ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Tashi Farida tayi tana ɗan ƙunƙuni haɗe da shigewa ɗaki ta bar Ammin tana ta sababi abunta.
Ni kuwa nace Allah yaja da ran manyan mata, masu godiyar Allah, to wallahi dai iyaye sai mun gyara don mu mata wani zubin muna da matsala da ka samu namiji shiru-shiru mai haƙuri sai mu fara fin ƙarfin shi muma mai kallon wani wawa haɗe da kawo mai raini, to abunda ba mu sani ba shine muna da ƴaƴa fa a tsakani me zai faru idan har yaran suka raina mu, to a gaskiya sai mun kula, Allah yasa mu dace ya kuma bamu mazaje na gari wa’inda za su kula da mu ba *mujin bahaushiya ba* wanda su suka fi yawa a wannan zamanin.
London….
Ahmad kuwa a nan ya tafi ya bar Kausar zuciyar shi na mishi wani zafi, a ɓangaren Ammi da Suhaila ma hakan take don tayi ta mata kuka kan tana so ta koma ga iyayen ta, amma ta lallame ta ta bari har sai su Jibril sun dawo daga tafiya.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Ahmad ba abunda ya ragu na soyyayar Suhaila a cikin zuciyar shi, sai ma ƙaruwa da yayi gashi an kira shi an sanar da shi aikin su na nan Washington yana gab da zuwa ƙarshe don haka su fara shirin komawa can New York asalin gurin aikin su, hankalin shi ya tashi sosai ga su Daddy suna shirin dawowa suma, haka dai yayi ta daurewa yana cizewa amma ina abun ya gagara.
Ita kuwa Suhaila yanzu ba abunda yake gabanta illa ta ganta a gida kawai don ba abinda yafi asalin ka daɗi ba London ba ko wani gari ne indai babu naka a kusa da kai ina abun sai dai addu’a, Jibril kuwa kullum ƙirga kwanaki yake yi don ya ƙagu su dawo gida ayi ta da wajewa kawai.
Bayan sati uku..
Yau ta kama su Jibril za su dawo gida, ko ina ya kaceme ba abunda akeyi sai girkin tarbar su, speciall meal suke haɗa musu, fried rice suka yi akayi paper chicken, sai salad sannan aka soya doya da ƙwai da mayar hanta, sai milk shake sannan suka yi different juices. Jere komai aka yi a dining aka gyare gidan aka saka wani room freshner me daɗin gaske.
Sannan kowa yaje yayi wanka ya shiryar tarbar su, kowa da abunda yake ranshi, Ahmad ba abunda yake tunani sai ta yaya zai fara sanar da maifin nashi hukuncin da ya yanke, ga wani faɗuwa da gaban shi yake yi, ita kuwa Suhaila daɗi kashe ta saboda tasan ta kusa komawa gida, Kausar kuwa bata san dawowar tasu saboda abunda yayan nata yake shirin aikatawa kan shi, ita kuwa Ummi ba abunda zata ce don bata cikin farin ciki kuma bata cikin ɓakin ciki ita dai gata nan sai addu’a kawai.
Da misalin ƙarfe 8:30 na dare suka sauka a ƙasar England, wasu manya-manyan motaci be guda biyu suka je ɗakko su, babu wani ɓata lokaci suka iso gida, daga Daddy har Jibril babu wanda beyi ƙiba ya ƙara fari ba.
Cikin shigar su ta alfarma suka shiga cikin gidan yayin da ma’aikata suke biye dasu da akwatunan su. Suna shiga cikin gidan Kausar ta taho da gudu ta rungume su tana “Oyoyo Daddy na, nayi missing ɗin ka sosai, sakin shi tayi, tayi kyau kissing goshin Jibri tace; ” kaima nayi missing ɗin ka irin totally ɗin nan”.
Dariya yayi yana girgiza kai haɗe da faɗin”Allah ya shirya ki auta, nima nayi missing ɗin ki”.
Zainab ce ta ƙaraso itama tana hugging ɗin shi “Dady you are welcome”.
“Welcome daughter”.
Ummi ce ta ƙaraso gurin tana musu sannu da zuwa, ɗan harar ta Daddy yayi yace; “Ba wani bana so, ko ɗan hugging ɗin nan babu”.
Dariya tayi sosai sannan taji daɗin yadda ya faɗi hakan ɗan faɗawa jikin shi tayi, duk sukayi shewa suna dariya, Ahmad da yake kitchen yana kallon su shima yayi dariya haɗe da goge hawayen da ya zubo mai yanajij son Daddyn nashi har cikin ɓargon shi, finally dai in sha Allahu kamar yadda yayi sanadiyyar ɓata komai zai gyara komai yau.
