HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Sai da yayi kusan 10 minute kafin ya fara sauke ajiyar zuciya inda ya buɗe idon shi yana zubawa Suhailan.

Kallon shi itama tayi tace; “Are okay? Ko akwai wani abun?”

Tayi maganar a mugun kiɗime.

Gyaɗa mata kai yayi kafin ya fara yunƙurin tashi inda Ummi ta temaka mai, Kausar na riƙe ɗayan hannun shi sukayi sama da shi ɗakin Ummi yayin da Zainab take biye da su tana dana sanin ɗaukan pic ɗin.

Ni kuwa nace ke kika sani wawiya kawai.

Akan gadon Ummi suka kwantar da shi inda taja mai blanket , ita kuma Suhaila ta haɗo abinci ta biyosu da shi, yana hangota ya tashi ya zauna, Ummi ce ta karɓi abincin tana mata sannu inda ta fara bashi abaki babu wasa ya fara karɓa yana ci don dama muguwar yunwa yake ji, kuma ba ciwo ba ko meye baya hana shi cin abinci.

Ɗaki Suhaila ta koma inda bata ji daɗin abunda ya faru ba sam.

Sai da ya gama ci Ummi ta bashi ruwa, sannan ya ɗan jingina da gadon yana lumshe ido bacci yayi awan gaba da shi a zaunen.

Zainab ma ɗaki ta koma duk abun duniya ya ishe ta, shin wai me yasa ma ta aikata abunda ta aikata, gashinan tana daɗa ganin tsantsar tsanar ta a idon shi.

Ummi ce ta kalli Kausar tace ; “Maganin da aka kawo Ahmad na menene?”

Ɗan shiru Kausar tayi ta kasa magana”Ba magana nake miki ba!”

Ummi ta wani daka mata tsawa wanda sai da hanjin cikin ta suka motsa, bata san sanda ta buɗe baki ta fara bata bayani ba” Ammm Ummi i think depression ne yake damun shi kuma yayi worst sosai ban san me ya faru ba and ban san sanda ya fara shan magani ba but amma daga gani therapy suka bashi maganin i don’t know Ummi nasan dai yana shan maganin bayan dawowan shi that all”.

Kallon shi tayi tanajin wani mugu-mugun son baby boy ɗin nata yana taso mata, me yasa ma ta mare shi, why will she, me yazo kanta, wani long sigh ta saki tana kallon shi.

Ɗan shafa goshin shi tayi tana jin son shi yana ƙara shiga ɓargon ta, idon ta ne ya ciko da ƙwalla tayi saurin maida su.

Tuni Kausar ta bar ɗakin don baza ta iya ganin Ummin nata tana breaking haka ba, tana shiga ta hango Suhaila tsaye jikin Window da gudu ta ƙarasa suna rungume junan su kafin suka saka wani kuka a tare ba wanda yake iya rarrashin wani, sun ɗau kusan 10 minutes a haka kafin Suhaila tayi breaking hug ɗin nasu tana sharewa Kausar fuska inda su kayi mazauni a bakin gadon.

 

Zama sukayi ta kalli Kausar tana faɗin”Ta ya Ummi zata yarda da mu Kausar?”

” Shhhh Ummi ta riga ta haƙura kar ki damu, kuma tasan ya Ahmad bazai taɓa yin haka ba”.

 

A ɓangaren Ummi kuwa, tana kan Ahmad bata motsa ba har ya tashi daga baccin da idan banda Suhaila ba abunda yake gani.

 

Yana buɗe ido yace; “Suhaila” yanda yayi maganan a hankali yasa Ummi ta ɗan matsa tana kallon bakin shi don bata ji me yace ba.

“Suhaila” Ya faɗa yana ɗan ƙara ɗaga muryar shi wanda Ummi ta samu damar jin abunda ya faɗa, a take kuma gaban ta yayi mugun faɗuwa, me hakan yake nufi ya tashi da sunan ta a bakin shi.

Idanun shine suka buɗe tarr inda ya zuba su akan fuskar Ummin nashi, tashi yayi kamar wanda aka zaburar yana kallon ta haɗe da kamo hannun ta yana faɗin”Ummi ki yarda da abunda Suhaila take faɗa miki, wallahi, wallahi ba da wani abu hakan ya faru ba, so please ki dena tunanin ina having affair da Suhaila ne please Ummi, is just a coincidence don Allah ki fahimce ni bazan taɓa aikata wani abu makamacin haka ba, Ummi kuma kin san inda wani abu nayi Mata zata faɗa ba sai anyi fixing hoto an nuna miki ba, please Ummi na, tana da issues da yawa don’t make it hard for her please Ummi a yanzu haka ma tana da issues a kanta please Ummi na ki fahimce ni”.

