HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

A dai-dai lokacin kuma Kausar da Suhaila suka shigo cikin ɗakin don zuwa loakacin tasan itama an tura mata da saƙon, ƙarasawa tayi itama ta zube a ƙasan tana rungume Ummin nata, cikin kuka tace ; “Wallahi Ummi ƙarya ake mai so ake a haɗa ku faɗa kar ki yarda da maganar kowa don Allah, ga Suhaila ki tambaye ta zata faɗa miki yadda abun ya faru don Allah ki dena wannan kukan”.

“Kausar taya zan yarda da dake bayan ga sheda na gani da ido na, Ya gama dani ya cuce ni”.

Suhaila ce ta matso tana faɗin”Wallahi ba haka bane Ummi, ba abunda kike tunani bane kiyi haƙuri wallahi ba haka bane ki tsaya na faɗa miki abunda ya faru, ni na fara kwanciya a jikin shi, shi kuma ya rungume ni yana lallashi na amma wallahi ba abunda ake tunanin bane don Allah Ummi, kar ki bari sanadi na Familyn ki ya ƙara tarwatsewa”.

Miƙa mata hannu Ummi tayi ta rungume ta itama tana faɗin”Aa karki kare shi, don Allah kar ki ƙara magana bana son jin komai”.

A taƙaice dai ranar kwana suka yi suna lallashin Ummi amma taƙi yin shiri, har sai da asuba tayi suka yi sallah sannan ta ɗan samu bacci, bayan gari ya gama wayewa suka haɗu a dining inda gaba ɗayan su babu wanda hankalin shi yake kwance sai Zainab da take cin abincin hankali kwance.

Bayan ta gama, kallon Ummi tayi tana faɗin”Yanzu kin yarda da ni ko? kin yarda da abunda ɗanki ya aikata a baya ko? uhmmm dama ance kowa da ranar shi, yau kuma sai naji me zaki ce”.

A dai-dai lokacin motar Ahmad ta shigo cikin gidan inda yabar komai a mota ya nufo cikin gidan direct don yunwa yake ji so yake kawai yazo yaci abincin Suhaila shiyasa ma yau da asuba ko da sukayi hadling case ɗin Sara a hannun police be tsaya jiran wani abinci ba ya taho gida.

Sai da yana shigowa da fara’ar shi ya hango Ummin shi hawaye na ta zuba a idon ta, da sauri ya ƙaraso yana tsugunuwa haɗe da ɗora hannuwan shi akan cinyar ta yana tambayar dalilin da yasa take kuka.

Hankaɗe shi tayi ta ɗaga hannu ta bashi maruka guda biyi kyawawa masu shiga jiki………

 

******

_*Su Zainab gulma tayi garɗi*_

_*Ma’asalam, follow me on Wattpad@cynosure3*_

*_Faɗma Ahmad_*
[7/30, 2:22 PM] Aunty Sumie: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*page 5️⃣7️⃣to5️⃣8️⃣*

 

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Addu’a Ga Wanda ya ba da Bashi idan aka zo biyan sa bashin:*

بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي أَهْلِكَ وَمَاِلكَ. إِنَّمَا جَزَاءُ السَّلَفِ الْحَمْدُ وَاْلأَدَاءُ.

Barakal lahu laka fi ahlika wa malika, Innama jaza’us salafil hamdu wal’ada.

Allah ya yi maka albarka a cikin iyalinka da dukiyarka. Hakika sakamakon bashi shi ne godiya da biya.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

 

_*Sorrows*_

Dafe ƙuncin shi yayi ya tsaya yana kallon Ummin nashi, wacce bata taɓa ɗaga hannu ta mare shi ba, kai idan ya tuna when last tayi mai faɗa ma ya manta wallahi amma yau Ummin shi ce ta ɗaga hannu ta mare shi, for what? Which means kukan da take yi saboda shi ne.

