ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Hanyar library suka nufa inda suna shiga ya wuce ɗaki don ɗakko system ɗin shi, be wani jima ba ya fito ɗauke da drinks a hannun shi ya miƙa mata, inda ita kuma ta karɓa ta ajiye tana amsar system ta fara duba flowers ɗin, amma har suka zo kan roses babu wani abu, dariya yayi yace; “Har rose zaki duba, ai kema wannan kin san ba poisonous bace”.
“Yeah amma gwara mu duba ko zamu samu ƙarin ilimi”. amma ina har ta gama dubawa babu.
Tashi yayi yana faɗin “You see, bari na shiga na fito ba abunda za mu samu a flowers ɗin nan.
Ɗaki ya shige inda ita kuma bata yi giving up ba ta danna poppy flower wadda itace ta ƙarshe.
Bincike ta fara yi a kanta inda sai da tayi kusan ten minute tana dubawa, wani murmushi naga ta sake inda ta danna copy tana relaxing a kan kujerar da take zaune, a dai-dai lokacin kuma ya dawo yana kallon ta haɗe da sakin murmushi irin kinyi giving up ɗin nan kenan kema.
Zama yayi inda ta juya mai laptop ɗin zuwa gaban shi.
Kallon ta yayi yana faɗin “Me kuma ya faru?”
“Take a look”.
Ɗaukan system ɗin yayi yana ƙarewa rubutun kallo, saurin ɗagowa yayi yana kallon ta da mamaki kwance akan fuskar shi, inda ita kuma ta ɗaga mai gira tana sakin murmushi.
Be san sanda ya ajiye laptop ɗin ba yana kama hannun ta yana mata godiya, ji yake kamar ya rungume ta amma baya son hakan, tunda ita ɗin a matsayin matar ƙanin shi take.
Poppy flower is poisonous, and kuma idan aka yi amfani da ita gurin poisoning mutum nan da take aikin ta batare da wani ɓata lokaci ba, sai dai kuma sai tayi sati ɗaya a jikin ka sannan take nuna alamun da ita akayi amfanin wajen poisoning mutum.
Murmushi tayi tace; “Uhmmm yau psychologist tayi guiding criminologist, ya kamata ace kuna aiki da mu don mun fiku ƙwaƙwalwa”.
Dariya yayi yana tashi haɗe da laptop ɗin shi yace; “Zanyi lokacin ki, amma yanzu zan ɗau hanyar Washington, bye sai na dawo zuwa gobe, zan kira Ummi ko ki faɗa mata don bazan samu damar shiga ciki ba, kije
gurin Kausar na san yanzu anyi delivering wayar ki ki karɓa a gurin ta”.
Ɗaki ya shige inda ita kuma take jin farin ciki mara misaltuwa yau tayi temako kuma me amfani.
Cikin gida ta koma, har zuwa yamma sannan Kausar ta dawo daga gurin aiki, labari ta shiga bata inda itama taji daɗi sosai, ta ke daɗa bata shawarar ta cigaba da karatun ta, tunda tana da ƙwaƙwalwa har haka.
Wayar ta ta ciro ƙirar iphon 11 pro sabuwa dau a kwali me camera ukun nan ta miƙa mata, kallon wayar tayi da mamaki kwance akan fuskar ta, wanan ce sabuwar wayar tata, taɓɓ ina takai matsayin riƙe wannan wayar.
Kamar ta san abun da take tunani kenan yasa tace mata”Ƴar gatan ya Ahmad, da ya Jibril,su suka gata ki haka”.
Murmushi tayi haɗe da karɓa tayi godiya, tuni ta jona wayar a charge inda zuwa magrib aka saita mata komai.
Jibril ta fara kira inda su kayi kusan awa suna Abbu ɗaya bayan haka ta kira Abbun ta suka jima suna waya inda ta gaisa da kowa na gidan su harda Ammin ta.
Surayya ta kira suka sha hira take sanar da ita baby Najwa ta fara tafiya har tace zata tura mata pictures nata through whatapp.
Bayan sun gama waya ta ɗan tsaya a jikin window tana kallon harabar gidan nasu, from no where taji Ahmad ya faɗo mata, gashi bata da numbern shi amma ta san yanzu suna can suna fafatawa.
Zainab kuwa ta gama haɗa plan ɗin ta inda ta turawa Jibril pictures ɗin da ta ɗauka.
Dariya tayi tace; “Saura Hajiya Kulthum kuma, dole ne ka nisanta da ita don ni ma fara hango abunda baka san da shi ba Ahmad a cikin idanun ka, kiran Umman ta tayi ta sanar da ita plan ɗin da ta ce tayi ya tafi dai-dai babu wani kuskure.
Daga cen ɓangaren tace;” Hmmm, yanzu zaki ga yadda Jibril zai musu katangar ƙarfe inda ita kuma kulthum za ta sa ayi gaggawar ɗaura musu aure kinga Ahmad ya zama naki ko yana so ko baya so”.