 

Wani irin rungume shi tayi tana sakin kuka haɗe da girgiza mai kai tana shafa bayan shi alamar rarrashi.

Cikin kuka tace; “Ya isa haka Ahmad, ya isa haka na yarda, na yarda da abunda kuka faɗa am sorry, am really sorry Ahmad”.

Ɗago ta yayi ya manna mata kiss a forehead ɗin ta yace; “Ummi na san baza ki taɓa fushi da ni ba haka ba, nasan kin san bazan taɓa aikata abu irin haka ba, ba abunda yake tsakani na da Suhaila Ummi na ki fahimce, we where just sharing our problems and wani lokacin tana taya ni aiki that all, ko jiya ma ita ta temaka mun naje nayi handling wani case a Washington”.

Kallon idon Ahmad ɗin tayi tana hango son Suhailan a idon nashi don yadda yake bayanin nan, kasan akwai wani strong connection between the two of them ba tare da sun sani ba.

A hankali ta riƙo hannun shi tana murzawa ta fara magana in a low and soft voice ɗin ta”Ahmad”ta kira sunan shi, kallon ta ya yayi yana zuba mata idanun shi.

“I want you to stay away from Suhaila, ba ruwanka da ita duk wani abu da kasan yana shiga tsakanin ku ka katse shi kana ji na, i don’t want problems, yanzu haka ma ya aka ƙare ballantana wani matsalan ya ƙara kunno kai, ka fahimci abunda nake son faɗa maka, i don’t want you to fall in her love,saboda ita Jibril yake so kuma ita zai aura, Ahmad saboda kai na kawo Suhaila gidan nan amma tunda na fuskanci sun haɗu a Nigeria har sun fara soyyaya na haƙura, so kaima ina son ka bar komai ka kuma dena shiga sabganta saboda itama ta fara sabawa da kai, and kasan yadda kake da shiga ran mutane kar tazo wata rana itama ta fara son ka, wanda zai ƙara kawo mana alot of confusion a gidan nan kuma kaima ka sani, ba sai na faɗa maka ba”.

Wani irin kallo yake ma Ummin nashi, “Fall in love with Suhaila ta ya ma zan fara wannan tunanin, haba me Ummin nashi take faɗa ne”. Yayi maganan a cikin zuciyan shi a fili kuma yace; “Haba dai Ummi na baki fahimci abun bane amma ko sau ɗaya ban taɓa kawo wa a raina ba, look bari ma kiji i promise you i will stay away from her koda kuwa ace son nata nake yi”.

Murmushi tayi tana shafa kan shi, inda a cikin zuciyar ta take jin wani iri dama ace shine zai aure ta don tasan zata kular mata da Ahmad ɗin.

Tashi yayi ya fita daga ɗakin Ummin ba tare da ya ƙara magana ba ya fita zuwa ƙasa.

Tana jikin windown inda ta ƙurawa dream catchern da Jibril ya bata ido amma a zahirin gaskiya bashi take kallo ba, kamar daga sama taga wulgawar shi nan ta ware idon ta tana dawowa cikin hayyacin ta, inda kamar an tsikare ta ta juya tayi ƙasa da gudu tana bin bayan shi, tana fitowa yana ɗora hannun shi akan handle ɗin part ɗin su.

Kira ta ƙwalla mai tana ƙarasawa gurin da gudu, tsayawa yayi cak yana kallon ta from head to toe, safa ne kawai a ƙafan ta don ko slippers bata saka ba, gashi rigan sanyin jikin ta ba wani na kirki bane sai kanta da yake role da mayafi wanda ko da yaushe a haka yake.

Ƙarasowa tayi tana nishi, inda bakinta yake fitar da wani tiriri tsabar sanyin garin.

“Ummi ta haƙura, ta gane ta fahimce mu ko?”

Gyaɗa mata kai yayi batare da yace komai ba, yanajin wani irin abu yana tsarga mishi tunda daga kanshi har zuwa babban ɗan yatsan shi na ƙafa.

Da sauri ya ɗauke kan shi a kanta yana murɗa ƙofar zai shige ta ƙara jefo mai wata tambaya” How was your work, was it successful?”

Gyaɗa mata kai yayi yace ; ” Yeah, it was”.

Be jira abunda zata faɗa ba ya shige yana rufo ƙofar haɗe da jingina a jikin ta,a dai-dai lokacin kuma wayar shi ta ɗau ƙara, ya ciro ta a aljihu yana duba me kiran shi ganin sunan Jibril yasa ya ɗauka yana karawa a kunnen shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button