HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“Amin Umma na gode sosai da addu’ar ki”.

“Ina Abba yake?

” Gani nan Mama na”.

“Laaaa Abbu yi haƙuri ban ganka ba wallahi, Abbu kaima fa ka makara”.

“Aaaa, to yanzu ba gani nazo ba umm, Allah yayi miki albarka, Allah ya albarkaci wannan karatu naki yasa iya bakin wahalar kenan mama na”.

“Amin Abbu na gode sosai”.

Nan fa gurin ya ƙara kacamewa ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa suke.

Nan akayi hotuna akaci aka sha, akayi raha aka ji daɗi sosai.

“Ammi ba fa muyi hoton dake ba fa”.

“A’a ki gama ta Abbun naki dai kafin kizo kai na”.

Shiru gurin yayi ba wanda ya ƙara magana, sai da Umman sheka ta gallawa Ammi harara kafin ta shiga me hoto ya ɗauke su”.

“Haba ɗan Habibi na kazo mana muyi hotan”.

“Aaa ni ya Suhaila nayi fushi gaskiya tuntuni ba a neme ni ba sai yanzu”.

“Haba ɗan ƙaniƙani kazo mana”.

Nan akayi musu hoto me kyau ita da Mubarak.

“Aunty khadija kema ba muyi hotan da ke ba”.

*****

Surayya ce ta daka wani uban tsalle haɗe da ihu kafin ta rungume wani handsome guy da yake tsaye a gaban motar da na ke tunanin a cikin ta yazo.

Ni kam kallon ta nayi nace lallai ke ko kunyar Isyakun naki ma baki ji ba.

Cikin farin ciki ta ce”Uncle Habib!! Yaushe a gari!? What a big surprise thank you very much, i really miss you”.

“Kai amma dai gaskiya kinji kunya wallahi, har yanzu baki dena abubuwan ƴan fari ba sam, wauta da shashanci. Kai yanzu haka kake fama da ita Ishaq?

Ya faɗa yana kallon mijin Surayya da yake ta yaƙe.

” Au haka ma zaka ce Uncle, indai haka ne kawai ka koma wallahi”.

“Hajiya kin ganshi yana ce mun ƴar fari ko?

” Aa Habib wallahi baza ka zo ka takura mun auta na ba. Wai bana ce ma kar ka zo bane?

“Haba Hajiya ya za ayi naƙi zuwa convocation ɗin wannan village girl ɗin?

“To kar ka samun ita a gaba gaskiya”.

“Suhaila! Suhaila! Zo ki ga Uncle Habibyazo”.

“A haba da gaske, ki ce abokin faɗan ki yazo, ni na taɓa ganin inda uba da ƴa suke wasan kaka”.

“Wallahi yanzu ma sai da ya gama tsokana ta”.

“Uhmm to muje na gaishe shi, ni wallahi kaina ma har ya fara ciwo gida zan wuce kawai sai dai ku ga babu ni wallahi”.

“Gaskiya baki isa ba, idana ba so kike ki ƙara jangwalo mana Ammi ba”.

“Hmm lallai kuwa don naga har yanzu fushi take da ni”.

“Assslama alaikum, ina wuni ya Habib anzo lafiya ya mutanen gida?

Tayi gaisuwar lokaci ɗaya saboda a gajiye take.

Shi kuwa tunda ta fara magana yake kallon bakin ta, sai da ta gama tass kafin hankalin shi ya dawo dai dai.

” Kai gaskiya ban gane ba Uncle Habib. Meet Suhaila my hanjin lagwani”.

_”Masha Allah wonderful, Allah yayi halitta a nan dama ita ce Suhailan”_?

A fili kuma ya ce, “Lafiya lau Alhamdullilah. To ke kuma mara *M* what do you mean?”.

“Uhmm nothing oooo nace wani abun ne”.

“Sury bari naje. Ya Habib sai anjima”.

“Okay Suhaila, sai anjima na gode sosai, congrats Allah ya ƙara hazaƙa, ya kuma bada sa’a result fa yayi kyau”.

” Amin mun gode sosai. Sury idan kinji shiru nifa na wuce wallahi”.

“Kika isa ma”.

“Harma nayi yawa”.

*****

*The next day*………

_*Hihihihi ya kuka ji wannan page ɗin*_?

_*Tofa ga Unlce Habib mun haɗu da shi, ko yaza ta kasance, kuma gashi kamar ya yaba mu, umm su Suhaila ko dai mun samu miji ne*_?