Daga Kausar har Suhaila ji suka yi ƙafafun su na rawa as if baza su iya ɗaukan gangar jikin su ba, hannu Ummi ta ƙara ɗagawa zata ƙara kwashe shi da mari don ji take kamar zuciyarta zata faɗo ƙasa her only son, wanda take cherishing kamar ranta, ace shi ya aikata wannan abun, saukar marin kawai suka ji tasssss inda Ahmad yayi saurin riƙe shoulder ɗin Suhaila da take shirin zubewa a ƙasa tsabar yadda marin ya shige ta, ganin Suhaila ta mara yasa tayi saurin ƙarasawa tana riƙe ta, cikin kuka da tsantsar tashin hankali Suhaila tace; “Ummi na faɗa miki ba lefin shi bane, why are you hurting him han? Ni na fara shiga jikin shi and then yayi hugging ɗina amma ba abunda kike tunani bane, kuma ban san wanda yayi taking picture ɗin ba”.

Cikin kukanta wanda yake tahowa harda majina ta juya tana kallon shi, wayar ta ta buɗe ta danno hotan tana nuna mai kafin tace; “Just take a look, Ummi tana tunanin wani abu muke yi kuma ba haka bane please ka mata bayani, ban san wa ya ɗauka ba, but mun san abunda ake zargi ba haka bane, Jibril send the picture ban sani ba, ban san ya akayi yaje wajen shi ba, ban san wa ya ɗau hotan ba, am burning saboda ni, saboda ni”.

Ta ƙarashe maganar tana nuna kanta haɗe da zubewa a ƙasa tana sakin wani kuka wanda rabonta da shi tun lokacin da akayi raping ɗin ta.

Ahmad kuwa da yaji wani abu ya taso mai don sai yanzu ya fuskanci inda zancen ya dosa wani kallo ya watsawa Zainab don yasan babu wanda zai yi wannan aika-aikar idan ba ita ba, sunkuyar da kai tayi tana wani tura baki alamar don accuse me, am not the one.

Ji yayi zuciyar shi na mishi wani mugun zafi ga kukan da take yi har cikin ranshi, ji yake kamar ya bita ya tsuguna kamar yadda tayi ya jawo ta jikin ya rarrasshe ta ya share mata hawayen ta, kai idan ma da dama he will use his tongue to wipe all her tears, ji yayi shima idon shi ya ciko don abun shi ya fara tashi, be san sanda ya zube a ƙasan ba, ya wani jawota jikin shi ya rungume ta kamar zai shige cikin jikin ta har sai da ƙasusuwanta su kayi ƙara wani kuka ya saki me cin zuciya yana faɗin”Ummi na it just happen just like this, kamar haka, she was crying and i embrace her, i don’t mean it, ba abunda kuke tunani bane, and Ummi kin fi kowa sani na akan kowa so please ki dena wannan tunan…….

Be ƙarasa faɗan abunda zai faɗa ba jikin ya fara saki yayin da ya sassauta mata riƙon da yayi mata wanda ta kasa motsin arziƙi, baya yayi luuuuuuu ya tafi zai zube a ƙasa tayi saurin janyo shi ta dawo dashi jikin ta tana faɗin”Ummi he is dying, aren’t he? Please Kausar help us with his medicine, duba jikin shi”. tayi maganar tana ɗan sakin shi da sauri duk suka yo kanshi inda Ummi ta zube a ƙasa tana girgiza shi, numfashi yake fitarwa sama-sama yayinda idon shi da yake shirin rufewa suna kan Ummin shi, riƙe hannun shi tayi tana girgiza mai kai, a hankali ya furta “Ruwa, Ummi ruwa”.

Da gudu Zainab ta tafi kitchen ta ɗakko ruwa ta dawo a lokacin kuma Zainab ta gama duba jikin shi amma babu maganin.

Ganin haka yasa Suhaila ta tashi ta gudu ta fita daga cikin gidan tana shiga part ɗin su kallon ƙofofin ta tsaya yi don bata san wanne ne ɗakin shi ba, na Jibril ta shiga inda tana buɗe ƙofar taga ƙaton hotan shi wanda hakan ya tabbatar mata da ba ɗakin shi bane, wanda yake kallon shi ta tura ta shiga da sauri tana kalle-kalle, da sauri taje wajen side drawer tana dubawa, janyowa tayi nan taga robar maganin ai kuwa da sauri ta ɗauka tana dawowa cikin gidan a 360, amma kafin tazo Ummi ta bashi ruwa har ya ɗan fara dawowa dai-dai maganin ta ɗakko tana miƙawa Ummi inda ita dai bata san na meye ba kawai dai ta bashi ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button