HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

Washegari da safe Ahmad ne ya fara tashin Kausar tayi sallah, cikin gida ta koma ɗakin su, shi kuma ya shiga yayi wanka sannan ya ɗoro alwala, kuma har yanzu baya wani jin daɗi jikin shi, bayan yayi sallar asuba, yayi azkar sannan ya fara kwararo addu’a yana fatan Allah ya kawo mishi sassauci cikin lamarin shi, ya kuma zaɓa mai mafi alkhairi a gare shi ya cire mai soyyayar Suhaila.

Tashi yayi ya canza kayan jikin shi ya fara haɗa inashi-inashi, ya shiga library ya ɗibi abubuwan shi masu amfani sosai, painting da yake so da dai sauran abubuwa.

Kausar kuwa akan dadduma ta tarar da Suhaila ga idon ta yayi ƙanana, alamar bacci, bata runtsa ba tayi ta sallah tana kai kukanta ga mahallincin ta.

A tare suka yi Alwala suka yi sallah, sannan Kausar ta koma part ɗin Ahmad, nan taga ya haɗa uwar kaya har ya fito da su ya kira motar kwasar kaya ta kaimai ainahin masaukin shi dake can Washington, babu wani ɓata lokaci suka fara loda kayan, inda ita kuma Zainab ta tsaya tana kallon ikon Allah, da gaske tafiya zai yi kenan? kuma na har abada da ya faɗa in ba haka ba irin wannan haɗa kaya.

Kallon shi ta tsaya yi yayin da motar kayan ta fice abunta, haɗa ido suka yi ya sakar mata murmushin shi me kashe jiki.

Da gudu ta faɗa jikin shi tana fasa kuka, shima rungume ta yayi yana kukan aka ransa wanda zai ba wani haƙuri.

“Ya Ahmad yanzu tafiya za kayi ka barni da Ummi? don Allah kar ka tafi we will be missing you please, ta ya kake tunanin Ummi za ta iya mantawa da kai han? Abunda kake shirin yi ba dai-dai bane”.

 

Shoulder ɗinta ya dafa yace; “To Kausar ya kike so nayi? Me kike so na cewa Daddy kema kin san bazai taɓa fahimta ta ba so it’s better na tafi kawai, ko hankalin kowa zai kwanta”.

Ummi ce ta shiga ɗakin Daddy don suyi magana amma yaƙi bata dama sam, yace idan tana so ma zata iya bin Ahmad ɗin.

Ba yadda ta iya haka nan ta haƙura saboda Kausar da kuma amanar da Abokiyar zaman ta ta bar mata.

Ɗan kallon shi tayi tace; ” Amma ina nemar alfarma ka barmu muci abinci na ƙarshe tare da shi muyi sallama cikin kwanciyar hankali, ba da tashin hankali ba”.

Gyaɗa mata kai yayi ya shige toilet abun shi.

Fita tayi ta shiga kitchen ta haɗa breakfast me daɗin gaske ta jere komai a dining, ta gyare gurin sannan ta koma sama tayi wanka ta saka simple abaya a jikin ta tai kyau sosai, sai dai kana kallon ta kasan tana cikin tsanin damuwa.

Suhaila ma wanka tayi ta saka simple riga da skirt ta ɗaura rigar sanyi a kai, sannan ta sakko ƙasa ta tarar da Ammi ta gama haɗa komai, gaida ta tayi tana kallon yanayin Ummin inda take jin mugun tausayin ta, inama ace Ammin tace take da irin wannan haƙuri da kawaicin.

“Ina Kausar take?”

“Umm, ta fita tun ɗazu may be tana gurin ya Ahmad”.

“Okay je kice musu su zo ayi breakfast su dukan su”.

To ta amsa mata da shi ta fita daga palon tana bin hanyar part ɗin su Ahmad ɗin.

Tsaye ta hango su sun rungume junan su sai kuka suke yi, nan taji itama idonta ya ciko da ƙwalla, ɗan matsawa ta ƙara yi tana kallon su, ganin ta ne yasa ya saki Kausar ɗin yana zuba mata idanun shi wanda suka jiƙe da hawaye.

Kallo ɗaya ta mai ta ɗauke idanun ta don baƙara mun kyau yayi mata ba yau ɗin, sanye yake cikin brown silk trouser, daga saman shi kuma farar rigace mai hannun links sai falmaran brown ,takalmin shi ma sau ciki brown, fuskar shi tayi fayau yayi wani haske kamar ba shi ba, ya gyara ƴar sumar kanshi da ta fara fitowa, sai taga yafi mata kyau da ya ɗan bar gashi a kanshi.

Gyaran murya tayi saboda yadda ya tsare ta da idanu sannan tace; “Ammi ce tace kuzo ku duka za ayi breakfast”.