_*Bari nayi shiru na barku haka… We meet tomorrow in sha Allah*_

_*Assalama alaikum*_

*faɗma Ahmad*✍️

*???????? AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page* 4️⃣
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍????✍????GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍????✍????~*

*~We are bearer’s of so golden pen????~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen????,savour our words, for it will cause you no pain.~*

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: “ما عاب النبي صلى الله عليه وسلم طعاماً قطُّ، إن اشتهاه أكله وإن كرهه تركه” (رواه البخاري ومسلم)
An karɓo daga Abu hurairah Allah ya ƙara yarda dashi yace:«Manzon Allah baitaɓa ai bata wani abinci ba (Ya faɗi wani abu akanshi na rashin daɗi) idan yayi masa zai ci idan kuma baiyi masa ba to zai ƙyaleshi»,
Bukhari da Muslim ne suka rawaitoshi.

 

_*HABIB*_

 

*The next day*

Lafiya lau aka gama convocation kowa ya koma gida cikin farin ciki.

Tunda Habib ya koma gida yake tunanin haɗuwar shi da Suhaila saboda ko da yaushe idan Surayya ta ɗora su a status nata cikin niqab take, sai jiya ne ya ganta da kyau duk da shima kusan haɗuwar sauri suka yi.

Sai da ya kai kusan 11:00 yana jinjina haɗuwar tasu kafin bacci yayi awan gaba da shi.

Da sassafe ya shirya cikin wani yadi da yayi mai kyau sosai ya kuma karɓi farar fatar ta shi, sai da yayi breakfast kafin ya sanar da yayar ta shi zai ce gidan Surayyan.

“Kai Habib da safiyar Allahn nan zaka je gidan mutane? ƙila ma ko tashi basu yi ba saboda gajiyar jiya”.

“Haba dai Hajiya 9:00 fa, ace har yanzu basu tashi daga bacci ba.

“Hmm sosai ma kuwa, yanzu ai yayi saifiya da yawa, ka bari sai ɗan anjima kafin nan mijin ta ya fita, don na san yanzu idan ka je sai kunyi abunda zai sa yaji haushin ku, don kai da Surayya sai addu’a kawai”.

“Kai, amma dai Hajiya ku kanawa sai a hankali wallahi, mu yanzu kaduna tun yaushe da kowa ya kama sabgar gaban shi, yaushe zaki je gidan magidanci ki same shi a gida yanzu, indai ba ranar hutu bane ko kuma wani uzurin. Ai mu 7:00 mun fita ka makara da yawa ka kai8:00”.

“Ku kenan, amma yanzu kam na tabbata da Ishaq be bar gida ba”.

“To ai shikenan bari na bari 11:00 tayi na san dai duk jarabar shi ya fita don magana me mahimmanci za muyi wallahi”.

“Allah yasa dai ba shirgin ku za ka je kuyi ba”.

*****

Suhaila a gajiye ta koma gida, saboda rabon ta da tayi abu irin haka tun candyn su, don ita ko ranar da suka yi matriculation bata je ba tana gida, ranar da suka yi final paper kuwa tana fitowa daga exam hall ta kama hanyar gida, ba yadda Surayya bata yi da ita ba amma tace ita ina baza ta iya wa’inan abubuwan ba, wani rubutu a jikin riga forget me not, da kuma shirt da ake yi, duk baza ta iya saka su ba, shi yasa taga gwara kawai ta dawo gida.

Da wuri tayi bacci babu wani damuwa a cikin ranta.

Da asuba kuwa da wuri ta tashi tayi duk abunda zata yi ta saka ƙannen ta a gaba suka yi karatu sannan suka koma bacci kafin lokacin makaranta yayi saboda kowa ya gaji jiya.

“Suhaila har yanzu dai kuna karatun asuba ɗin nan baki barshi ya tafi ba”.

“Ya fatima kenan, kina nufin effort ɗin Abbu da na ki ya tafi a banza kenan? mu ajiye shi mu dena yi. Ai ba zai yiwu ba”.

“Allah yasa idan kinyi aure Farida ta iya da Mubarak don naga yayi masifar raina ta wallahi”.

“Hmm ai gani yake ma kamar shine yayan nata. Abbu yana nan zai ci masa uba ai idan yace zai yi wani miss behaving”.

“Haka ne kuma”.

Wani long sigh fatima tayi kafin ta kalli Suhaila with adoration ta ce”Wai ni har yanzu shiru babu wani na alamina Suhaila?

“Hmm ya Fatima babu wani na alamina wallahi, sai dai kawai addu’a. Kuma inajin tsoron Ammi wallahi, kinga dai tana takura mun akan na fitar da miji amma wallahi yanzu da zan samu cewa za tayi bai yi mata ba, shiyasa ma ni ba kowa nake kulawa ba ya fatima. Sai dai kawai ki cigaba da mun addu’a”.

“Babu komai in sha Allah, kar ki damu kinji ko komai zai zo ƙarshe in sha Allah”.

Suna cikin magana suka jiyo muryar Nihla.

“Aunty Hala kizo ki bani ɗumame yunwa nake ji”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button