HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Ɗan tsayawa tayi a stairs na ƙarshe wanda zai sada ta da ɗakin Kausar, jin kanta ya ɗau zafi da kalmar da ta furtawa kanta ta ƙarshe yasa ta kwance rolling ɗin kanta tana cusa hannun ta cikin gashin kanta haɗe da faɗin “Noooo, mustahil(never) ya Allah sa’idini, ana biddi ruh min hun, (ya Allah ka temake ni, ina son barin gurin nan)”.

Da sauri ta ƙarasa tana shigewa ɗakin haɗe da rufe ƙofar ta jingina a jiki, kallon ta Kasaur tayi from head to toe ga mayafin ta a hannu ta baza kalabar dake kanta, sannan kuma duk tayi zuru-zuru kamar ba ita ba.

Ƙarasowa tayi tana tamabayar ta me ya faru, a dai-dai lokacin kuma kiran Jibril ya shigo wayar ta, ɗauka tayi tana mai sallama inda ya fara mata gargaɗi kan ta nesanta kanta ga Ahmad, yayin da ta ƙara jin abun wani banbarakwai kenan shima abunda yake tunani kenan.

Kashe wayar tayi ta cilla ta a kan gado tana faɗawa gadon haɗe da runtse idon ta, ita kam tunanin ta ya tsaya ta rasa me suke nufi da ita gaskiya ta gaji gida zata koma, wata biyu da rabi ya mata yawa ma wallahi.

Kausar ce ta sake jefo mata tambaya”Wai Suhaila me ke damun ki ne? ”

Tashi tayi kamar mahaukaciya tace; “Your brothers, are confusing, ina so zan tafi gida please, ki faɗawa Ammi bazan iya jira har sai lokacin bikin nan ba wallahi na gaji i just want to go home”.

Kallon ta tayi da mamaki amma bata ce mata komai ba ta cigaba da sabgarta.

Bayan sati biyu, duk yadda Ahmad ya kai ga ya watsar da AL’AMARIN SUHAILA ya kasa ya rasa ina zai saka kanshi, shin wai ma me yake damun shi ne? me yasa ta kasa fita a kanshi ya san dai bazai taɓa yuwa ace sonta yake ba, amma a iya sannin shi yanayin da yake ciki kamar alamar soyyaya ce amma yasan never, zai saka kanshi a matsala ne kawai. Ta dena zuwa library duk inda yasan tana zuwa idan yaje baya ganin ta sai dai idan ya shigo cikin gida ko in ana hira ko kuma idan za a ci abinci, akwai wani aikin shi da yake so ta temaka mai amma ina babu fuska shin wai ina zai saka kanshi? me zai yi ne? gashi itama yaga tunda abun nan ya faru bata kula shi kamar da, sai dai gaisuwa kawai kuma shima a cikin sauri take gaishe da shi ta wuce abun ta,amma tabbas indai har sonta ya shige shi da sauri haka akwai babbar matsala kuwa don be san ya zai yi ba, dole ya koya mata tsanar shi, don kar ma tayi tunanin zuwa kusa da shi ko da kuwa da wasa ne.

A ɓangaren Suhailan ma hakan take amma ita sai dai ba wai son nashi take ji ba kawai dai ta damu da shi ne saboda issues ɗin da yake da shi a gidan su, gashi ko da yauahe tana son yi mai magana amma maganganun Ummi suna taso mata matuƙa,amma yau kam tanajin za tayi mai magana don ta ɗan samu sauƙi.

Bayan sun gama break fast kowa yaci ya ƙoshi ya tashi ya fita, zai koma part ɗin shi don har yanzu ba wani daɗin jikin shi yake ji ba, mussaman ma da Daddy ya kira shi ya ƙara mai gargaɗi akan Suhailan saboda Jibril ya sanar da shi ya kuma sanar mai da next month za su dawo sun rage kwanakin ma don haka ya fara shirin bar mishi gida kafin ya iso.

Ita kuwa Suhaila tana ganin ya fita ta miƙe ta shige Kitchen tana fita ta ƙofar kitchen ɗin Zainab kuwa a ankare take don ta gane abunda zai faru haka ma Ummi don duk wani move nasu ta san da shi har damuwar da suka shiga su duka biyun.

Tana fita yana zagayowa shi kuma, “Ya Ahmad”. Ta furta a hankali cikin sanyin murya.

Ɗan tsayawa yayi yana runtse ido yana jin wani abu na mugun ratsa shi a kuma lokacin yaji wani irin feeling ɗin ta wanda yana gab da zama ruwan soyyayar ta yaji ya
taso mai.

Har zai juyo yaji an ƙara kiran sunan shi “Ya Ahmad”. Sai dai a wannan karon ba muryar ta bace.

