lafiya ko? Farida, Mubarak, Ammi, kowa lafiya ko, i miss you so much ka yafe ni, waya na ya lalace amma soon zan siyi wani koda zaka jini shiru”.

“Mama na kowa lafiya lau, babu matsala indai baza ki ƙara fushi da ni ba, ki kula da kanki, ki kirani anjima yanzu ina da meeting da malamai”.

To ta amsa mishi da shi tana kashe wayar haɗe da miƙawa Ahmad wayar shi, sai yanzu wani kuka me cin rai ya kufce mata bata san sanda ta fara kukan ba.

Kallon ta yayi yana jin wani iri a jikin shi, jin ta kawai yayi ta faɗa saman kafaɗar shi tana cigaba da kukan ta, tausayin ta yasa ya rungumota tsam a jikin yana lallashin ta, a dai-dai lokacin kuma Zainab da take biye da shi tunda ya shigo garden ɗin ta ɗauke su a hoto, tana sakin wani shu’umin murmushi, yayin da wani ɓangare na zuciyar ta take ji kamar tashaƙeta saboda kishin Ahmad ɗin da ya taso mata……

******

*_Tofa hajiya Zainab ku me zaki ƙulla da wannan picture da kika ɗauka oho sai a next page dai za muji_*

_*Asalama alaikum, Faɗma Ahamd*_

[7/26, 10:56 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page5️⃣5️⃣to5️⃣6️⃣*

 

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

*Idan dayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, sai ya ce;*

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.

Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha ‘alayh, wa-a’oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha ‘alayh.

Ya Allah ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi’antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi’antar da ita a kansa.

Idan kuma ya sayi rakumi, to ya kama tozon rakumin ya fadi kwatankwacin wannan (addu’ar).

*_Hypocrite_*

Rungume wayar tayi a ƙirjin ta tana daɗa sakin shu’umin murmushi wanda ita kaɗai ce tasan ma’anar shi, barin gurin tayi yayin da take ji kamar zuciyar ta zata fashe tsabar baƙin cikin rungumar da Ahmad yayiwa Suhailan.

Kusan 5 minutes suka ɗauka a haka inda shine ya fara ƙoƙarin raba ta da jikin shi yana me daɗa bata haƙuri, saurin barin jikin nashi tayi da ta ankare da abunda ta aikata ba tare da ta sani ba.

Ɗan kallon ta yayi yace; “Shagwaɓaɓɓiya kawai, daga magana da Dad har kin wani fara kuka”.

Ɗan murmushi tayi tana goge fuskar ta, taji daɗin kasancewa da shi yau, ya bata damar magana da Abbun ta wanda a lokacin bata da tsarin yin hakan.

“Am sorry for what i did, i was out of control”.

“Ba komai”.ya faɗa yana kallon kyakkyawar fuskar ta.”Ɗan uwa na yayi dacen samun mata”.

Kallon shi tayi tana dariya tace; “Ko?”.

“Yes”. Yace yana basar da maganar.

Juyowa tayi ta kalle shi kafin a hankali ta fara magana”Ammm, ɗazu me kake cewa akan case ɗin ka ma, naji kace kun kasa samun evidence kuma kuma da tabbacin abunda ya faru”.

Gyaɗa mata kai yayi yana juya wayar da take hannun shi.

“Ummm, Baban wani mutumin mu ne akayi mudering nashi, wanda da yana amfani da drugs na a mutu, ko da yaushe a cikin maye yake, amma tunda muka haɗu da shi aka kaishi Rehab(guri ne inda ake kai mashaya don kula da su, ko da sun samu taɓin ƙwaƙwalwa ko kuma sun zama addicted to shayeye wanda basa jin za su iya denawa). To tun daga nan sai ya warke ya kuma dena, indai bawai asha don jin daɗi bane tunda kin san su baza a raba su da shan ko da wine bace”.

Gyaɗa mai kai tayi tana maida hankalin ta gaba ɗaya kan labarin da yake bata.

“So maman shi ta mutu, a gurin step mom ɗin shi ya girma inda ita kuma tazo da wani ɗan gidan baban shi, tunda baban shi ya aure ta ya shiga wani yanayi, aka dena bashi kulawa ko da yaushe, sai tace tana kula da shi don kawar da hankalin baban amma kuma ƙarya take yi, daga baya da ya fara tasowa sai ta fara sa mai ƙiyayar yaron a zuciyar shi, shi kuma da ya fuskanci haka kawai sai ya bar gida yaje ya haɗu da irin gang ɗin nan na marasa ji masu addabar mutane, sune club, sune harkar mata, ko wani hotel suna nan a haka har suka buɗe wani bar, inda muka aka bamu har kar binciken gurin a hannun mu har muka haɗa hannu da ƴan sanda aka yi kame inda aka kai su rehab su huɗu amma su biyu suka warware inda sauran suna can har yanzu”.

Long sigh ya sauke ya cigaba da bata bayani”So last week his father was dead, amma kafin ya mutu sai da ya mai voice record na messege ya tura mai, inda yake neman gafarar shi yace mai tabbas ya yadda da cewar yayi wrong choice da ya zaɓi Sara a matsayin abokiyar zaman shi, yace mai kuma poisoning ɗin shi aka yi, sai dai kuma be gaya mai wanda yayi poisoning ɗin ba, koda muka kai wannan voice record a matsayin shaida sai aka ce mana ai be faɗi suna ba don haka ba mu da tabbacin itace, kuma da aka gwada shi a asibiti ba wani poisoin a jikin shi, to kinji abunda yake faruwa”.

Ɗan shiru tayi kafin ta numfasa, kallon shi tayi tace ; “As a psychologist…”.

Saurin ɗagowa yayi ya kalle ta yace; “Mene! Kina nufin kice mun ke psychologist ce?”

Gyaɗa mai kai tayi yayin da ta kawar da maganar shi tana cigaba da faɗin “Abunda ka faɗa tabbas gaskiya ne itace ta kashe shi amma baku da evidence wanda za a yarda da ku, but kunje gidan kun caje komai babu wani sign na poisoin ko wani abu suspicious”.

“Babu”. ya faɗa yana sunkuyar da kanshi” Kun tabbatar babu”.

“Babu Suhaila”.

Ɗan shiru yayi yana wani nazari kafin ya kalle ta yace; “But akwai wani garden nata babu abun da yake ciki sai different followers, kuma shima mun duba, mun duba amma babu komai a ciki wallahi”.

“Flower garden?”

“Yes” ya faɗa yana kallon ta.

“Zaka iya faɗa mun irin flowers ɗin da ke ciki?”

“Uhmm wani amfani ma za su yi, amma bari na kira Daniel”.

Danna kiran shi yayi yana tamabayar sunan flowers ɗin dake gurin dama wayar a hands free take hakan ne yasa tana jin komai, lissafo su ya fara yi kamar haka.

” sun flower, orchids, lilies, daisies, roses and poppy flower, and many more can’t remember, but will check if i reach home”.

Ɗot ya kashe wayan shi yace; “To kin dai ji, me flower za su mana?”

Ɗan kallon shi tayi tace; “Amma ya kamata ku binciko ko wani flower ku tabbatar da abunda yake yi ko, ina laptop ɗin ka ɗakko mu duba, ko kuma muje library sai mu duba a can”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button