HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Juyawa tayi zata bar gurin ranta a ɓace da sauri Zainab ta sakko daga kujerar da take tana finciko Suhailan haɗe hankaɗa ta zata faɗa cikin swimming pool ɗin jikake danjamm ta faɗa cikin ruwan duk abubuwan da suke hannun ta suka zube a ƙasan gurin.

Tuni ta fara dambe da numfashin ta saboda ba iya ruwa tayi ba gashi yana da ɗan zurfi ruwan, wani irin ihu Kausar tayi tana ajiye laptop ɗin hannun ta ta cire takalminta ta faɗa ruwan amma sai dai kafin ta kai ga shiga Ahmad ya riga ta, wani irin swimming yayi ya nutse ƙasan ruwan yana janyo ta zuwa bakin gurin kafin ya jawota suka fita yana tsayar da ita haɗe da buga bayan ta, ita kuwa sai tari take yi, kausar ma fitowa tayi, sai dai kafin ta ƙaraso Suhailan ta hankaɗa shi ya koma cikin ruwan tana faɗin”me yasa zaka taɓa ni? ban yafe maka ba, ai da ka barni na mutu na huta kawai, Kausar ce tayi saurin riƙeta tana jan hannun ta suka bar gurin fitowa ya ƙara yi daga gurin yana jin zuciyar shi na mishi zafi kamar an ɗiga mai ruwan dalma.

Da sauri yayi gurin Zainab ya ɗoke ta da mari, ya nuna mata sabbaba ɗin shi haɗe da girgiza shi da kyau yace ; “Bari kiji abunda zan faɗa miki yau, i love her, and i love her si much, duk abunda nake yi i was just trying to avoid her, and that doesn’t mean you have the right ki mata irin wannan cin mutuncin, so’ i am just doing this for the sake of my brother and our family, saboda bazan iya zama rival ɗin shi ba, and idan na zama kema kin san wa Suhaila zata zaɓa so behave your self ki nutsu if not kina gab da rasa ni har abada, and idan na ƙara juya miki baya na wallahi wallahi na tafi har abada kenan wawiya kawai”.

Ita kuwa dafe kuncinta tayi tana jinjina irin maganganun da faɗa mata.

Ɗaki suka koma Suhaila ta canza kaya tana ta zubar da ruwan ƙwalla tsabar wulaƙanta mutum, ta jefa ta ciki, kenan tayi niyar kashe ta ne, wani hawayen ne ya ƙara cika mata ido a dai-dai lokacin Ummi ta shigo, Ahmad ya biyo bayan ta, da sauri ya ƙarasa yana bata haƙuri i ko kallon inda yake bata yi ba ballantana ta bashi amsa, kallon Ummi tayi tace; “Don Allah Ummi ki mayar dani gida bazan iya zaman gidan ki ba, kiyi haƙuri Jibril ɗin ma na haƙura da shi zan koma normal life ɗina nida Ammi na da sauaran ƴan uwa na, na jarabtu a rayuwa ta, ina tunanin lokaci yayi da san samu nutsuwa, don Allah Ummi”.

Babu wanda idon shi be ciko ba, Ummi ce tayiwa Kausar nuni da ido ta tashi taja hannun shi suka fita daga ɗakin suka shiga ɗakin Ummin nasu.

Zama yayi a bed bench ɗin ɗakin yana haɗa kai da gwiwa, tuni hawaye suka cika mai ido ya ɗago ya zuba idon shi cikin na Kausar ɗin, da sauri ta matsa kusa da shi tana rungume shi tsam a jikin ta wani kuka ya fasa yana sakin murya kamar wani ƙaramin yaro, ƙanƙame ta ya ƙara yi, yace; “Kausar I love her so much, i really love her, and banyi duk abunda nayi don na ɓata mata rai ba, kawai inason ta tsane ni ne, ina son nuna mata gaskiyar hali na da Jibril yake sanar da ita ko da yaushe, ina so ta yarda ni ɗan iska ne, manemin mata, mashayin giya, gang of American guys, koken user, duk ina so ta yadda, bad guy wanda baban shi baya so, ko zata tsane ni ta hutawa kanta da faɗawa soyyaya ta kamar yadda na faɗa soyyayar ta, wallahi Kausar am ready zan jira Daddy ya dawo na haƙura zan auri Zainab, saboda kar Suhaila ta rabu da Jibril, bana son tayi breaking heart ɗin shi, i want our family to be normal kamar yadda muke da, zamu haɗu da Aunty Aisha ta faɗa mun sun koma Nigeria mijinta ya gama karatun nashi, and so Daddy ma ya bar ƙasar da ba nashi ba, ya samu abunda ya samu, please Kausar mu gina happy family a Nigeria nagaji da rayuwar ƙasar wajen nan, am spoil”.