Ɗan juyowa yayi yana kallon su su duka biyun, Suhaila kuwa har ta buɗe baki za tayi magana taga fitowar Zainab ɗin.

Da sauri ta Ƙaraso tana faɗin”Please zan bika part ɗin ka, ka koya mun wani abu”.

Kallon Suhaila yayi yana tuna plan ɗin shi, murmushi yayi mata ya miƙa mata hannu, babu musu kuwa ta saƙala hannun ta cikin nashi, ya rungumota zuwa gefan jikin shi sannan ya kalli Suhailan ya sakar mata murmushi kafin suka yi gaba, Zainab kuwa juyowa tayi ta mata gwalo.

Sai dai suna zuwa dai-dai part ɗinshi ya saki hannun ta yana haɗe fuska, a gefe guda kuma yana tuno yanayin da yaga Suhailan ta shiga,runtse idon shi yayi yana jin haushin abunda yayi amma ya zai yi, don a yau ya ƙara tabbatar da abun da Ummi ta faɗa indai suka cigaba da having good time itama zata fara son shi, don haka bazai so yayi breaking heart ɗin ta ba.

Suhaila kuwa wani abu taji ya tsaya mata a maƙogaro nan da nan hawaye suka cika mata ido. Sai da ta ɗan yi tunani sannan ta shanye su tana dai-dai ta nutsuwar ta”Kar dai ace wai kishi nake yi?”

Ta tambayi kanta, shanye abunda taji ya tsaya mata tayi tana ƙara gyara muryar ta sannan ta shige cikin gida tana hayewa sama.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda ko da yaushe idan Ahmad yaga Suhaila za ta mai magana privately yanzu zai ga mandiya zaƙaƙura Zainab, shi kuma sai ya samu opportunity ɓatawa Suhaila rai, ko Zainab bata ganshi ba indai ya ganta to sai ya ƙirƙi wani abun inda ita kuma take jin daɗin ya dawo da sonta, shi kuwa idan yana haka ji yake kamar yana watsawa kanshi ruwan zafi. Akwai ranar da yacewa Zainab ɗin ma he will fuck her a gaban Suhailan ita kuma tun daga lokacin ta cire shi a ranta ta kuma tsane shi amma duk da haka acan ƙasan ranta akwai abunda bata san ko meye ne take ji gama da shi ba, kuma wai ita a tunanin be san taji abunda ya faɗa ba shi kuma sai da ya bari ya hangota ta kusa ƙarasowa kitchen sannan ya faɗawa Zainab.

Kausar da Ummi kuwa sun gano jirgin Ahmad, inda ba wanda yake jin daɗin abunda yake yi duk da sun san don ya nesanta kanshi da Suhailan ne.

Yauma kamar kullum Zainab da Ahmad suna zaune a gurin swimming pool Kausar da Suhaila suka shigo gurin saboda yanzu nan ne sabon gurin zaman su inda Ahmad ya gano, kuma yasan za su zo shiyasa ya gayyaci Zainab suka taho gurin, ko kallon inda suke Suhaila bata yi ba, ta samu guri ta zauna tana ciro littafin ta ta koma can nesa tana fara rubutun ta, ita kuma Kausar ta ɗaga musu hannu ta buɗe system ɗin ta ta fara aikin ta kanta tsaye, jefi-jefi Suhaila ta kan ɗago ta kalli Zainab da Ahmad inda duk ɗagowa sai sun haɗa ido su duka ukun suna kallon junan su.

Suhaila ce ta tashi don duk sun ishe ta, yiwa Kausar sallama tayi tazo zata wuce, a dai-dai lokacin kuma Zainab tace; “Ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu, wata bata da zuciya ta yar kare ya ɗauka, kai ya Ahmad Allah ya rabamu da iyaye masu son zuciya, yanzu ka duba ka gani wata an ɗakko ta ankawo ta gurin da ba a biɗar ta wannan wacce irin rayuwa ce”.

Cak Suhaila ta tsaya tana jin kalmomin Zainab ɗin na ratsa jinin jikin ta, a fusace ta juyo tace; “Tabbas baki yi ƙaryaba, amma inaso ki sani ina gab da bar muku gidan ku kuma bazan taɓa dawowa cikin wannan family ɗin naku me cike da SARƘAƘIYA ba kuma ina so ki sani bani da sha’awar zuwa garin nan ko kaɗan, kuma duk yadda nake ƴar karere wallahi na fiki daraja a idanun mutanen gidan nan, yadda Ummi take mun da yadda Suhaila suke mun basu miki haka, so don haka kowa ya tsaya a matsayin shi, sannan kuma inaso ki sani duk abunda kike taƙama da shi wallahi zan iya karɓe shi daga gare ki don ni ba mahaukaciya bace da ilimi na sannan duk abunda kuke daga ke har Ahmad na sani aikin banza aikin hofi kawai”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button