ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

“You are welcome Hanoon, ya hanya kun iso lafiya? Nayi missing ɗin ka sosai, shikenan na biya bashi”.
Dariya yayi yace; “Kin biya bashi kam, to yanzu me aka tanadar mun”.
“Babu” ta faɗa tana ɗaga kafaɗa yayin da gaba ɗaya hankalin ta yana kan Ahmad.
Ahmad kuwa shahada yayi kawai ya fito daga kitchen yana musu sallama, azabure Daddy ya ɗago yana kallon shi, nan da nan duk fara’a da farin cikin kasancewa da iyalin shi ya kau, wani kallo ya watsawa Ummi alamun tuhuma, kafin takai ga magana ya jefe shi da glass cup dake hannun shi yana shan lemo, ji kake ƙwalll, ya sauka a goshin Ahmad, dafe gurin yayi yana rufe idon shi don har sai da kofin ya tsage sannan yayi ƙasa ya ƙarasa fashewa, nan da nan kuma jini ya fara zuba daga saman girar shi, wani irin kukan kura yayi yaja kujerar da yake zaune a kai tayi baya ya miƙe tsaye yanaa nuna shi da yatsa.
A lokaci ɗaya kuma Kausar da Zainab da Ummi suka yi kanshi suna riƙe shi, tuni Daddy ya ƙaraso yana finciko shi.
Ummi ce tayi ƙarfin halin yin magana tana faɗin”Haba Alhaji ai ka bari kaji da me yazo maka, amma kawai ba kaji abunda zai faɗa ba ka yanke wannan hukuncin”. Ta ƙarashe maganar hawaye na zubo mata.
“Me zai faɗa mun Kulthum, wannan ɗan iskan yaron shiyasa nace bana son idan na dawo na ganshi saboda zan iya aikata mai komai wallahi, don me yasa yake da taurin kai? “.
Cire hannun shi yayi a kan goshin shi, nan da nan jini ya cigaba da ɗika zuwa saman idon shi har ya gangaro fuskar shi.
Ummi ce ta ƙaraso tana riƙe hannun shi tace; “Ka bari kawai mu tafi asibiti kana zubar da jini”.
Riƙe hannun ta yayi ya girgiza mata kai sannan yace; “Daddy zan auri Zainab na yarda da sharaɗin ka, ba abunda nake so illa na kasance tare daku sannan na goge ƙiyayyata a zuciyar ka”.
Sakin shi yayi ya cillar da shi yace; “Ka makara Ahmad, inaso ka sani bayan abunda ka yiwa Suhaila bazan taɓa bari ka auri Zainab ba, saboda haka zaka je ka kashe ta da baƙin cikin ka na neman mata, Allah ya haɗa kowa da rabon sa, now, get out from my house”.
Sai yanzu yaji wani mugun jiri ya fara ɗibar shi amma haka nan ya daure yana jin zuciyar shi kamar zata fashe be yi ƙoƙarin ce mai komai ba, saboda yasan ɓata lokacin shi zai yi kawai tunda har ya faɗi wannan ya san halin Daddyn shi da kafiya kamar mutanen farko.
“Daddy zan tafi, amma inaso ka sani ni ba manemin mata bane, kuma in sha Allahu bazan taɓa zama manemin mata ba, ko da ace na taɓa yi ba tare da na sani ba, ka sani kaine sanadi kuma Allah yana kallon ka, na gode, Ummi na kiyi haƙurin rashi na da zaki yi don idan na tafi baza ki ƙara jin labari na ba har abada”.
Hanyar fita yayi yana tafiya a hankali, Kausar na riƙe da shi tana kuka, Ummi kuwa ta kasa motsawa tsabar baƙin ciki, Zainab kuwa matsowa tayi za tayiwa Daddy magana ya ɗaga mata hannu.
Fita tayi riƙe da shi, haka suka tako a hankali zuwa compound ɗin gidan, kamar ance Suhaila ta ɗago suka yi four eyes da shi daga cikin lanbun da suke, ai Kawai ganin gilmawar ta Jibril yayi don be san sanda ta tashi ba ma, tana ƙarasawa ta tsaya tana mai wani irin kallo me wuyar fassarawa shima kallon ta ya tsaya yayi, yayin da Kausar da jibril suka tsaya suna kallon su, ita kam bata san a wani irin yana yi take ba, matsawa tayi tana tamabayar shi abunda ya same shi duk hankalin ta a tashe kamar ba itace wanda tayi wata bata kula shi ba.