Ya ƙarasa maganar yana daɗa sakin murya yana rusa kukan shi abunshi.

Ɗago shi tayi ta share mai hawayen fuskar shi ta ɗan bar jikin shi ta saka hannun ta cikin nashi ta kalli fuskar shi tace; “I know ya Ahmad” na sanka, na san ka fara son Suhaila tun ba yau ba, amma kana ganin wannan shine decision ɗinka? ka haƙura da ita? idan kana son ta zaka iya samun ta”.

Wani kallo ya watsa mata na baki da hankali, “Kausar kin san me kike faɗa Kuwa? in ƙara tarwatsa familyn kenan ko, mu samu dawamammiyar ƙiyayya ko, to bazan iya ba, this is my final decision idan kina baya na to, zaki iya temaka mun….

Nigeria

Bari muji a wani halin su Ammi suke mun daɗe ba mu leƙo su ba…..

*****

*_Ma’asalam_*????

_*Faɗma Ahmad*_✍????
[8/7, 9:21 PM] Aunty Sumie: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*

*Bintu Ahmad*

*Wattpad@cynosure3*

*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*

 

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

 

*Addu’ar Kin shu’umci*

اَللَّهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلاَّ طَيْرُكَ، وَلاَ خَيْرَ إِلاَّ خَيْرُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ.

Allahumma la tayra illa tayruk, wala khayra illa khayruk, wala ilaha ghayruk.

Ya Allah! Babu shu’umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.

*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????

https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp

_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._

 

*_Back to the journey_*

*Nigeria*

Yau ma kamar kullum zaune suke a palo bayan sun gama breakfast, Farida ce ta kalli Abbu tace; “Abbu mun gode jiya Ammi ta bamu kuɗin mu na sati Allah ya ƙara buɗi”.

“Amin Faridede, amm ta faɗa mun zancen littafin da akace ku siya, dubu goma ko?”

Ɗan ɗagowa tayi ta kalli Abbun nata sannan ta kalli Ammin, haɗe rai tayi tana galla mata harara haɗe da yi mata gargaɗi da ido.

Sunkuyar da kai tayi ba tare da tace masa komai ba, ta shiga tunanin wai sai yaushe ne Ammin su zata girma, bata jin kunyar yin ƙarya bata da aiki sai na cin kuɗin Abbun nasu babu gaira ba dalili wannan wacce irin uwa ce.

Muryar Abbun ta ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula “Farida kinaji na ko, na bata dubu biyar zata baki, sai muga zuwa gobe jibi me Allah zai yi kuma ,in sha Allah zaki siya”.

To ta amsa da shi sannan tayi musu sallama ta wuce makaranta abunta.

Da yamma can ta Dawo gida a gajiye, ta tarar da Ammin nasu tayi musu girki ,sannu da gida tayi mata sannan ta shiga Kitchen ta zuba abinci taci ta ƙoshi, bayan ta gama cin abincin ta matso kusa da Ammin tana ɗan sunkuyar da kai, babu wani tsoro a tattare da ita tace; “Ammi me yasa kika karɓi har dubu goma a gurin Abba kika ce nace zan siyi littafi?”

Ɗan dakatawa da abunda take yi tayi tana watsa mata wani kallo kafin tace; “To sannu uwar marasa kunya titsiye ni kika zo yi kenan, wato naciwa ubanki kuɗi ko, to ina da abun yi ne shiyasa na karɓa ƴar me tsaurin idanuwa, mare kunya kawai kina kallo na da ido ƙif-ƙif, sai naji duka tukunna”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button