Cikin gida Daddy ya shiga yayi wanka, ya rama sallolin da ake bin shi sannan ya saklo ƙasa don cin abinci kafin lokacin shima Jibril har yayi shirin shi ya shigo cikin gida, cikin nishaɗi da kewar juna suke cin abincin yayin da hankalin Ummi yana ga Ahmad da yake cikin kitchen ɗin tayi-tayi da shi suci abinci tare yace mata A’a sai sun gama zai sanar da shi, ita kuwa Suhaila tana ɗaki kamar me takaba sai Daddy ne da kanshi ya tambaye ta aka sanar da shi ai tana ɗaki, bayan sun gama cin abinci yasa aka kira ta, nan ta sakko da gaida shi ya kuma amsa mata ba yabo ba fallasa, tambayar ta yayi ra’ayin ta akan auren Jibril ɗin nan da nan taji gaban ta yayi mugun faɗuwa, shi kuwa gogan sai washe baki yake yana kallon ta yana wani haɗiye miyau don ba ƙaramun kyau ta mai ba, ta rame amma kuma tayi fari sannan fatarta ta wani goge kamar ba ita ba.
Haɗa ido suka yi da Ummi ta lumshe ido alamar tace eh, ɗan sunkuyar da kanta tayi tana murmushi, kallon Ummi yayi yace; “To ya, Aunty amarya, shirun ta yana nufin eh ko?”
Gyaɗa mai Ummi tayi, dariya yayi yace; “Allah ya muku albarka, nan da sati uku za muje Nigeria ai inyaso ayi maganar auren naku”.
Gyaɗa mai kai tayi tana bin hanyar kitchen sabida tsabar yadda jikin ta yake rawa.
Tana shiga ta tsaya daga jikin fridge tana runtse ido wasu hawaye masu zafi na zubo mata ta rasa me yasa taji abun wani iri, ta rasa me yasa taji she is not happy at all, yadda take son suyi aure da Jibril a kwanakin baya amma yanzu taji komai ya canza mata, ko don abunda yake faruwa a gidan ne.
Shikuwa Ahmad yana zaune yana kallon ta shima hawayen na cika mishi ido, amma yayi saurinm ya shanye su yana sai-saita kan shi.
Kamar daga sama taji yace; limaza?”
Saurin buɗe idon ta tayi ta zuba mai su da suka jiƙe da ƙwalla, shafa kan shi yayi yace;” Ohhh sorry baki gane reall arabic ko, kin fi gane gargaliyya”.
Shiru tayi bata ce mai komai ba sai mamakin shi da take yi dama ya iya arabic
Wani lokacin take arabic a gaban shi ashe yanajin me take cewa shiyasa wani abun idan ya faɗa take mamakin inda ya sani.
Katse mata tunani yayi yana faɗin” lesh am tufki? Ma biddek jawazo? “(me yasa kike kuka? Ba kya son auren shi)”.
Sakin baki tayi tana kallon shi, sai kuma ta maze ta juya mai baya tana wani haɗe rai.
“La, uridu an azhabu ilal bait”. (A’a ina son in tafi gida).
“Ohhh, Masha Allah, ahsanti, ashe kina jin real arabic basai gargaliyya ba, wow bravo alaiki”.
Daɗa haɗe rai tayi tana bin hanyar fita daga kitchen ɗin.
“Azizateyyyy”….
Ya faɗa in a slow voice ba tare da ya bari taji abunda ya faɗa ba.
Fita tayi da sauri sannan ta saki wani murmushi wanda bata san na meye ba, haɗa ido suka yi da Jibril nan ta ƙara sakar mai wani murmushin har sai da one side dimple ɗin ta ya lotsa. Fita tayi ta mean palo ta nufi garden tanajin wani daɗi mara misaltuwa, dariya ta ƙarayi tana girgiza kai, akwai ranar da tana library bata jin daɗi suka yi waya da Fatima take gaya mata ai period ɗin ta ne yazo kuma yana zaune, kenan duk yaji abunda tace shiyasa wani zubin sai ya dinga ɗagowa yana kallon ta, haka tayi ta tuna abubuwan da tayi a gaban shi, wani tayi dariya wani kuma taji kunya, tana zaune Jibril ya iso gurin.
Ƙara kallon shi tayi tana daɗa sakin murmushi haɗe da rufe fuskar ta.
Guri ya samu ya zauna yana kallon ta sannan ya fara magana a hankali shima yana murmushin”Wannan kunyar fa, tun yanzu? Ba wani sannu da zuwa nayi missing ɗin ka sai wani kunya da kike ji kamar wanda akace an ɗaura mana aure yau.
Sauke hannun tayi tana kallon shi, bazai gane ba ne kawai ba wai shi take jin kunya ba, aa abunda tayi ne yake bata dariya wai ita bata yarda ba tana nunke shi a bai-bai ashe shine ya maida ta sakarya.