Murmushi tayi tana faɗin “Wannan haka yake Umma shiyasa nake bala’in sonki”.
Da haka sukayi sallama inda ita kuma Zainab take cikin farin ciki mara misaltuwa.
Jibril kuwa yana komawa gida yayi wanka ya saka kayan baccin shi yabi lafiyar gado ya janyo wayar shi ya kunna data yana hawa whatapp, da saƙon Zainab ya fara cin karo, be san numbern ba don bashi da numbern ta.
Kallon hutan yayi, nan da nan ya tashi daga kwancen da yake yana ƙarewa hotan kallo wata zufa ce ta haɗar mai, inda cikin lokaci ɗaya jikin shi ya fara rawa, zuciyar shi kuwa kamar ta fito haka yake ji tsabar bugawar da take yi, a lokaci ɗaya kuma hawaye suka wanke mishi fuska, Suhailan shi a jikin Ahmad kalli yadda ta ƙanƙame shi wanda a ko wani lokaci idan ya taɓa ta bata da wani buri da ya wuce ta dakatar da shi amma yau itace kwance a jikin Ahmad tayi mai irin wannan rungumar.
Tuni yayi mata forwarding hoton yana kiran numbern ta, ɗauka tayi tana mai sallama “Ki hau whatapp”. kawai shine abunda ya iya furtawa.
Hawa tayi inda tayi ido biyu da abunda yayi mugun ɗaga mata hankali tana tunanin inda ya samu wannan hotan nasu, kenan haka yana nufin bibiyar ta yake yi ko me.
Bata gama tambayar kanta ba kiran shi ya shigo wayar ta.
Ɗauka tayi jikin a sanyaye.
“Nasan kinyi viewing saƙona ko? So i need more explanations, me ya haɗa ki da wancen tsinannen manemun matan?”
Lumshe idon ta tayi, taji zafin kalmar da ya jefi Ahmad ɗin da ita alhalin ba lefun shi bane, itace ta fara kai jikin ta ga nashi.
“Tambayar ki nake fa kin mun shiru malama! Inajin ki”.
“Ba lefin shi bane, lefi nane, kuma nima hakan ya faru ne bisa halin da nake ciki, don haka please kar kayi misunderstanding ɗin abun nan na roƙe ka don Allah”.
Wata iska ya furzar me zafin gaske kafin yace; “Wallahi, wallahi, sai na raba shi da duk wani jin daɗin shi tunda har rawar ƙarfar shi tasa ya raɓe ki, da bezo kusa dake ba ai da baki kasa controlling kan ki ba ko?”.
“Please na roƙe ka leave him alone lefi nane kuma zan gyara komai don Allah”.
Ya kashe wayar shi ba tare da yaji ƙarashen abunda take faɗi ba.
A dai-dai lokacin Kausar ta shigo inda ta hangota sai kuka take yi, da sauri ta ƙaraso tana tamabayar ta me ya faru, nuna mata hutan tayi gabanta na ƙara faɗuwa”Shikenan nazo zan ƙara tarwatsa muku gida na shiga uku na ni Sakinatu me nake shirin aikatawa”.
Rungume ta Kausar tayi tana tunanin waye zai jiƙa wannan ɗanyen aikin.
Jibril kuwa yayi ta kiran Ahmad amma ba a ɗaukan wayar hakanne yasa ranshi ya daɗa ɓacci.
Ummi yayi ma forwarding pic ɗin, inda ya kira ta yace ya tura mata saƙo ta duba through whatapp.
Bata kawo komai ba ta hau ta duba, gabanta ne ya buga damm, har wani jiri ne taji yana ƙoƙarin ɗibar ta saboda tsabar tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki, kardai zargin ɗanta da akayi a lokatan baya ya zama gaskiya, innallilahi wainna ilaihi raji’un.
Kiran Jibril ya shigo wayar ta inda ya fara zazzaga bala’i baji ba gani”Kin gani ko Hajiya, duk abunda ake faɗa a baya baki taɓa yarda ba ko, to yau gashi nan with evidence ko zaki musa ne? Wallahi, wallahi sai Ahmad yasan ya shiga gonata, babu ni babu shi, kuma sai na karɓi haƙƙin taɓa mun matata da zan aura da yayi, sai ya faɗa mun me yake nufi da hakan, sai naga bayan shi, Allah ya isa tsakani na dashi, kuma in Allah ya yarda……..
Bata ƙarasa jin abunda zai faɗa ba ta kashe wayar tana zubewa a ƙasa haɗe ta fasa kuka me cin zuciya”Shikenan Ahmad, duk yardar da nayi maka ashe yaudara ta kawai kake yi, ashe duk abunda ake zargin ka da shi haka yake ba ƙarya ake maka ba, ashe duk rantsuwar da kayi mun duk ta ƙarya ce, wayyo ni Ummukulthum ina zan saka kaina ya Allah ka kawo mun ɗauki”.