ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ba sallama ba komai ya fara zazzaga bala’i yana faɗa mai baƙaƙen maganganu “Just stay away from her, wallahi tafi ƙarfin irin ku gang guys masu bin mata a New York, she is mine and only, wallahi sai kayi danasanin taɓa mun Suhaila ta da kayi, korrare kawai, i love her to the core and zan iya yin komai akanta ao watch out idan ba haka ba wata rana i will…….
Be ƙarasa jin abunda zai faɗa ya cire wayan a kunnen shi haɗe buga wayan a jikin bango ji kake tarastass wayan ya faɗi a ƙasa, Suhaila da take tsaye a gurin bata motsa ba ganin yadda yayi behaving tayi saurin tura ƙofar tana kiran sunan shi inda shi kuma yake a tsaye ƙiƙam kamar wanda aka dasa.
“Ya Ahmad me ya faru what happened?” ta shigo ciki tana ƙoƙarin kama hannun rigar shi tsabar kiɗimewar da tayi wani irin cilli yayi da ita ta faɗa gefe kafin ya nuna ta hannu yana faɗin”Just stay away from Suhaila, karki ƙara zuwa kusa da ni am suffering much and much saboda ke, ki bari kawai kar na miki wani abun da zan zo ina dana sani”.
Nan hawaye suka cika mata ido inda ta tashi tayi cikin gida da gudu, shi kuwa juyawa yayi ya dunƙule hannu ya daki bango yace; “Damn! Damn!!! Damn it, damn it, damn it Jibril”.
Buɗe ƙofar ɗakin shi yayi ya shige toilet ya kunna shower zuwa warm water ya tsaya a gurin yana tokare hannun shi da bango ba tare da ya cire kayan jikin shi ba ruwa ya fara sauka akan bald head ɗin shi zuwa kwantaccen sajen shi da koda yaushe yake jin gyara, a hankli ya kai hannun shi ya fara cire kayan jikin shi yayi watsi da su a gurin yana sauke wani irin ajiyar zujiya inda ruwan ya samu nasarar fara bin murɗaɗɗen jikin shi da ban taɓa sanin haka yake ba sai yau……
*******
_*So, here we are, till after sallah in sha Allah, i love you all, just bear with me don jin yadda zata kaya tsakanin, Ahmad da Suhaila and Jibri, shin Ahmad zai iya avoiding Suhaila? Shin Suhaila will fall in love with Ahmad? Jibril zai iya haƙura da ita kuwa? Kai i have alot of tambayoyi don ina son sanin tarihin gidan su Ahmad wollah..*_
_*Asalama alaikum, eid mubarak in advance aci nama dai a hankali*_
*_Faɗma Ahmad_*
[8/6, 7:58 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*page5️⃣9️⃣to6️⃣0️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*Addu’a Ga Wanda ya ba da Bashi idan aka zo biyan sa bashin:*
بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي أَهْلِكَ وَمَاِلكَ. إِنَّمَا جَزَاءُ السَّلَفِ الْحَمْدُ وَاْلأَدَاءُ.
Barakal lahu laka fi ahlika wa malika, Innama jaza’us salafil hamdu wal’ada.
Allah ya yi maka albarka a cikin iyalinka da dukiyarka. Hakika sakamakon bashi shi ne godiya da biya.
*_EIDKUM MUBARAK, KUL AAAM WA NAHNA BIKHAIRIN IN SHA ALLAH_*????????????????
Da fatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya mai-maita mana, Amin ya rabbi.
_*Can i do this?*_
Sai da ya kwashe kusan mintuna goma sha biyar kafin ya fara murɗa kan shower yana rage ta a hankali, yayin da yake jin ƙafar shi kamar ba a jikin take ba saboda daɗewar da yayi a tsaye ba tare da ya motsa ba, ga ruwan da yake dukan kanshi da babu ganshin arziƙi, shi kanshi ya san dole yau yayi mura ko zazzaɓi ya kama shi a cikin biyu dai za ayi ɗaya.
Sai da ya ƙara kamar five minute sannan ya kashe shower gaba ɗaya yana fitowa daga cikin jakuzin.