Tana gama faɗan haka ta juya da sauri don kar ƙwallar da take riƙewa ta zubo mata, ba tare da ta shirya ba.

Kallon juna suka yi sannan Kausar ta kama hannun shi suka bi bayan Suhailan, suna shiga suka tarar har kowa ya samu guri ya zauna, inda Daddy ya haɗe rai, Jibril kuma ya ɗaga kai sama, shi kuwa Ahmad kusa da Ummin shi ya zauna, ita tayi serving kowa sannan ta zauna ta zuba abincin ta.

Ba abunda kake ji sai ƙarar cokula kowa da abunda yake ranshi, ba irin Ahmad da Zainab.

Bayan Daddy ya gama cin abinci ya kalli Jibril yace; “Son idan ka gama zamu yi iya tafiya”.

Gyaɗa mai kai yayi yana ɗaukan coat ɗin shi da ya ajiye a jikin kujerar da ya zauna.

Ahmad ne yace ; “Daddy”.

Cak Daddyn nasu ya tsaya ba tare da yace komai ba, takowa gaban shi Ahmad ɗin yayi yana tsugunawa kafin a hankali cikin zubar da ƙwalla ya fara magana”Abba na, kayi haƙuri ka yafe mun duk abunda nayi maka, wanda na sani da wanda ban sani ba, sannan kuma ina so ka sani soyyayar da nake maka babu abunda ya ragu a raina don kayi abandoning ɗina daddy, ina sonka, ina sonka kuma bazan taɓa dena sonka ba, zan tafi kamar yadda ka buƙata kuma in sha Allahu bazan ƙara zuwa kusa da zuri’ar ka ba, ina so ka sani zan shiga duniya zan aikata ayyukan alheri, zan mutu da kewar ku, zan tafi can inda nasan ko da wasa baza mu taɓa haɗuwa ba, daga ƙarshe kuma ina so kasan lokacin da ka koreni a gidan ka a kashi na farko ban aikata abunda aka ce na aikata ba, amma zata iya yuwuwa bayan hakan nayi wani aikin alfashan, kuma ka sani kaine sanadi, na ƙara maimaita maka ni ba manemin mata bane, sannan kuma nagode da kula da kayi da ni na tsahon shekaru ishirin da huɗu, hakan ma ya ishe ni wallahi, sai wata rana Abba”.

Yana gama faɗa ya rungume shi sannan ya koma gefan Ammin shi yana runtse idanuwan shi, daddy kuwa ko gezau yaja hannun Jibril suka fita.

Da gudu Ummi ta haye sama tana kukan da ba taɓa yi ba a rayuwar ta, babu wanda be zubar da ƙwalla ba har Suhaila da take laɓe tana jin abunda yake faruwa.

Fita yayi shima ya koma ɗakin shi yana mai kallon ƙarshe.

Haka kowa ya wuni a gidan sukuku babu wani walwala, bayan sallar magrib ya shigo ciki suka ci abinci, sannan ya dawo kusa da Ummin shi yana riƙe hannun ta.

Cikin dauriya da jarumta yace; “Ummi na, na shirya zan tafi ki saka mun albarkar ki”.

Wani irin kallo ta watsa mai ,ƙwalla na cika idanuwan ta, bata san sanda ta jawoshi ta rungume shi a jikin ta ba, tana cigaba da kukan kamar ranta zai fita.

“Ahmad ni me zance maka ne ma, ɗana me zance maka”.

Ta ƙarashe maganar cikin shessheƙar kuka.

“Ummi na koma menene ni dai kisa mun albarka kinji”.

Shiru tayi ba tare da tace komai ba, sun kai kusan 10 minutes a haka kafin ya ɗago yace; “Ummi Daddy ya kusa dawowa i have to go please”.

Hannun ta guda ɗaya tasa ta tallafo kumatun shi tana kuka me cin zuciya tace; “Allah ya maka albarka, ya tsare mun kai duk inda ka je, Allah ya rabaka da aikata alfasha, ya Allah ya haɗa ka da wasu iyayen na gari ba irin mu ba, Allah ya haɗa ka da mata ta gari, yasa ka haifi ƴaƴa na gari, yasa su maka biyayya kamar yadda ka mana, Allah ya haska maka ya tsare ka ga duk wani sharri,Ahmad ina sonka, ina sonka, ka yafe mun, na kasa karɓar maka ƴancin ka”.

Rungume ta yayi yace; “Ammi nima ina son ki Allah ya barmun ke, ki kula da kanki don Allah, kinji ko, ki kula da Kausar da kowa da kowa han, ki kula da Suhaila a matsayin surukar ki”.

Yana gama faɗan haka ya bar jikin ta ya rumgume Kausar, sannan ya kalli Zainab itama yaje ya rungume ta yana faɗin”Na yafe miki duk abunda kika mun sai wata rana”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button