Juyowa tayi ta kalli Jibril a ruɗe tana faɗin”please ka duba shi yana bleeding innallilahi, don Allah Jibril”.
Wani kallo ya watsa mata, yana aika mata da wata harara wanda bata san na meye ba, wani wawan tsaki yaja yana juyawa zai shiga cikin gida.
“Jibril!! Ta kira sunan shi amma ina yaƙi juyowa ya cigaba da tafiya abun shi.
” Jibril idan ka tafi, zan duba shi, i will treat him”.
Cak ya tsaya yana juyowa da kallon shi zuwa gare ta, a wani mugun fusace ya dawo gurin da suke yana shigewa gaba, cigaba da tafiya suka yi har suka isa part ɗin su kafin su ƙaraso har ya ɗakko first aid box, suna zuwa Kausar ta kwantar da shi ya fara duba shi, ciwon be yi zurfin da za a mai ɗin ki ba amma ya ɗan shiga babu lefi, wanke gurin yayi ya saka abunda zai saka mai yasa plaster ya rufe gurin sannan, ya ɗaura mai drip don jikin shi ya ɗau zafi sosai.
Kallon Suhaila yayi da har yanzu bata ɗauke idon ta a kan Ahmad ba, shima ita yake kallo, wani malolo ne yaji ya tsaya mai hakan ne yasa yace mata”Na duba shi ai za mu iya tafiya ko?”
Tashi tayi tana kallon shi zata wuce taji an riƙo mata hannu, saurin juyowa tayi ta kalle shi, a dai-dai lokacin kuma idon shi ya fara lumshewa wani mugun bacci yana ɗaukar shi, juyawa tayi ta mayar da hannun nashi zuwa ƙirjin shi tana gyara blanket ɗin dake jikin shi.
Wani irin fizgar hannun ta Jibril yayi hakan yasa ta bishi babu shiri tana ƙwace hannun ta cikin nashi.
Har suka shiga cikin gida yana haɗe rai, inda ita kuma kanta yake mugun sara mata kamar zai fita, ɗaki ta wuce tana sakin wani kuka me cin rai kamar zata mutu, ta gaji wallahi ta gaji, meke shirin faruwa da ita badai son Ahmad take ba, ta shiga ukun ta ina zata saka rayuwar ta yanzu ita ya za tayi ne, ina zata saka kanta taji daɗin rayuwa….
****
_*Ku biyo ni akwai drama a gaba*_
_*Ma’asalam, faɗma Ahmad*_
[8/9, 1:57 PM] Cynosure: *????????AL’AMARIN SUHAILAT????????*
*Bintu Ahmad*
*Wattpad@cynosure3*
*Page6️⃣3️⃣to6️⃣4️⃣*
*✍✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾✍✍*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶’s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*????
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ ???? *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Addu’a ga Wanda Ya ce Maka: Allah Ya yi Maka Albarka:*
وَفِيكَ بَارَكَ اللهُ.
wa fika barakallah.
Kai ma Allah ya yi maka albarka.
*~INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?~*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
_Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samun wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook_. ????
https://www.facebook.com/101594048306878?referrer=whatsapp
_Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu._
*Sorry last page banyi indicating ba, waccan shine 61 to 62,wannan kuma 63-64*
_*Besotted*_
Haka kowa ya kwana babu daɗi a gidan, kowa da abunda yake a ranshi, kowa kuma da hukuncin da yake so ya yanke kafin safiya.
Ahmad yaji daɗin jikin shi da Jibril ya saka mai ruwan, a gurin shi Kausar ta kwana tana yi tana kula da shi, Ummi kuwa kwana tayi tana kuka, inda shima Daddy ba a barshi a baya ba, indai har Ahmad ɗan shi ne to ta yaya za ayi ace be damu da shi har haka ba, ya damu amma shi a ganin shi wannan shine best solution, and shi zai kawo zaman lafiya ga kowa.
Zainab kuwa sai da ta kira Umman ta ta gaya mata duk abunda ya faru sannan hankalin ta ya kwanta, nan ta lallashe ta, ta kuma nuna mata za su yi maganin Daddy tunda shine matsalar su yanzu.