Towel ya ɗaura zuwa ƙugunshi ya fito daga cikin banɗakin yana tsayawa gaban mudubi, kallon kan shi yayi ta cikin mudubin, nan da nan abunda yayiwa Suhaila ƴan mintunan da suka wuce suka shiga dawo mai, runtse idon shi yayi nan take hotan cillar da ita da tayi ɗazun ya bayyana a cikin idanun nashi, saurin buɗe idon yayi yana ƙara kallon kanshi, ji yake kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu kawai ya huta.
Mai ya shafa sama-sama ya feshe jikin shi da turare me ƙanshin gaske sannan ya buɗe closet ɗin shi ya ɗakko wata black long sleeve da black jeans yasa a jikin shi, gado ya haye yana jan bargo a dai-dai lokacin kuma yaji wani zazzaɓi me mugun zafi ya rufe shi, tuni ya fara maƙerƙeta yana daɗa dunƙulewa guri ɗaya.
Ita kuwa Suhaila tana fita daga ɓangaren su ta shige ciki taja birki a kitchen tana fasa kuka me cin zuciya.
Cikin zuciyar ta take ayyana _”Me yasa Ahmad zai mun haka? meye lefi na don naje ganin halin da yake ciki, ya Allah, ka kawo mun ɗauki wallahi na gaji da garin nan gida kawai nake so, gwara jarabar Ammi da ciwon kan da nake sa kaina a cikin gidan nan kowa da matsalar shi wannan wacce irin rayuwa ce, Jibril yana mata Abu kamar wani Abbun ta, shi kuma Ahmad ya tsiro da sabon iskanci, shin ni baiwar su ce ko kuma ƙannen uba na ne, shi kanshi Jibril ɗin tsaf zan iya fasa auren shi don bazan iya da matsalar gidan nan ba_”.
Haka dai ta gama zancen zucin, sannan ta wanke fuskar ta a sink ɗin kitchen Sannan ta juya zata shiga cikin gida a dai-dai lokacin kuma Ammi ta shigo cikin kitchen ɗin don ɗora abinci kallon Suhaila tayi tana karantan yanayin ta.
Riƙo hannun ta tayi ta zaunar da ita a ƙaramar kujerar dake kitchen ɗin ta riƙo hannun ta.
“Suhaila kiyi haƙuri a kan abunda ya faru ɗazu ki kuma yafe mun, naji tsoron kar abinda naƙi yarda da shi shekarun baya ya tabbata gaskiya ne shiyasa hankali na yayi mugun tashi har na fara kokwanton Ahmad ɗin, saboda wani lokacin kai haifi ɗa ne amma baka haifi halin shi ba, kana nan kana tarbiyya wani yana warware maka musamman ma shi da ya ɗibi shekaru baya gidan, duk da da hankalin shi ya bar gidan nan, amma ban san da wasu irin mutane ya haɗu ba bayan haka, mussaman da ya tafi America hankali na duk yaƙi kwanciya, don haka kiyi haƙuri kuma ya mun bayani duk na fahimta Allah ya miki albarka, sannan kuma don Allah kiyi ƙoƙari wajen nesanta kanki da Ahmad don na fara hango abunda ku baku hango shi ba, bana son fitina a tsakanin Jibril da Ahmad saboda amana ce uwar su ta barmun, so please Suhaila ki taya ni ƙoƙarin yin hakan nasan idan kika zauna kika yi tunanin zaki gane abunda nake nufi. Kije ki kwanta ki huta zanyi girki da kaina yau”.
Har ta buɗe baki za tayi magana Ummi ta ɗora hannun ta akan bakin ta tace; “Bana son musu jeki kawai”.
Jikin ta a sanyaye ta nufi cikin gida tana juya magangamun Ummi, ko da ita ba psychologist bace indai har ka tsaya kayi dogon tunani zaka gane abunda Ummin take nufi.
Ɗan murmushi tayi tana jin kanta na wani mugun sara mata yayin da take tafiya tana tunanin kalmomin”Ummi tana nufin wai za mu iya faɗawa soyyayar junan mu ni da Ahmad ko me take nufi”.